← Book details Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 18

BABI NA SHA SHIDA (16)

Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masarautar Deehar.

Yau kimanin shekaru ashirin da Takwas da rabuwa da duk wani me musu gani gani, don haka cikin nasara Galadima yana zaune wata hankaka ta shigo fadar. Tuni mayakan ko ta kwana suka fara kokarin farmakar shi, ya d'aga musu hannu.

   Sauka ya yi a kafadar Galadima, ya juya yana kallon hankakan. Kafin ya mike a hankali ya nufi cikin gidan, babban zauren saukar baki na musamman ya shiga. Hankakan ya tashi a kafadar shi ya sauka a kasa, a take ya rikid'e zuwa wani tsoho me yalwan farin gashi da tarin shekaru masu yawan gaske. Rike yake da sandar karfe yana dogarawa.
   "Duk da lokacin sa'a tana kara bunkasa nahiyar mu, shi yasa nake son na gaggauta gaya maka rundunar mayaka su nufi gaɓɓar takun Nahara. Sun karya alkadarin kauyen." Shafa kan shi yayi yana kallon Galadima.
"Kar ka manta ku kashe mazan kauyen da yaran su maza ku kamo matan zuwa Deehar ta haka zamu gane wacece me irin tasirin Nahara yadda zamu wanke ta mu bawa Arshan yayi kwana arba'in yana jima'i da ita, idan wa'adin ya cika zamu yankata sai mu mishi wanka da jininta yadda zamu mallaki karfin mulki da da farin jinin Nahara dan mace ce da ta shahara a duniya."

           Zubewa ya yi a kan gwiwar shi, yana me cewa.
"Nasara tana gare ka, na amince yau zamu kai farmaki a garin Nahara"
"Kar ka manta ayi yadda nace domin bunkasa nahiyar Deehar."
Daga haka ya koma hankaka ya hau kafadar galadima suka fito.

       Suna fitowa Fadar ya tashi sama yayi tafiyar shi, sannan Galadima ya gyara murya yana faɗin.
"Nan da dan wani lokaci, za a fara bikin mikawa Arshan mulkin shi. Dan haka yana da kyau kowa ya sani! Sarkin Yaki q shirya rundunoni da zasu tsallaka Nahara a farmake su farmakar da ba zasu manta ba. A kwaso mana mata da yan matan nahara kar wani badakare yayi gigin kallon wadannan matan domin mallakar masarautar deehar ce, matukar aka samu akasin haka toh kuwa ku shafe rundunar kafin ku iso deehar domin zan yi hukuncin da ban tab'a irin shi ba. A tsawon shekaru"
"Mun Amince!" Suka fada baki dayan su,
  Mikewa ya yi ya nufi cikin gidan, a bakin harabar gidan ya hango Fulani Babba da Yarima Shehu.
Bai san me suke tattaunawa ba, amma yadda ya fuskanci Yarima Shehu yana fara'a cikin maganar shi yayin da Fulani Babba wacce shekaru ya mata shura.
"Yarima Shehu kenan! Kana tsammanin har akwai mulkin da ya fi namu adalci? Idan na fahimta hasashen ka yana tafiya ne da cewa akwai wani wanda zai iya tsaya mana a gaba?"
Murmushi ya yi mara sauti, duk da shima shekaru sun fara ja. Ya lumshe dara-daran idanun shi, masu matukar kyau da haske kamar ta Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye. Ya bude su,
"Fulani ai ke uwa ce, sannan kin fahimci abin da nake nufi, abin da zai faru ke ce zaki fi kowa rashi. Kuskure anyi shi amma bana tsammanin daga haka akwai gyarar da zaku iya. Kar ku manta tunda kuka tab'a Abdullahi har yau kuna cikin firgici domin ku kanku baku san ta inda yakin zai fara ba. Shi can ya kawo miki labarin kauyen da idanunku yake kai" ya nuna inda Galadima yake tsaye, sannan ya juya yana tafiya da sandar shi.
Tun bayan kashe mutanen da aka yi, hatta Mahaifiyar shi sai da aka kashe, ta hanyar zuba mata guba.
Yan uwan shi kuwa raba kan su aka yi kowa yana jin haushin dan uwan shi.
Wai a haka shi daya ne kaf cikin masarautar yake gaya musu kuskuren shi.
Yanzu haka yayi aure yana da matar shi da Yaran shi biyu.
Aliyah da Khamil. Su kan yaran lafiyar su lau.
"Baka tunani akan Yaran ka ne?" Ta fada cikin kasaita.
"Kar ki damu da su, kiyi tunanin kanku  Yarana kuwa ko farcen su ba zaku iya kusanta ba, balle har ku cutar dasu. Suna tare da da kariyar Allah."
Isowa Galadima yayi ya gaishe ta, yana kallon bayan Yarima Shehu.
"Me yasa ba zamu kashe wannan abin ba?"
"Waye ya gaya maka irin su Shehu ana kashe su sakarai! Ai idan dasu dole adawar tayi yadda ake so. Sannan idan suna raye dole suga cigaban mu!" Ta fada tana bin bayan shi da idanu,
"Fulani! dama akan kauyen da aka kai Abdullahi jinya ne, yau mun samu labarin sa'a zata fara daga yau. "
Kura mishi idanu tayi, sannan ta kalli Yarima Shehu da ya yi nisa.
"Yaron nan da yana gani toh tabbas da na ce a hallaka shi, sai dai ya gama nakasa babu abin da zai iya sai hakuri. Ya gaya min abin da yake tafe da kai "
Ta fada tana kallon shi.
"Me yasa kuke son farmakar Nahara?" Nan ya mata bayani cikin wayo da dabara.
"Na gamsu amma ka sani dole duk yan matan da za a kai su ga Yarima Arshan a duba budurcin kowacce mace domin kar a dauko mana bara gurbi cikin gidan mu"
"An gama ranki shi dade." Ya fada yana kaskantar da kan shi.
Sannan ta juya ta koma cikin gidan, ya bi bayan ta da harara.
Baki daya sun saka rayuwar shi cikin wani irin yanayi, bashi da ikon kan shi sai nasu, sai abin da suka fada ko suka ce. Ana ganin shi kamar shi ke juya kowa amma wallahi shi ma juya shi ake kamar gwado.
★‡★
Nahara.
Tun da ta fito daga cikin gidan su, take tafiya tana share kwalla. Tabbas Mama Uwa tayi gaskiya, amma kuma itama tana da nata burin. Haka zata mutu bata ga mahaifiyar ta ba? Haka zata kare bata ga nata cigaban ba. Haka ta nufi gidan Nahara tana kuka..
"Ki koma bake ake nima ba, domin babu yadda hasken Nahara ya bar ki, haka ki koma"
_Idan har aka fahimci bake bane ki sani shima cin zarafin alummar Nahara ne dan haka ki tsaya tsayin daka, ki tabbatar da Nahira kece_
Kalaman Mama Uwa ya dawo kanta.
"Nahira nice me laifi ba kowa ba, ni na aikata"
"Ki koma nace"
Ya daka mata tsawa.
"Ba zan iya ba! Nice Nahira nice nayi laifin ni ce na bashi alfaharin Nahara! Ni ce na bada kadaran nahara, Nahira ka hukunta sabida zunubina kafin masifar da ake hangowa zata auku ta auku"
"Ai masifa kan ta auku! Bamu da tsimmi bamu da dabara abun da bamu shirya ba, shi samu gani. Duk da nasan ba ke bace. Tawo muje" ya shiga da ita dakin bokancinsa, ya dauki wata irin sarka ya daura mata a wuyarta.
"Kar ki sake ki rabu da wannan sarkan. Kyauta rayuwar ki cike take da albarka. Zaki gana da Mahaifiyar ki amma lokacin da yana da tazara. Yanzu ki tashi na kai ki wurin me gari a miki tofin altsine sannan ki sani kece zaki dawo da al'ummar Nahara "

