BABI NA GOMA (10)
Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
This book isn't free....
Fashewa suka yi da dariya, suna kallon shi tare da faÉ—in.
"Wannan d'an abun shi zai yi fada da mu? Bayan ya yi laifi lallai Yaro kayi kuskure."
Suka sake fashewa da dariya.
Sannan suka nufe shi da nufin idan suka isa wurin shi su make shi yadda ba zai mori kan shi ba har na tsawon kwanaki. Sai dai kuskure ne nufin su, domin yadda ya maida sandar baya, suna nufar shi, ya shiga walwalata a sararin samaniya, kafin ya fara zane su da sandar idanun shi rufe, duk abin da suke Sarkin yaki Uzairu na kallon su, kuma yaki ya hana su. Babu abin da ya kara bashi mamaki kamar yadda Abdullah yake zane su, kuma cikin abin bai wuce dakika dari da sittin ba. Ya zane su ya koma kan Yarima Arshan.
"Kayi abin da ya kawo ka! Idan ka kuma zuwa da sunan rigima!" Sannan ya koma ya ajiye sandar.
Wucewa yayi ya nufi hanyar gida, wannan al'amarin da ya faru, ya haifar da tashin hankali, domin wurin sallah isha aka turo fadawa suka tafi da shi.
Filin da ake basu horo nan aka kai shi, suka kalle shi baki daya ya yi kankanta da cewa shi ya daki manya maza.
"Abdullah kai ne ka dake su?" Kallon su ya yi, sannan ya girgiza kan shi.
"Me zai saka na dake su Baffa?"
"Wallahi shi ya dake mu" suka fada,
Takaici ne ya turnike Galadima taya dan mitsitsin yaro kamar wannan zai daki maza.
"Ko mai da shi gida" haka suka juya ya kalli Galadima, shima kallon shi ya yi, sannan ya lumshe idanun shi. Suka bar wurin.
Washi gari, da Ya Musa ya kawo shi. Kallon Sarkin yaki Uzairu yayi ganin yadda aka turke kuraye biyu. A wurin ana jiran yazo.
"Sarkin Yaki Uzairu! Me za ayi da kurayen nan?" Ya Musa ya tambaye shi,
"Umarni aka bani, wai Abdullah ya koyi yaki da su."
"Amma kasada ce babba, Yaro karami ya zai yi da wadannan ababen. Ina zuwa" ya juya cikin gidan kai tsaye fada ya nufa.
"Uzairu!" Arshan ya kira sunan shi,
"Ya ba a fara ba? Ko tsoro jarumi yaƙe? Maza a fara"
"Toh ya shugaba na"
--
A fada kuwa hana Ya Musa shiga fadar aka yi, hankalin shi a tashe ya nufi gidan waziri, ya labarta mishi.
Shima koda ya zo fadar bai samu shiga ba, haka suka hana su shiga, idan rayukan su yakai dubu sai da ya b'aci, kafin aka bude musu fadar.
"Galadima! Taya za a haÉ—a Abdullahi da kuraye?"
"Hmm! Mangori wasa kanka da kanka, ni meye nawa a cikin wannan lamarin? Salon ka yab'a min bakin jini."
"A'a amma matukar wani abu ya same shi, wallahi kowa yayi kuka da kan shi." Ya juya ya fita cikin kunar rai shi da Ya Musa,
---
Filin suka koma, anan suka samu an cika kamar an kira jama'ar fadar da na wajen masarautar.
Abdullah yana tsaye a cikin tsakiyar filin da aka kewaye shi da wasu irin karafuna.
Gashi ko sanda an ki bashi, yana tsaye yana kallon yadda kurayen ke gurnanin.
Jikin shi ne ya dauki rawa, Arshan suka kwashe da dariya.
"Yaro man kaza, waye ya gaya maka fada da Aljani akwai riba ne? Sai dai Uwarka ta kuma haihuwar wani idan akwai halin haka, ku sake su."
Duk da akwai Yarinta a tare da shi, haka bai hana shi jin kunci akan abin da Arshan ya gaya masa ba. Dan haka ya tsaya tare da lumshe idanun shi, idanun shi wani irin iska yaji a tsakiyar kan shi, kafin ya bude idanun shi da suka yi fari sol.
