← Book details Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 18

BABI NA BAKWAI (7)

Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda yaso da bukatar Kubrah yasan matuƙar ya yi amfani da bukatar shi, sai ya kusan hallakata. Dan haka ya rarrashin kan shi, ya kyale ta. Sannan ya rungume ta a hankali yana shafa bayan ta. Domin babu abin da ya ke so ya ga, mace na narke mishi, yana masifar kaunar haka. Yana son ganin mace tana mishi yar rigima da rikici, haka yasa shi lalacewa a kan ta. Shi a sanin sa, bukatar ta yake amma a hankali wani irin yanayi me gauraye da madarar kauna ya gauraye tsakanin su.

Sun yi tafiyar wata biyu bayan isa manyan biranen ƙasar Hausa, ta samu kyautattuka daga manyan sarakunan kasar Hausa, zuwa matan su. Har zuwa lokacin tsakanin Hayatudeen Abdullahi Noye, sai a hankali.
A hanyar su ta dawo ne, bayan sun ziyarci birnin kwantagora. Ya haÉ—u da Zulai.
Bayan abin da ya shiga tsakanin su, sai yaga Zulai itama ba wata babba ba ce, tunda ta iya daukar bukatar shi toh itama Kubrah zata iya daukar na shi.
....
Dan haka yana dawowa yaji yana bukatar kasancewar shi da ita. Duk da bata da hayaniya, amma ta sake jiki da shi. Tunda suka kwanta ta lura da yanayin bukatar shi ya fita ta kullum.
Dan haka koda ya fara abin da ya saba mata, ta kuwa biye shi, suka yi nisa sai ta fahimci ai labarin daban, inda ya dosa daban. Dan haka a take ta kwace bakin ta, ta fara kokarin kwace kanta da jikinta, sai dai yadda ya mata kyakyawar riko, yasa ta kasa tabuka kome. Yadda yake shige mata da hake mata tare da shiga jikin ta, yasa ta sume mishi dan bata tab'a daukar haka abin yake ba, sai da ya shiga cikin jikin ta, ainun yana jin shi daidai sannan ya shiga aikin da ya dace. Ya jima yana bibiyar lamarin ta, sosai dan sai da ya maida ita cikakkiyar mace, sannan ya janye daga jikin ta.
Shi da kan shi, ya taimaka mata. Sannan ya dawo ya kwantar da ita, shima ya shiga ya yi wanka ya dawo.

Haka suka kwana daga ita har shi, babu wanda ya iya rintsawa, domin ita kuka take shi kuwa, yana kallon ta da dukkan zuciyar shi. So ne gauraye da madarar kauna, yana kuma kara karfi a zuciyar shi. Haka suka kwana dalilin da yasa aka d'aga komawan su, Rano kenan, sai da suka kwashe kwanaki kamar biyar sannan ranar na shida, ana gobe zasu tafi ya kuma rutsa ta, tana kwance.
Tunda ya cire alkyabar shi, ya kwanta a bayan ta yake shafa jikin ta, tun daga cinyoyinta har zuwa saman dukiyar fulanin ta, masu kyau da suka fara fitowa, saboda samun kulawar da yake daga Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye.
Goga kan shi yake a kafad'arta, yana me kara damkar tsokar jikinta. A hankali abin da ua faru ya dawo kanta, janye jikinta tayi ta fara kuka.
"Ba ki so ne?"
"I" ta fada, cikin matsanancin kuka, shafa bayan ta yayi sannan ya dawo sa ita jikin shi ya ce mata.
"Tafiyar da zamu yi ina son na koma gida ne, na sanar da iyalina ke. Sannan sai na dawo na dauke ki da kaina, idan kika bari na kara ƙad'an ba zan miki da zafi ba,.kin ji!"
Hawaye na zuba mata, ta koma ta kwanta a jikin shi. A hankali ya shiga turmusata, har ya kai da ya kuma bin tsarin shi na farko. Ta sha wuya a hannun shi, shi kan shi wannan daren yayi mugun danasanin halin da ya jefa kan shi. Domin baki daya ji yake kamar karfin shi baki daya yake juyewa jikin ta.  Daga shi har ita a galabaice suke, sai wurin asuba ya sarara mata, shima dan yadda yaga jikin ta ya sake ne, yasa shi kyale ta. Yana sauka a kan ta ya fara amai. A hankali zazzaɓi me zafi ya rufe shi. Har aka yi sallah asuba. Sai sa gari ya fara haske sannan ya nufi makewayi ya yi wanka, sannan ya koma ya gabatar da sallah. A matukar gajiye ya taimaka mata tayi wanka, koda ta fito a hankali take takawa. Ya zuba mata idanu, tausayi take bashi wani irin tausayinta yake ji, mik'awa yayi ya nufe ta, sannan ya rungume ta a kirji shi yana shafa bayan ta.
"Kiyi hakuri kin ji" d'aga mishi kai tayi.
Haka ta saka kaya tayi sallah, sannan suka ci abinci, suka dauki hanya. Tana kwance a kirjin shi, dake suna keken doki ne. Haka yasa shi shafa fuskar ta, lokaci zuwa lokaci.
A hankali ya sumbaci goshin ta, da hancinta. Lumshe idanunta tayi tana shafa yar kasumbar shi da suka yi fari.
"Kubrah!"
Bude idanun tayi tana kallon shi.
"Kin san me? Idan na koma in sha Allah ba zan mai dake a sad'akata ba. Zan baki yanci me girma yadda kema zaki samu damar shiga cikin gidan yadda kike so!"
Gyada mishi kai tayi, tana me lumshe idanun ta, kamar yadda take tun farko.

