BABI NA TAKWAS (8)
Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*NAHMIFAK*
_Collections_
```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```
Sauka tayi a gadon ta nufi ban dakin ta, ta wanke fuska sannan ta fita ta nufi gadonta, ta zauna kafin ta gyara ƙwanciyar ta, domin bata ga dalilin da zai saka ta hana kanta barci ba, zuwa gobe zata yi maganin abin.
★‡★
MASARAUTAT RANO.
Wani irin tausayinta yake ji, tare da shafa sumar kanta yana rarrashinta.
"Zan dawo fa nace!" Ya fada cikin rarrashinta.
"Toh" ta ce mishi,
Haka ya dauke ta sauka shiga wanka, bayan sun fita ta kwanta da wani irin zazzaɓi. Amma sai ta boye kamar babu kome. Haka suka kwana tana kwance a jikin shi, sosai ya fahimci bata jin dadi amma haka ya shirya, wuraren asuba ya bar masarautan baki daya dan sallah asuba ma a hanya yayi ta.
......
Bayan farkawarta ne ta fahimci baya nan, dan haka ta tattara kayan ta, ta koma bangaren su, duk da a cikin gidan an bata babban sashi, amma bata iya zama ba, sai kusa da Inno. Itama Inno tana kunyar bangaren Kubrah. Wannan abin ya janyo musu tsana da tsangwama a cikin gidan sarauta, wanda yasa baki daya basu da wani kuzari a cikin gidan.
Anan haka Inno ta gano cikin yar nata, bata yi kasa a gwiwa ba, ta shaidawa Fulani Hadizah ita kuma ta shaidawa Mai Martaba sarki Abbas, shine ya tura sakon a labarin cikin.
Bayan sakon ya isa da kwana biyu Ya Musa ya iso, yaso matuka gayya ya tafi da ita, amma taki bata son tayi nesa da iyayen ta. Har zuwa lokacin da Waziri ya mai da ita Deehar.
Har zuwa dawowan ta.
---
Dawo labari.
A hankali ta mike, ita kanta zuwa yanzu bata jin daÉ—in jikin ta, ga uban nauyi da kasala.
Kirjinta zuwa kugunta, ya sauya sosai. Domin daga sama ta sauya kirjin ya cika kamar ba yarinya ba, haka kugunta ya kara budewa da wani irin fad'i, asalima tayi irin cikar masu tsohon cikin nan ne, amma ta bangaren tumbin ta, a shafe yake kamar ba kome. A hankali take takawa, har cikin gidan. Da sallama ta shiga zauren Fulani Hadizah.
A hankali ta durkusa daga nesa ta ce mata.
"Umma gani"
"Taso kizo nan na gaya miki ke ma Y'ace ba dan kin yi b'ari ba, ai da kece uwar Sarkin Deehar."
Hawayen da ya cika idanun ta ne, ya sauko ta mike a hankali.
"Fulani wannan yarinyar ai akwai jifa a Jikinta. Ga ciki nan ya bayyana amma babu hanyar fitowa!"
Inji wata tsohuwar Bororoji, da take yawan kawowa Fulani kayan tsarin jiki, domin su yasu ma jifar juna suke, ita ce dai bata damu da ta rama abin da ake mata ba, ta kan tsare kanta ne da Yaran ta maza da suke cikin masarautar.
"Ya za ayi haka? Cikin ya zube shakara kusan uku kenan" inji Fulani.
"Hmm, kainuwa dashen Allah, ba dashen mutum ba. Allah ya shirya waye ya isa dakatarwa? Ku bani danyen madara yau insha Allah zai fito ya shaki iska kamar kowa." Inji Barmani, haka aka kawo madaran ta cewa Jakadiya.
"Dauke ta muje dakin can, idan da Allah bai aiko ni ba, yarinyar nan mutuwa zata yi da cikin jikinta, saboda zalinci irin na wasu, Yarinya karama ma ba zasu barta ba. " Haka suka wuce dakin da aka sauke Barmani, aka shiga hada mata magani.
Ana gama damawa Barmani ta shiga dakin, ta mika mata, bayan tace ta mike tsaye.
Tana mikewa ta shanye sannan ta ce mata.
"Sake kwaryan a kasa!" Sake kwaryan da tayi, yayi daidai da jin wani abu kamar an sare ta. Durkusawa tayi ita kuma, ta cigaba da had'a wani ruwa da magani, tana watsa mata.
"Wayyo Allah na! Wayyo Inno! Wayyo Baffana don Allah ku kira min Inno"
Ta fada cikin tsannanin azaba da tashin hankali.
Sosai ta fita hayacinta, tare da niman agajin Mahaifiyar ta, amma ina kunya ya hanata zuwa. Har zuwa dare abu daya ake, sai wurin bayan sallah isha, Allah ya sauke ikon shi akan Kubrah, inda ta haifi yaronta dan kankani. Kamar ba cikakken d'an Adam ba. Ta koma tana maida numfashi.
Daukar Yaron Barmani tayi tana kallon shi. Sai ka saka idanu zaka fahimci yana raye.
"Fulani a bawa Yarima auduga, kasancewar danne shi da aka yi ya mai da shi baya, a lullube shi ina man shanu da kadanya?" Kafin kace me an kawo ta, ta yanke cibiyar, sannan ta goge shi ta bawa Unguwar zoma damar gyara ta, shi kuma ta goge shi tass, sannan aka saka wutan dakin yadda ya dauki dumi, yasa zai sake ya warware.
Ita kuma uwar aka mata wanka aka gyarata, sannan aka saka taci abinci ta kwanta tuni barci yayi gaba da ita.
Gyara dakin bayi suka yi, sannan suka fito aka bar Barmani a dakin da Fulani.