Ya shata layi yana Fuskantar kurayen, kamar dama jira suke ya musu alama, sake musu igiyar karfen da aka daura musu aka yi, suka famtsa kan shi a guje.
Cikin mugun nufi suka kawo mishi cafka, cikin zafin nama ya kauce. Suka kara kawo mishi wata irin Mahaukaciyr cafka, garin ya zille daya ya yaga rigar shi har sai da ya tab'a fadar shi ya karta.
Tsalle yayi ya fada can gefen, yana jin saukar abu a gadon bayan shi. Shafawa yayi yaji jini, kan shi ne yayi wani irin sarawa, ya damki ƙasa da hannun shi na dama, ya watsa a bayan shi.
Kallon shi kurayen suka yi, bayan dayan ya lashi jinin akaifar shi.
Shima daya kuran ya bi inda rigar yake yana lasar jinin.
Wani mahaukacin ihu suka yi, kafin suka nufe shi da mugun gudu, domin kawai suyi dage-dage da namar shi.
Yana durkushe a wurin, yana kallon su, cikin abin da bai wuce taku hudu ba zuwa biyar da ya shata tsakanin su.
Waziri ya cilla mishi sanda, kamar dama jiran sandar yake, yana dauka ba tare da alakari da kome da zai faru ya faru ba, ya kai musu wani irin harbi da sandar, ai kuwa haka sandar ta huda goshin kura daya sai da ta fito ta bayan shi, can ya fadi matacce.
Dayan yana zuwa Allah ya bashi sa'a ya karci kumatun Abdullah, sai da ya fadi can dan kartan yazo daidai da mangare shi da kuran yayi ya fadi can, kusa da mataccen kuran.
Dukar kasa yayi ya kai hannun shi zai zare sandar, kurar ya kuma kai mishi sura.
Suka fadi can. Wani azababben fada suka shiga yi, ga yanayin wurin da yashi kamar Sahara kura ya rufe wurin, baka iya gane waye ake mishi ake kan shi waye a kasa.
Sai dai ihun kuran da gunjin sa, zai iya baka amsoshin masu birkita lissafi, shin kukan ceton rayuwar shi yake ko kukan fatatakar Abdullahi yaƙe.
Bayan kamar dakikai dari da Ashirin, kuran da ta turnike filin ya washe, sarai Abdullahi ne tsaye akan kurayen, fuskar shi da jikin shi jini ya wanke mishi, bude idanu yayi ya Zubawa Galadima idanu da aka kafa mishi rumfa.
A hankali ya janye idanun shi, sannan ya sauke kafar shi, akan kurayen. Ya nufi wurin ya musu da yake dauke da wata ƙatuwar tulu, ya shiga zuba mishi ruwan a kan shi yana wanke mishi jikin shi.
"Yaron nan an haife shi ne domin kafa tarihi, duk abin da muke tabbas yana kallon mu yake. A yayin da muke mishi kallon biri shi kallon ayaba yake mana. A dauki mataki gaskiya"
Inji garkuwa.
"Hmm" ganin yadda fuskar shi ya karce yasa ya musu ya dauke shi a bayan shi, shi da waziri suka nufi gidan me magani.
Me suna Ya Dauda.
Kallon shi yayi ya ja waziri da Ya Musa gefe, yayi musu magana kafin suka shiga wani daki sun jima a dakin sosai. Kafin suka fito ya gyara Nishi fuskar shi da bayan shi.
Haka suka isa sashin su,.yana me sauke ajiyar zuciya musamman ganin yadda Innar shi take kallon shi kasa kasa. Amma yaki tambayar shi me yasa me shi. Shima wucewa yayi ya kwanta rub da ciki.
A hankali barci ya dauke shi, sai lokacin ta lura da sosai jikin shi babu lafiya.
★‡★
Tsawon sati biyu Baya fita, ranar da ya fara fita, ciwon fuskar shi ta warke sai dai rabon yasa shi kasa sakewa a cikin mutane, abu na farko da ua fara fuskanta kenan, idan ya fita mutane sai su fara ihu.
Hankalin Ya Musa da Waziri ya tashi, dan haka suka nufi gidan Ya Dauda. A hankali ya kalle shi.
