← Book details Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 15 OF 18

BABI NA SHA BIYAR (15)

Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mijinyawa
Bamaguje da yake cikin kauyen Nahara, babban mutum ne da yake noma da kiwo, uwa Uba shi din baduku ne da yake sarrafa fata da jimar su zuwa wasu sassa domin fatauci.
Mijinyawa yana da mata goma sha daya, kuma a cikin matar shi nan babu wacce ta haifa mishi É—a sai dangana, matar shi ta sha daya. Lokacin da ta haifi Magaji sai ta mutu, ko ganin dan bata yi ba.
Magaji ya taso cikin kulawar matan Ubanshi goma russ din nan, domin sun fahimci idan kana son shiga toh dole ka kaunaci magaji.
Sai ya zama Magaji shi ne abin kishin matan gidan, domin kuwa kowacce tana kyautatta mishi ne domin kaunar Uban shi.
Duk da ba wani kishi aka yi a zaman su ba, sai gashi Magaji ya zama É—an da ake kishi akan shi kowacce so take lallai ta rike shi dan Mijinyawa ya so ta.
Asalin sunan Mijin yawa, Danladi ne amma saboda yawan aure aure yasa aka saka mishi mijin yawwa.
Saboda zumunci da jin dadin yadda suke kyautattawa dan shi yasa shi ma yayi musu ixinin su dauko yaran Yan uwan su.
Kafin Magaji ya cika shekara goma gidan ya cika da yara, kuma Mijinyawa shi ya basu damar rike Yaran kamar Magaji.
Saboda gata irin wadda Magaji ya samu yana da shekaru goma sha biyar aka mishi Aure da Uwa, sai dai Uwa ta kasance mace me yawan wabi.
Tana haihuwa dan baya wuce shekara daya ya koma.

A lokacin karfin Mijinyawa ya fara ja baya, sai ya fara fita da Magaji zuwa fatauci da sana'ar shi, idan suka tafi suna wata biyar wata shida.
Haka ya cigaba da tafiya da shi har Magaji ya cika shekara ashirin lokacin duk wadda ya ganshi ya ga cikakken namiji, ga kyau ga kuruciya.
Haka yasa duk inda ya shiga sai ya samu masu bashi mata, domin shi mutum ne me yawan fara'a da kamun kai.
A lokacin da ya cika shekaru talatin a duniya ya zama me daukar duk wani nauyi da gidan su baki daya.
A lokacin da ya kara zama shahararren attajiri a cikin garin Nahara, domin yana da jakuna na shi na kanshi, sannan yana da doki daya.
Domin fa a lokacin me arzikin sayan doki ba karamin attajiri bane, dan haka da yawan mutane sune mishi kallon me kashin kudi alfadari.
Ana haka Magaji ya tafi fatauci can gabashin nahiyar bakaken fata, inda ya sauka a kasar Habasha a lokacin.

Kwanan shi biyu, ya shiga kasuwa da kayan da yazo da shi, kasancewar basu samu irin kayan shi, sai suka fara saya kamar hauka. Kuma Allah ya taimaka yazo da jakuna kusan guda goma sha biyar da kayan, haka kayan suka yi ta karewa.

Magaji yana da baiwar fahimtar Yaren duk ƙasar da ya shiga,.kuma wannan dabi'ar Fatake ce. A cikin sati biyu ya iya Yaren su ta Amhara. Sosai a cikin satin na uku ya fara karya musu harshe, lokacin da ya cika wata guda zuwa biyu nan, suka hadu da Jessica, ita din yar ƙabilar Amhara ce da take cikin kasar babanta Babban malamin majami'ar catholic ne a wancan zamanin.
Duk da kuwa suna riko da addinin Kirista bai hana su bawa Yaran su abin da suke so ba, dan haka lokacin da suka ji labarin soyayyar ta da shi, sun kira shi suka mishi tambayoyi ya bada amsa yadda ya dace sai dai ya gaya musu shi bai san wata addini bayan maguzanci ba, basu yi mamaki ba, dan haka suka tallata mishi addinin su, wanda ya amsa hannu bibbiyu.  Uwa Uba bai boye musu yana da iyali ba, basu ki ba.
Domin suna son duk abinda Jessica tace tana so.
Ba ayi bikin ba, sai bayan ya dawo ya gayawa Mahaifin shi da matar shi, ai kuwa tayi tsalle ta diro ba zata zauna da kishiya ba.
Shi kuwa ya ce mata ba zai fasa ba, idan da ya bi na mutane toh tuntuni ya dace ya yanta wasu mata a gaban Nahira.
Jin haka yasa ta hakura, ta shiga faffutukar niman maganin da abin da zata haifa ba zai mutu ba.

Watan shi biyu ya koma aka yi auren shi da Jessica, suka bude rayuwa me albarka da kaunar juna.
A lokacin ya maida hankali sosai wurin kasuwanci da niman Ilimin addinin Kirista.

A haka suka shekara bakwai lokacin Ta haifi yarta Mace wacce a take ya saka mata suna da Kyauta, dan bai kawo zata haihu kusa ba.
Ta haifi yarinyar ranar Easter san haka aka saka mata suna Easter. Tare da saka mata Albarkan iyaye da kakanni. Da mata Kyakyawar fatan zama mace me daraja, domin sun yi imani duk macen da aka haifa ranar Easter zata kasance mace me darajar da babu irin ta a cikin alumma.

