← Book details Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 18

BABI NA SHA HUÆŠU (14)

Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsowa ya yi kusa ita, tayi baya tana kallon shi bakin ta a sake. Lashe bakin ta tayi tana zare idanu.
"Waye kai?"
"Nalado" ware idanu tayi sosai cikin tsoro ta ce mishi.
"Na gidan rumbun hatsi?" Lumshe idanun shi yayi yana budewa a hankali akan ta fess.
"Kin amince na kai maganar mu gaban Nahira?"
"A'a" ta mike jikin ta yana rawa,
Cike da mamaki yake kallon ta.
"Me ya sa?" Ya tambaye ta,
"Ai zaren ba irin yadin ba ce."
Ta fada tana mikewa, shima mikewa yayi.
"Jima mana"ya ce mata.
"Wai kai lafiyar ka? Yau naga duniya tow ce maka aka yi zan kula ka ne"
"Ai kuwa da kin kula shi da kin ci uwaki"
Juyawa tai tana kallon yarinyar da bata wuce tsarar su Abigail ba.
Murmushi tayi mata sannan ta ce mata.
"Wai ke da ni kike?" Ta tambaye ta,
"Sai ka karci kan uwarki zaki fahimci da wacce nake."
Juyawa Easter tayi tana kallon gefe da gefe, kafin ta ce mata.
"Eh tow Kya karci ta uwatai" sannan tayi gaba abin ta, haka take bata san tsoro ba, ba ta san fargaba ba. Abu daya ta sani matukar tana da gaskiya wallahi babu me tab'a lafiyarta.

Shan gabanta yarinyar tayi tana faÉ—in.
"Dan Ubanki kafirin nan, da ya butulcewa abin bauta, kar na kuma ganin ki."
"Tauuu" ta dauke ta da mari, rike kuncinta tayi tana kallon Easter da ko a jikin ta.
"Yo da nasan wancan abin yana kula ki, dan kan Ubanki ai da bai ishe ni kallo ba, wawuya me abin faÉ—a" da matukar kunya a samu mace a cikin garin Nahara tana fada akan Namiji, sabida girmama Jaruma Nahara, suna da wani irin alfahari akan kasancewar su mata, babu namijin da ya isa su yi fada da shi, koda kuwa kwace maka shi aka yi wannan jijji da kai da alfaharin Jaruma Nahara yana jinin su.
Tun da ta tsinka mata mari tayi tafiyar ta, shima Matashin tafiya yayi ya barta cikin kunya da tashin hankali.
A hanya kuwa daukar kara tayi tana tafiya,
"Lati kar ka min kome, kasan matukar ka d'aga min fatarina tsinuwa da masifa zata auku na hada ka da Jaruma Nahara kar ka min kome" ware idanu tayi tana kallon wurin bishiyar tsamiyar da yayi duhuwa, tana kuma jin muryan Abigail.
"Ba wani abu xan yi ba, gogawa zan yi ke kamar baki waye ba. Ai idan muka fita wajen Nahara ba karamin dadi muje ji ba mata da kan su suke zuwa mana"
A hankali take takawa tana jin muryan Lati, a hankali ya leka hasken farin wata ya haska ko ina amma ban dasu.
"Su waye ne a wurin?"
"Na shiga uku! Mayyar nan ta gan mu" inji Abigail ta ture shi tana daura fatarin ta, da kuma matarin Kirjinta.
Fitowa suka yi, ta saka hannu a baki tana mamakin su.
"Me za a goga? Kuma a iya za a goga?" Ganin bata fahimci kome ba yasa suka mai da ita shashasha na gaske.
"Ai babu kome kawai jin ciwo tayi nake son goga mata ganyen tsamiya" tab'e baki tayi, daga haka ta wuce abin ta. Janyo Abigail yayi jikin shi yana cewa.
"Ki san yadda zaki yi amma ba wani abu bane, duk fada ake da camfi"
Juyawa tayi ta ga yadda suke manne da juna.
"Na shiga uku! Me kuke yi ne haka?"
Sake ta yayi yana me cewa.
"Ina duba ciwon ne" bata iyawa da takaicin su, dan haka ta nufi gida abinta.
--
A daren Magaji yana kwance a bayan Mama Uwar, har barci ya fara daukar shi ta ce mishi.
"Ban fahimci makomar Wabi da Lati ba, shin ba  za a yanta su bane?"
Dan ita a tunanin ta, ai auren Lati da Wabi shine abin da zai hana Kyauta zama wani abu.
Bude idanun shi yayi sannan ya ce mata.
"Ki yiwa yarki fada kar ta zama wutar da zata tadda mana fitinar da bamu da ruwan kashe shi"
"Ban gane ba Magaji?"
"Eh haka na faÉ—a." Ya juya abin shi bai kuma tanka mata ba, haka ta kwana cikin ranta a kudire da mugun niyya.
Asubar farko, ta nika garinta sai gidan Nahira.

