BABI NA UKU (3)
Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ransu ya yi matukar b'aci amma sanin a kwai zagon kasa yasa baki daya babu wanda ya ce kala, sannan a ka shirya manyan dattawan Fadan Galadima da wasu mayaka kimanin dari biyu, suka nufi masarautar Kwantagora. Da yawan waɗanda suka nufi can kwantagora wasu zuciyar su biyu, domin sun tafi ne domin wata manufa nasu na kan su.
  Â
    Tafiya ce ta kwanaki da ba zasu wuce arba'in ba, ya kai su masarautar kwantagora. Cikin girmamawa a ka mashi jakadar Deehar kafin Mai Martaba ya musu iso akan bukatar su. Sun yi farin cikin jin haka. Sai da suka kwashe kwanaki kamar uku sannan a ka basu Zulai itace sad'akar sarki Hayatudeen. Suka nufi Deehar da ita.
  Lokacin da suka isa dare yayi dan haka suka yada zango a cikin harabar filin da yake cikin Masarautar tare da bai wa Zulai kariya na musamman.
Cikin tsakiyar dare me É—auke da al'amarin ban mamaki, wasu irin surutai marasa tushe da kan gado suka shiga tashi.
  Sosai aka fara samun iska me tafe da guguwa wanda sun san cewa aika ce daga wasun su, kuma duk wannan abin ana yin shi ne domin kar cikin Zulai ya kai labari, don haka aka shiga aiko da miyagun jifa.
Irin wannan yana faruwa amma ba kasafai ba, sai idan an kusan Haihuwar ÆŠa namiji a cikin masarautar don haka Galadima da Wanbai suka yi tsaye tare da kare Zulai wasu dakarun suna masu mamaye ilahirin masaukinta.
Artabu ake har gari ya waye, sai da alfijir ya keto sannan waɗannan ababe suka sarara bayan sun fasa wata ƙara me ƙarfin gaske. Sannan suka tafi, ita kan Zulai tsoro yasa ta takurewa wuri guda. Har gari ya waye, sannan suka mata magana ta fito fuskar ta a kumbure domin bata rintsa idanunta ba daren jiya ba.
Jagora suka mata har zuwa cikin fadar masarautar, aka gabatar da ita.
"Ku kaita shashin gabar, a bata duk wani abin da take bukata" inji Waziri yana kallon ta.
Kafin ya mai da hankalin shi kan sauran mutanen Fadar ya ce.
"A saka idanu a kanta ita da abin cikin, domin bai zama dole su tsalleke yanayin gidan nan ba."
Shigowar Sarkin gida da wasu abubuwan ya zube su a gaban jama'a,
"Sarkin gida lafiya?"
"Wannan sakon ya iske shi a turakar Marigayi Mai Martaba."
Daukar takardan saman ya yi, ya mik'awa Maga takarda.
BuÉ—e takardan ya yi cikin kulawa yaga tambarin masarautar Rano.
Cike da mamaki yake kallon mutanen fadar, kenan mai Martaba kafin ya rasu yasan da za a nemi wannan sakon.
_ASSALAMUN ALAIKUM_
*BAYAN DUBUN GAISUWA DA BAN GAJIYAR RANGADIN DA KAYI, ALHAMDULLAHI AJIYAR KA TAYI YAD'O DA YABAN YA ALLAH YASA KA ISO LAFIYA*
SAKO
DAGA
SARKIN RANO
Ajiyar zuciya kowa ya sauke suna kara jin wani irin tsana akan Marigayi Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye.
"Ai sai a tafi Ranon ko a taho da ita, domin bata cikakken tsaro." Inji Chiroma.
Kura musu idanun sarkin yaki ya yi, sannan ya ce musu.
"Wannan matar itace Ya Musa yake tare da ita. Domin kuwa idan ba ita ba, toh akwai wani abu a ƙasa. Don haka ayi kokarin ganin a kawo ta, har da Ya Musan domin akwai wani abu."