Lokacin da Easter ta cika shekaru biyar zuwa bakwai a lokacin Magaji wanda ya koma Jacob, ya dauki Jessica zuwa garin su, da tarin dukiya me yawan gaske. Domin iyayen ta attajirai ne.
Lokacin da suka isa garin Nahara, Easter ta fara wani irin zazzaɓi har da suma.
Aka suka mata yan dabaru kafin su isa gida, amma ina dole kafin su isa gida sai sun tsaya a gidan Nahira, domin shine akan hanya.
Amma wani abin mamaki shine suna isa kofar shi suka same shi a kofar gidan yana tsaye, da kan sa ya amshi yarinyar.
"Haba Nahara! Kishin ne ya motsa akan kyauta? A kyale ta mana, ai itama tana da irin hasken ki sai dai nata daban da naki! Idan har Nahara ruhinta me tsarki ne toh tabbas da kanta zata albarkaci kyauta"

Ya dauki lokaci yana magana kafin, Easter taja numfashi. Ya mikawa Magaji yana faÉ—in.
"A kula da ita, domin daraja ce da ita ba kamar sauran Yaran mu ba."
Da farko Jessica bata yi imani da abin da ya fada ba. Amma kuma lokacin da suka isa gidansu Magaji sai ta fara gasgata abin da Nahira ya gaya musu.

Jessica tasha mugun wahala a hannun Mama Uwa da sauran Matan Mijinyawa, domin macen da namiji yake so baya iya boyewa haka ya kasance domin Magaji ya kasa boye kaunar shi me girma akanta.
A lokacin Wabi wacce suna zuwa ya sauya mata suna zuwa Abigail, tana sa shekara goma. Yayin da Easter take da shekara bakwai. Tsana da tsangwama yasa baki daya basu sakewa a gidan sai Magaji yana nan, a hankali lokaci ya tafi. Ga damuwar gidan su Magaji yasa Jessica rokon shi alfarmar ya mai da ita gida, ta gaji ba zata iya zama a cikin gidan ba.
Fir yaki toh yana sonta, dan haka ta nemi taimakon Nahira, shi kuma ya roketa da ta bar musu Kyauta.

Ganin girman shi da abin da yake mata, akan matsalar Yarta yasa ta hakura ta bar kyauta, da saka idanun shi. A cikin yaran Magaji yasa mutane biyu suka rakata har garin su. Bayan wata uku suka dawo bayan an basu sakon Kyauta.
Haka yarinyar nan ta girma cikin wahala da azaba, idan Yaran gidan suka yi abu ita ake daurawa, ita kan ma ta saba abu na faruwa koda bata nan, ana fara magana zata ce ita ce.

Wabi idan tayi abu, karshe ita ce zata amsa akan ita ce, koda kuwa kashe Easter za ayi ita babu ruwanta, ita kuma Easter tana amsar laifin Wabi ne ba dan kome ba sai bata da kowa sai Wabi. Amma ita tana ganin ai dole Easter ta amshi duk abin da tayi domin ita ce karama.

Haka suka taso, kome ya faru zata ce Easter ce.
A dawo labari.
----
Jikinta yana rawa, taja da baya tana girgiza kai.
"Yanzu kin fi son ki ga an kashe yar uwarki? Haba Kyauta meye a cikin wannan duniyar da ban miki ba? Tun da Mamanki ta watsar dake na rike ki kamar nice na haife ki ashe ba zaki iya bada rayuwar ki domin Yar uwarki ba? Shi kenan ta je a kashe ta, Abigail wuce ki tafi a kashe ki, son kai da son zuciya yana tare da masu son dawwama a gidan duniya"
"Mama Uwa!" Abigail ya kira sunanta cikin kuka.
"Ki je bakome wadda ya miki haka Nahara ba zata bar shi ba, yara goma na haifa kece kawai naga girman ki, wayyo nayi asara na boni na lalace"
Riko hannun Abigail tayi, tana girgiza mata kai.
"Idan har na barki kika tafi waye zai kula da Mama Uwa kamar ki? Na amshi haka ba kome bane kake da saka ran samun shi. Na roke ki da ki kai Mama na wurin da aka binne ni" sannan ta share hawayen ta, ta juya ta fita daga dakin, ta wuce dakin Baban su. Ta zube a gaban shi tana kallon shi.
"Ban yi riko da Addinin mu ba, na fada hallaka na ci amanar Nahara, tsinuwa ya tabbata a kaina, zan tafi na isar musu da cewa nice na aikata zunubi mara iyaka, ka yafe min"
Daga haka ta juya ta fita daga cikin gidan, ajiyar Zuciya Mama Uwa ta sauke.
"Idan har ta mutu yau, tabbas zaki bar Nahara izuwa Deehar a can akwai rayuwa me albarka, zaki tafi can ki rayu koda a baiwa ce domin cika min mafarki na na haihuwar Kyakyawar Y'a irin ki"

"Mama ina ne Deehar?"
"Masarauta ce da take tsallaken ruwan Nahara, ki tafi can ki rayu domin ki nunawa Nahira cewa bai isa yayi kome ba. Alwashin sa akan Easter karya ne. Ke zaki rayu a cikin farin ciki da daula me yawan gaske!"

"Idan har haka ne toh ba makawa sai mun share tunanin me cewa ba zamu kai labari ba...
500₦
Mai_Dambu
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*

               Mai_Dambu...
Chapter 15 · 0% Book details