"Ai babu shakka abin da na fahimta tun wancan lokacin kenan, jinin shi ake bukata. Allah kaÉ—ai yasan me zai iya faruwa domin alal hakika zasu cimma mashi. Sai dai ya daina fita idan zai fita yana rufe fuskar shi."
Sannan ya haÉ—a mishi magani, suka tafi.
A daren ranar aka shiga har wurin maganin Ya Dauda aka mishi kisan gilla, wanda yasa sauran masu magajin fadar shiga hankalin su, domin matsalar Abdullah kara ta'azzara yaƙe, idan yana barci yaji ta gunji da gurnani kamar zaki. Idan da zaka ga halin da yake ciki sai kayi kuka. Domin azabtarwan tayi yawa.
Dan haka ta nime Izinin tafiya da shi Rano ko za a dace a can, amma aka hanata tafiya. Haka tana ji tana gani shima Waziri da yake taimaka musu, ya rasa yadda za yi.
Dan haka cikin sirri ya nime wani amintaccen abokin shi wani bamagujen yakin nahiyar ne, amma suna can gabashin Deehar a wani kauye me suna.
Nahara.
Kauyen Nahara maguzawa ne, a kauyen baki daya. Sannan sun kasance masu tsafi da bautar gumaka, suna cikin aminci da zaman lafiya. Duk da basu yawo da kaya sai ganyen da suka rufe kugun su, gaban su da bayan su. Mata kuma suna rufe kirjin su. Kauyen Nahara sai an tsallaka ruwa kafin a shigar da mutum garin.
Dan haka Waziri ya dauke shi, suka tafi bai dauki Ya Musa ba, domin haka zai iya sakawa a fahimci basu nan.
Tun da bason a mishi jinya suke ba.
Lokacin da suka isa garin a lullube yake, sai da aka yi wani irin tsafi ya buÉ—e suka shiga da shi.
Kai tsaye gidan.
Gumsi nahira aka nufa da shi. Yana kofar gidan shi. Duk da tare ya raba,
Tashi yayi ya amshi Abdullahi, ya kwantar da shi.
Ya dafe goshin sa, yana me lumshe idanun shi.
A hankali yake ganin wasu al'amurran marasa kyau da dadi, bude idanun shi yayi.
Sannan ya shiga cikin gidan ya haÉ—a Maganin kafin ya zo ya watsa Mishi. Ihu yayi kamar zai tashi sama, launin jikin shi ya sauya, gashi ya shiga fitowa a jikin shi.
Watsa mishi yayi. Ya koma ya kwanta, sannan ya bude idanun shi da suka yi wani irin ja, asalin idanun ya koma kalar ta kuraye.
"Ban san me gobe zai iya haifarwa ba, amma a lokacin da zai dauka kome ba kome ba, yana karatowa, amma wannan ku mishi amfani da shi. Tabbas akwai boyayyen al'amari a tare da shi da kuma muma alummar Nahara. Duk da akwai Lokuta maso tsawo dole ya kasance haka."
"Kamar ya?"
Mikewa nahira yayi ya nufi hanyar shi, Waziri ya bishi.
"Kasan shi din an haife shi ne dan kafa tarihi! Kasan adadin mutanen da suke tsaye domin ganin bayan shi? Dan haka kowacce dakika ta rayuwarsu da shi suke kwana, mafi alkhairi ku dauke shi daga nahiyar nan domin zasu iya kashe shi a yanzu ma ai sun kashe shi kaÉ—an ya rage musu..
*Wannan littafin na kudi ne akan 500N*
500₦... Insha Allah'
a tuntube wannan number 08130269641 Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
*A Hausa historical ancient*
20/Nov/2023
#Mai_Dambu
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*
```Haseer collection dealer ce kayanmu suna da sauqi sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayan mu cikin sauqi alhmdllh ga kadan daga ciki ina Matan iyayen giji! Yau ga sabon labari mun zo muku da shi kawo kunnen ku kuji labari.
1: royal jelly 2500 me 60pc babba 19k me 365pcs
2: sugar wanita 2500
3: extreme maca 4000
4: vitamin c 2200/2500
5: vitamin e 2000
6: gluta white 2500
7: khusus 3500
8: pesona 2500```
        Mai_Dambu...