A hankali Zuciyoyin wasu ya kasu gida-gida domin kuwa basu zaci haka ba, dan haka aka shirya dakarun na musamman karkashin jagorancin Wazirin Deehar da Shamaki, suka nufi masarautan Rano.
**
Tafiya kwanaki goma ya isar da su Rano, tare da samun tarb'a na musamman.
Bayan sun huta, Waziri ya shigo da zancen rasuwar Mai Martaba sarki Hayatudeen Abdullahi Noye. Tabbas Sarki Abbas ya girgiza domin abokin shi ne tun Yarinta, dan haka ya yi kasa da kai sannan ya ce.
"A kwai Yarinyar da ya gani anan tun zuwan shi kafin ya wuce rangadi, sunanta Kubra, Mahaifinta bayi ne da Sarkin Borno ya bamu su, lokacin auren mata ta Hadizah. Sune suka haifi Kubra suka mata takwara da mata ta. Yar ya gani ya amsa a matsayin sad'akar shi. Kuma ya yi wannan rangadin da ita."
Jinjina kai Waziri ya yi sannan ya sauke ajiyar zuciya. Ya labarta mishi abin da yake faruwa.
Shiru Sarki Abbas na Rano ya yi sannan ya ce.
"Ya turo Ya Musa ko?"
"Eh Ya Musa yana tare da su, sai dai nayi alƙawarin kare rayuwar ta da abin cikin "
Jikin Waziri ne ya yi sanyi ya kalle Sarki Abbas.
"Idan alkawari ne nayi maka rantsuwa da Allah zan bada rayuwata domin kare uwar da É—an!"
Sanin girman rantsuwa da Allah tare da girman Waziri ya mike tare da mishi iso cikin gidan, domin shi daya ya samu ganin Mai Martaba sarkin Rano. Shima din saboda a kwai kyakyawar alaka ce me karfi a tare da su.
Lokacin da suka isa cikin gidan, ya saka a ka kira Fulani Hadizah, tana zuwa ta samu wuri ta zauna, sannan ta miks gaisuwa ga Wazirin Deehar. Kafin ya tattara nutsuwar ta ga Mijinta.
Sai da ya yi shiru kafin ya ce mata.
"Takwaran ki ce za a mai da ita Deehar" dake kirjinta tayi tana girgiza kai ta ce musu.
"Deehar?"
"Kwarai da gaske!"
"Kubra tai kankanta da masarautar Deehar." Ta fada hawaye na zuba mata.
Shi kan shi Sarki Abbas wallahi jikin shi ya mutu balle ita.
"Kuyi hakuri, In sha Allah babu abin da zai faru da ita sai alkhairi"
Zuwa yanzu waziri ya tsorata shi ma da son daukar Kubra.
"Ba mu san me a ran ka ba, sannan ba zamu hanaka daukar ta ba. Sai dai a nimo Ya Musa."
Haka kuwa aka tura Jakadiya, kiran shi.
Yana shigowa ya zube akan gwiwar shi ya gaishe da Wazirin Deehar .
"Ka kyauta ko! Ashe da wannan yanayin ka zab'i shiru ka sulale ka tafi, me yasa baka gaya min ba?" Waziri yake tuhumar Ya Musa.
Idanun Ya Musa na zubda hawaye ya ce.
"Ka gafarce ni, amma Amana daya ce ita ya bani akan Kwarkwarah Kubra. Taya zan rushe amanar da ya bani?" Ya fada yana share kwalla.
Jikin waziri ya kara sanyi.
Maganganun Magajiya ya dawo kan shi, ya kurawa Ya Musa idanu sannan ya ce mishi.
"Amana daya ce! Kuma ya baka nima kuma na kara baka, sai dai dole a kaita su ganta sauran kuma ka yarda da Allah ka yarda da ni ba zan zalince ka ba. Itama kuma ba zan zalince ba" domin ya fahimci matukar ya saka zalamar son mulki jikokin shi ba zasu yi ba, Hakazalika idan ya juya ya ce sai yaga bayan abin da a haifa sai dai ya rasa ran shi.