Sai da ya gama bata wata irin sirrintacciyar ruwa, sannan ya saka ta a gaba izuwa fadar tunba. A take aka kwabe ta. Hawaye ne ya zubo daga idanun Nahira."
Sai da aka zane ta tare da farfasa mata jiki, sannan aka É—auki bakin shuni aka watsa mata. Sannan Nahira ya basu shawaran a dauke Yara maza da matasa maza a kai su tsibirin kakati.
Wannan tsibirin kakati wata irin sirrintacciyar wuri ne me É—auke da kariya tun shekaru aru aru, ana dauke maza ne idan aka fahimci akwai tarzoman da zata hallaka su.
Ai kuwa matasa suka ce babu inda zasu tunda ta iya bayyana kanta, Toh suma zasu bada rayuwar su domin kare Nahara.
Dole aka kwashe Yara musu tasowa aka tafi da su da tsofaffin mata da maza.
Kallon Nahara tayi hawaye na zuba mata.
"Me haka yake nufi?"
"Makomar Nahara tana hannun ki kyautah ruwanki ne ki dawo da yancin Nahara ruwanki ne ki rushe ta har abada. Ban sani ba ko zan rayu amma alhakin kare Nahara na wuyarki, kiyi amfani da damar da kika samu domin dawo da kufayin mu."

Hawaye ne ya zubo musu, sannan aka shiga yawo da ita gida-gida ana fadar abin da ta aikata. Abin tausayi masu zaginta nayi masu jifarta nayi,  kafin su dawo dare yayi, dan haka suna zuwa an hura wutar da zasu jefata, Babanta ya tawo da gudu aka riƙe shi.
"Kyautah ba zata tab'a aikata abin da ake zargin ta da shi ba, nasan tarbiyyar da na mata kar ku.."

Haske suka gani tare da fashewar wata irin abu, kafin kace me gidajen su ya fara ci da wuta gadan-gadan.
"Shi kenan! Ta janyo mana masifa da bala'i a cikin Nahara."

Hankulan jama'a ya tashi, kowa gudu yake ya domin ceton rayuwar shi, amma suna fara gudu, za ayi ta sake musu kibiya.
Matasan da suka shiga yakin, sune suka iya kare wasu mutanen, amma an gwabza yaki na fitar hankali, dake an ce sarkin yawa yafi sarkin karfi.
Kafin wayewar gari, sun yiwa garin Nahara barnan da bata a tab'a yi ba a tsawon tarihin kauyen, sannan suka tattaro mata da yan matan domin an hana a tab'a yan matan.
Haka aka bi gida gida, aka kwaso matan da suke gida a cikin su kuwa har da Wabi da Uwarta.
Idanun wani badakare ne ya sauka akan Easther wacce take zaune a takure tsirara, ta zubawa gawan Nahira da Baban ta, idanu hawaye na zuba daga idanunta.
Jini ya wanke mata jiki.
Gefenta gawar Saurayin nan ne da ya tab'a mata magana a dandali. An zo za a harbeta ya tare mata, sannan suka yi ta saran shi..
500₦
Mai_Dambu
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*
START YOUR GOLDEN HOURS NOW.... 08130269641 HURRY UP DON'T MISS IT...

               Mai_Dambu...
Chapter 16 · 0% Book details