Yana zaune a dakin shi na aiki ta same shi,
"Nahira meye kace akan yar kishiyata?"
Ta tambaye shi,
Lumshe idanun shi yayi yana motsa bakin shi.
Kafin ya bude idanun shi.
"Ban san me zai faru ba, sai dai goben su tana hannun abin Bauta. Bai zama dole sai na duba yanayin su ba. Sai dai ita Yar kishiyar ki zata iya zama farin ciki ga al'ummar Nahara"
"Y'a ta fa?"
"Ban san kome akan ta ba, sai dai ta kiyayye abin da take yi ita da Lati!"
"Karya kake Nahira! Ita sai ta zama fitilar farin ciki ga Al'ummar Nahara. Idan kuma kana ganin zaka iya tow ga fili ga me doki"
"Bakin cikin mutum shi yake kashe shi" daga haka ya nuna mata hanya.
Fita tai tana jin kamar ta kona gidan Nahira ta huta, tunda ya sake maganar ya shiga kunnen Magaji tayi imani cewa ba zai bar yar shi haka ba.
Dan haka koda ta isa gida, ta samu yaran suna ta diban ruwan amfanin gida.
Kallon Easter tayi bakin ciki da hassada ya cika ranta, yarinyar wata irin boyayyen halitta ce da ita, idan har nan da shekaru uku zuwa hudu, ta zama cikakkiyar mace, tabbas Yarta lokacin ta tashi aiki.

Shi yasa duk rintsi ba zata, tab'a barin ta tayi aure ba sai Wabi tayi taga inda Wabi tayi, kafin tayi nata wannan shine alwashin ta.
A can rafi wurin diban ruwa, Lati ne yazo yana jiran Abigail wato wabi.
Tana zuwa dake tasan da zuwan shi ta cewa Easter.
"Kin ga ki tafi ki dawo, kafin nan nayi wanka sai ki zo min da wasu kayan sawan"
"Hmm" ta bata amsa,
Haka ta dauki tulun ta nufi hanyar gida, ita kuma Abigail ta bi inda Lati yake mata magana.
Tana isa wurin shi ya amshi tulun.
Ya ajiye mata.
"Ina Kyauta?"
"Ta tafi, kafin ta dawo ai zaka gama" ta fada tana kallon shi.
"Eh amma ai kinsan ba zata dawo da wuri ba ko?"
"Eh ba zata dawo ba."
"Tow" ya janyota jikin shi, sannan ya shiga tab'a ta, ta ko ina.
A tsorace ta ce mishi.
"Kace min camfi ne babu wani abin da zai faru ko?"
"Ke babu abin da zai faru duk karya ce"
Ya zare fatarinta, ya shiga bin tsakanin cinyoyinta, wani irin kuka ta saka da ƙara.
Toshe mata baki yayi, shi ba yau ya fara ta'adin shi ba, amma ita ce mace ta farko da ya samu a matsayin cikakkiyar mace.
Ganin zai hallakata yasa ta fara kokarin kwacewa daga jikin shi.
Ai kuwa ya saka mata karfi baki daya, ta koma ta mike mishi.