"Mai Martaba sarki Abbas, ina niman Alfarman saka baki su dawo Deehar babu abin da zai faru sai ikon Allah"
Sun tsayar da maganar tafiya washi gari. Don haka Ya Musa ya musu iso har cikin gidan wurin iyayen Kubra, tabbas yaga mace inda ake kira mace dole Sarki Hayatudeen ya rud'e, duk da lullube take da babban mayafi, bai hana shi hango tsagwaran kyau da Allah ya zuba mata.
Ya gaya musu rasuwar Mai Martaba sarki Hayatudeen, a firgice ta zuba mishi ido kafin ta sunkuyar da kai tana me fashewa da kuka, tabbas tayi rashi ita aka yiwa mutuwa, kuka take sosai me shiga jiki, shi kansa sai da ya fahimci irin kaunar da take yiwa Sarki Hayatudeen, ai dole taso shi kuma dole ta yi kukan mutuwar shi domin yasan kan mace, ya kuma san yadda zai bi da mace kome kankantarta ta fada kaunar shi mara iyaka.
Haka ta kwana tana kuka, har kunya iyayen ta suke ji domin basu tab'a ganin haka daga gare ta ba, tana da kunya sosai domin ko cikin jikinta bata so su sani ba, sai dai rashin lafiya da walwla yasa dole suka d'ago ta, tare da kiran unguwar zoman masarautar ta duba ta.
Washi gari
Suka dauki hanyar Deehar, haka ba karamin al'amari ba ne a gare su, sannan an bata bayi goma mata masu kula da ita. Har suka isa masarautan, wanda suka mishi shigar almuru. Tun kafin su isa wurin Bishiyar kukan da Sarki Hayatudeen yake zama aka aji an fara bushe bushe da algaita da k'ak'aki, haka ya tabbatar da ilahirin masarautan sun fahimci wadancan mutanen boyen sun yi na'am da macen da aka kawo kenan. Dan haka suka wuce cikin Masarautan Deehar, babu b'ata lokaci aka nufi shashin Magajiya da ita, domin wannan tafiyar Waziri ce. Da kan shi ya mika ta da Yar shi.
"Ga Kubra nan, nasan yadda zuciyar ki bata da tsatsa zaki kula da ita" wani kallo ta mishi sannan ta ce mishi.
"Wallahi ba zan rike matar da Hayatudeen ya rab'e ta ba, domin kuwa ba zan iya cigaba da kallon idanun ta a matsayin matar da mijina ya kwanta da ita ba."
"Ni..."
"Baba ka tafi da ita kawai" haka ya fito da ita jikin shi a mace, ya nufi wurin Kilishi, wacce sai yanzu aka fahimci tana dauke da karamin ciki bayan rasuwar Sarki Hayatudeen.
"Waziri ka tafi min da ita ba zan amshe ta ba, domin kuwa rab'ar mijina tayi, sannan abin da take dauke da shi, shi nima nake dauke da shi."
Jinjina kai ya yi, sannan ya fice wurin Fulani Karama ya shiga da sama.
"Kamar Muryar Waziri yaushe ka dawo daga Rano?" Wani matashin saurayi makaho ya tambaye shi yana rike da sandar shi.
"Na ji kamshin Ya Musa"
"Yarima Usmanu gani nan." Ya nufe shi yana kukan farin ciki. Juyawa yayi sannan ya ce mishi.
"Ku uku ne?" Domin Allah ya mishi baiwar fahimtar mutane a wuri musamman suka haura biyu zuwa uku....
*NAHMIFAK*
_Collections_
*Hausa Historical Ancient*
#Mai_Dambu
#wed/Nov/2022
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*
        Mai_Dambu...
*NAHMIFAK*
_Collections_
```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```