Tafiyar kwanaki hudu ya kawo su Rano, a lokacin da suka isa da tsakar rana ne, dan haka da kan shi ya rakata har bangaren su. Abin ya bawa kowa mamaki. Duk inda ya wuce zubewa ake ana gaishe shi.
Yana shiga , cikin girmamawa ya gaida Inno, wacce labari ya iske ta. Ga Kubrah da Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye,. Cikin girmamawa ta shiga hidima da shi, shi kuma idanun shi yana kan hasken shi, da take takure a can gefe guda. Shinfida mishi taburma tayi, duk da bai da niyyar zama, amma sai ya ji yana son zama ɗin.  Daki ta shiga ta kawo wani kyakyawar akushi da wasu kofunar tasa, ta kawo mishi dafaffiyar madara, wanda Mahaifin Kubrah ya kawo ta mishi kindirmo. Ta ajiye a gaban Kubrah, sai dambun tafasa ta kawo mata ta saka mishi.
Ita kuma ta koma daki, tana ajiye mishi zata mike ya riko hannunta.
Tare da gyada mata kai, zama tayi ta wanke hannun ta, shima ta zuba mishi ruwa ya wanke hannun shi, idanun shi yana kanta.
"Kiyi hakuri" d'ago kai tayi, ta kalle shi, sannan ta kawar. Haka suka ci Abincin a tare, yana kallon yadda take kokarin boye hawayen ta.
"Na miki laifi ko?"
Ya tambaye,
"A'a"
"Na miki gashi kina kuka, ko kar na tafi ne?" Cikin kunyar shi ta sadda kanta kasa, tana girgiza kai.
"Zan dawo in sha Allah"
",Kayi alkawari?" Ta mika mishi karamin yatsarta, murmushi yayi sannan ya saka yatsar shi, suka kulla alƙawarin.
Shigowar Ya Musa da Sarkin gida, yasa ta fara kokarin cire yatsarta, ya rike gam. Magana Ya Musa ya mishi, a hankali ya mike tare da ita.
Sumbatar hannun yayi sannan ya ce mata.
"An jima Jakadiya zata zo daukar ki."
Gyada kai tayi tana wasa da yatsarta.  Fita suka yi, aka take mishi baya. Yadda fuskar shi ta koma ba zaka tab'a yarda shi ya gama hira da Kubrah ba, amma sakamakon, labarin da aka aka turo mishi, dan haka dole gobe ya bar Rano.
Sun gana da Mai Martaba sarki Abbas, sun tattauna. Sannan ya gaya mishi kudirin shi akan Kubrah, shiru yayi sannan ya ce mishi.
"Ina ga ka hakura da ita a haka man, idan yaso sai ka rike ta hannu bibiyu, ai ba dukkan abin da muke so, muke samu ba haka sai ya zama kamar jarabawar so ce"
"Na gode, kuma na fahimta."
Ya fada, haka suka wuce sallah azhar basu dawo ba, sai bayan la'asar.

Nan ma tattaunawa suka yi ta yi, sai isha suka fita dake akwai abinci da aka shirya musu, shi kan Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya kasa cin kome, domin abinciin Innar Kubrah ta cika mishi ciki. Bayan sallah isha, aka tura Jakadiya ta kawo ta.
Tasha ado, cikin wani yadin silki da ake kawowa daga kasar yamma, sai kamshi take, haka suka fito wurin shi, wunin yau tayi shi ne cike da kewar shi.
Koda suka isa, Jakadiya ta tafi zama tayi a shimfidar zauren idanun ta kan kofar. Tun tana saka ran zuwan shi, har ta cire rai ta kwanta. Barci yana fara daukar ta, ya shigo a hankali ya zuba mata ido.
Shafa fuskar shi ya yi, yana murmushi.
A hankali ya dauke ta, zuwa dakin bude idanu tayi tana zarewa ganin shi yasa ta kwantar da kanta, wunin yau bai bashi damar jin laushin Jikinta ba, dan haka cike da kewar juna, na kwanakin da suka dauka basu kasance a inuwar juna ba, ya murzata, ta jure sosai amma a karshe sai da ta fashe mishi da kuka, domin shi bai iya ji ba, kuma bai iya tab'awa kad'an ya bari ba. Sai da ya jima sosai sannan ya janye daga jikin ta, yana shafa bayan ta zuwa dokin wuyar shi.
★‡★

MASARAUTAR DEEHAR
W

uta ne ya kama baki ɗaya, masarautar yana ci da wuta. Gawar da aka ajiye na wasu mutanen da bata san su waye ba. A hankali take takawa har cikin fadar da wutar take ciki. Hango tayi kome na fadar ya kone, sai kujeran sarki ce take nan babu abin da ya same ta. A hankali ta saka kafarta, ta ji ta cikin ruwa. Da sauri ta ciro kafarta ta juya inda gawarwarkin nan suke, ta koma da sauri amma kofar fadar ta rufe,  kukan yara da sassan jikin jarirai ne a zuba a fadar.
"Kowanni zunubi yana da iyakar shi. Zunubin ku yana da iyaka iyaka mara karshe. Ki duba izuwa gawarwarkin da kika tsallake. Dan haka dole ku biya zunubin da kuka aikata domin san zuciya irin taku. Idan rana tafito tafin hannun bai kare shi. Dan haka ishara ce."
Farkawar tayi daga barci da take gumin yana ratso mata, duk da yanayin sanyi da ake ciki bai hanata jin gumi ta ko ina na jikin ta...

*16/Nov/2022*
*A Hausa historical ancient*
#Mai_Dambu--For more information chat me 08130269641..
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*


               Mai_Dambu...
Chapter 7 · 0% Book details