Lokaci guda garin Nahara ya koma wani irin duhu da yanayi me ban tsoro, tashi yayi bayan ya gama biyan buƙatar shi ya shiga tattab'a. Amma iya bata motsi, ganin duhun har tafin hannun shi baya gani yasa shi, tashi a guje ya bar wurin duk da ba haka yaso ba.
-
Bude idanun shi yayi yana kallon garin.
Kafin ya hango Easther da take tafiya a tsorace.
_Nan da wasu yan kananan Lokuta kaddran yaranka zata sauya. Ita wannan babban al'amari yana bibiyarta Yar Uwarta kuma ban san me zance ba! Amma tabbas akwai abubuwan da ba kowa zai sani ba_
Bin ta yayi da ido kamar zai kirata, kafin yayi tunanin haka tayi nisa,
A bangaren Nahira fitowa yayi yana kallon yadda garin yayi duhu.
"Sun karya mana tsari da kariyar mu! Bamu da hanyar tsira." Ya faÉ—a.,

A hankali garin ya fara washewa, ya koma kamar da.
Ganin garin yayi haske yasa ta, nufar rafin anan tayi ta niman Wabi bata ganta ba. Sai a can ta hango kafarta.
Da sauri ta isa wurinta, turus tayi a tsorace ta sake ƙara zata juya Abigail ta riko kafar ta.
"Na hada ki da abin bautar Baban mu, ki rufa min asiri, kar ki fadawa kowa ki min alkawarin haka" cikin tsoro ta ce mata.
"Nayi me yasa miki?" Ta tambaye ta tana matsawa jikinta.
"Ya cuce ni yayi min dadin baki, yar uwata Easther ki min alkawarin ba zaki tab'a tona min asiri ba."
"Nayi miki babu wanda zai tab'a sanin haka"
Ruwan tulun ta dauka ta wanke Jikinta, suka nufi rafin tayi wanka suka koma gida, lokacin da suka isa gida, nan take bawa Mama Uwa labarin karya wai faduwa tayi a rafi bata ganin gabanta har ta fada akan wani kututture ya suke mata gabanta.
"Nice na taimaka mata ma"
Gyada kai Mama uwa tai, amma bata yarda ba.
"Kyauta ki boye maganar nan kar ki yarda ki gayawa kowa kin ji"
Gyada kai tayi tana tausayin Yar Uwarta.
Haka Mama Uwa suka yi ta kula da Abigail babu wanda ya sani.

Zuwa yamma likis, ta warware kamar babu abin da ya faru da ita,
Suna zaune a dakin su ita da Easther aka shigo gidan aka fada musu sakon me gari da Nahira.
"Ana kira ga Iyaye da Yan mata matukar sun san akwai abin da yarsu tayi toh maza su turata gidan Nahira a kashe ta. Domin tare abin da zai faru a gaba."
Riko hannun Mama Uwa tayi cikin tsoro.
"Mama Uwa!"
Girgiza kai tayi.
Zuciyar su baki daya a rabe yake, suna shiga cikin dakin su. Ta kalli Easter. Zubewa Mama Uwa tayi a gabanta tare da hada hannunta dukka biyu.
"Easter ki taimaka mana kar na rasa Wabi! Nasan boye min gaskiya ku ka yi...
```Haseer collection dealer ce kayanmu suna da sauqi sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayan mu cikin sauqi alhmdllh ga kadan daga ciki ina Matan iyayen giji! Yau ga sabon labari mun zo muku da shi kawo kunnen ku kuji labari.
1: royal jelly 2500 me 60pc babba 19k me 365pcs
2: sugar wanita 2500
3: extreme maca 4000
4: vitamin c 2200/2500
5: vitamin e 2000
6: gluta white 2500
7: khusus 3500
8: pesona 2500```
+

234 803 879 6871 zuku iya tuntubar Number nan.....

*A Hausa historical Ancient*
24/Nov/2022
#Mai_Dambu


Wacece Easter?
500₦... Insha Allah'
a tuntube wannan number 08130269641 Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu

*A Hausa historical ancient
#Mai_Dambu
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*
               Mai_Dambu...
Chapter 14 · 0% Book details