----
Da murmushi ya iso dakin yana kallonta, itama murmushi take tana wasa da hannun ta.
"Hadizatul Kubra wannan nawa ne?" Ya tambaye ta, gyada mishi kai yayi.
Murmushi yayi ya dauki jaririn ya sumbata, sannan ya juya zai fita ya ce mata.
"Kiyi hakuri." Daga haka ya saka kai ya fita, Mikewa tayi zata bishi.
Bude idanu tai, ta ga Inno a gefenta tana mata murmushi.
Tashi tayi zaune.
"Sannu Kubrah!"
"Inno muje gida " ta fada idanunta cike da kwallar.
"Kin girma yanzu babu batun kuka, dan haka kiyi hakuri, ki zauna anan domin rayuwar shi tana buƙatar kulawar manyan mutane, shi kan shi Yarima ne, ba zai taso a cikin bayi ba sai dole. Dan haka ki kula da shi zan na zuwa duba ki in sha Allah "
Mikewa tayi ta shiga ban daki, tayi tsarki sannan ta dawo ta samu Inno ta bar dakin, abinci me zafi ta gani ta zauna taci ta koshi. Shigowar Barmani yasata d'ago kai.
"Shiga a miki wanka."
"Toh" ta nufi ban dakin Innar Sahura take ciki.
Ta zauna, bayan ta cire kayanta.
A hankali ta shiga yafa mata ruwan zafi. Zuciyar ta cike da hassada da bakin ciki. Take yafa mata ruwan.
Tana gamawa mata, ta ce mata.
"Kiyi wankar" ta fito, a wannan bangaren ita kanta Kubra tayi hakuri sosai.
★‡★
MASARAUTAR DEEHAR.
Yau an tashi da wata irin sirrintacciyar al'amari ne, wanda ya daure kan mutane, domin ga rana da wata, wato rana bata fadi ba. Amma wata ya fito da hasken shi.
Ya Musa da yake tare da Yarima Shehu d'ago kai yayi yana kallon sama.
_A duk lokacin da rana da wata suka fito a lokaci guda! Ka nisanta shi da nahiyar nan_
Sunkuyar da kai yayi idanun shi cike da kwalla.
"Kafin Mai Martaba ya rasu ya bani amanar a duk lokacin da rana da wata suka fito lokaci guda, na nisanta abin da za a haifa a wannan lokacin da nahiyar Deehar baki É—aya, yau ga rana da wata a sarari amma babu abin da aka haifa."
"Hmm!" Yarima Shehu ya fada, yana kallon sama kamar me nazarin wani abu..
Haka suka kasance a wurin, har rana ta fad'i.
----
Sosai suke gudu a cikin kasungurmin dajin. Kafin suka isa kogon bishiyar Aljanu.
"Boka me duniya!"
"Ya shiga halwa ba zai fito ba sai bayan shekaru biyar"
Wannan yasa suka juya zuciya babu dad'i.
---
MASARAUTAR RANO.
Duk wani abin da ake wa me jego, an mata ga wani abin burgewa ruwan Mamanta yana da kyau, a lokacin haihuwan Sarkin Rano yana kano, dan haka ana gobe suna ya iso, da kan shi ya isa zauren Fulani, ya amshi Yaron yayi mishi huÉ—uba.
"DASHEN ALLAH! Sannunka kainuwa!" Ya mishi Huduba da Abdullahi Hayatudeen Noye.
Fulani taso kwarai a tura Deehar, shi ya hana ta hanyar mata bayani. Dan haka ta hakura.
Suka cigaba da kula da Yaron,
Har tsawon wata shida, sannan Barmani ta gama shirya Yaron ta cewa Fulani.
"Ba dai mutum da aljan ba In sha Allah, ni zan tafi"
Sun mata alkhairi sosai, bayan kwana biyu ta tafi, suka cigaba da renon shi. Wanda yana girma, kamanin shi da Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye yana kara fitowa, sai dai farin fatar Mahaifiyar shi da ya dauko kamar balarabe. Gashin kan shi a kwance yake luff-luff.
Watan shi bakwai a duniya ya fara takawa, domin karambani ne da shi kamar me,
Yana cika shekara daya kuwa, kowa yasan cewa akwai wani ajiyar Allah a wurin. Domin kuwa gari ba wayewa zai fita wajen bayin gidan ya zauna da su. Ya saka su a gaba. Musamman Malam Audi, domin baki daya yake tattarowa ya dawo kofar fada ya zauna. Yana kallon mutane.
Haka Jakadiya da Sarkin gida, suke daukar shi a dawo da shi cikin gidan baki daya.
Idan kuwa aka saka masu tsaron shi domin baya kaunar zaman gida, yana cika shekaru uku. Anan aka sake saka idanu akan shi domin a lokacin wasu abubuwan al'ajabi ya fara bayyana a tare da shi, abin farko da ya fara faruwa, ko an rufe kofar dakin su, za a samu an bude ya fita, kuma idan ya fita zai tafi can wurin Dawakai ne, ya zauna. Ko a can zai kwana.
Abdullahi Noye bai kula kowa sai dabobbi, Allah ya daura mishi son dabbobi musamman masu hatsari, sannan dabi'ar shi ce, tun yana Yaron shi. Domin an sha samun shi da kananun macizai, ko kunama a cikin aljuhun rigar shi.
A lokacin da da ya cika shekara biyar ne, sarki Abbas da kan shi ya saka su a gaba suka yi bankwana da Jama'ar Rano, suka wuce Deehar domin duk abinda ake bukata a tare da shi ya bayyana, akwai wani tambari a wuyar shi, wanda sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya ke da ita, duk sauran yaran Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye suna da shi...
#Mai_Dambu.
*A Hausa historical ancient*
17/Nov/2022
For more information chat me:08130269641
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*
        Mai_Dambu...