← Book details Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 18

BABI NA BIYU (2)

Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*Shashin Fulani Babba.*
Shashi ne me zaman kan shi wanda ya haÉ—a bayi maza da mata kusan guda sittin da bakwai saboda yawan hidimar Yaran ta maza biyu Yusif da Ado.

Duk inda Galadima Sule ya wuce zubewa ake a gaban shi sabida kwasar gaisuwa, har ya isa babban shashin Fulani Babba.
Can yayi ta keta manyan zaurirruka har uku, sannan ya isa babbar zauren ta da aka zuba manyan tumtum tare da jera su akan kyakyawar darduman, ya cire takalmin shi sannan ya shiga cikin zauren, ya hango.
"Assalamu alaikum!" Yayi sallama cikin dattijiyar muryan shi.
"Waalaakumun Salam, Abin mamaki batan kare da tsire tauraro me wutsiya sanin ka bala'i. Ganin ka masifa yau meke tafe da kai bayan ana can ana zaman makokin mai martaba?"

Kasake yayi kafin yayi kwafa ya ce.
" Hmm kowa yaki tsotsan yatsu bai ji zak'in miya bane waye ya gaya maka ganina yana da nasaba da iftila'i, ai gani na a gare ku shine mafi girma da alkhairi "

"Anya masu iya magana sunce a rashin kira karen bebe ya b'ata," fitowar Jakadiya ta zube a gaban shi tana faÉ—in.
"Tuba nake Galadima, Inda kaji mutum yana tsoron dare an daure shi ya gudu ne, Uwar É—akina tana marabtar ka"
Jinjina kai yayi sannan ya shiga cikin dakin tana kishingid'e kamar ba mutuwa aka mata ba, kanta sunkuye cikin tsananin isa da izza. Zubewa yayi duk da kasancewar shi Wanta babban Yayan su, amma yana bata wata irin girma me É—auke da ban mamaki.
"Ina mika sakon ta'aziyata" sai lokacin ta d'ago kai ta dube shi na wasu yan dakikai, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zaren yadin jikin ta na awalayo , murmusa mishi tayi sannan ta ce mishi.
"Domin rana daya ba a kin guziri ina jin ka" gyara zama yayi sannan ya kalli bakin kofar da jakadiya take tsaye. Itama kallon Jakadiyar tayi, dukar da kai tayi sannan ta fita daga dakin cikin girmamawa.
"Ko kin san  makomar faffutukar da muke ina zata tsaya?"  Ya fadi yana kasa da muryan shi.
Hura iskar bakin ta tayi wannan ta ce mishi.
"Duk saurin unguwar zoma ta jira a Haihu ko!"
Gyara zama yayi sannan ya kasa da murya ya ce mata.
"Bafa yadda kike tsammanin bane!  Domin ranar tsafi bunsuru ke kud'i." Kallon tambaya ta mishi.
"Wato Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya samu wata sad'aka a tafiyar shi wanda ake hasashen tana dauke da cikin shi" firgit tayi ta kura mishi Idanu.
Idan bai yi karya ba, wallahi kwalla ya gani cikin idanun kanwar shi.
"Me haka yake nufi? Shirun ki sarewa ce a gare ni"
Hawaye ne suka zuba daga idanun ta, sannan ta lumshe idanun ta, mikewa yayi ya fita. Domin tunda tayi shiru nan ba zata kuma magana ba, Hakazalika ba zata ce mishi cikan ka ba, Fulani Babba mace ce, da ba a sanin gaskiyar gaban ta, shi yasa ba kowa take hulÉ—ar arziki da shi ba.
Haka ta cigaba da zama babu wanda zai ce ga abin da yake damunta.
*Shashin Magajiya.*
Ita din Y'ace ga Wazirin Deehar, kuma mafi soyuwa ga Wazirin Deehar, kallon ta yayi cikin nutsuwa ya ce mata.
"Hayatudeen ya gaya miki garin da ya tsaya bayan fitar shi rangadi?" D'ago kai tayi cikin ya tsina fuska ta ce mishi.
"Bai gaya min ba, domin ai ba a dakina ya sauka ba, a wurin Kilishi yq sauka."
"Lallai anyi sake Dan zaki ya girma domin kuwa ya ajiye sad'aka da har ake hasashen tana dauke da cikin shi. Dayawan sarakunan masarautar Deehar ba samamun Deehar bane haka zalika ba haifafun masarautar bane da girman su suke zuwa masarautar"
Kallon ina ruwa na tayi mishi sannan ta cigaba da sha'anin gabanta, ta ce mishi.
"Kasan bani da matsala da mulki domin ko na shiga maganar ba zai min dadi ba, ina fama da Shamsudeen da Muntari da bana son rigima ko na hana ba zai tab'a bawa Yarana daman mulki ba, tunda dai ba samun haka xan yi ba meye nawa da tashin hankali? Ana takai wake ta kaya"

Daga haka ta ja bakin ta tayi shiru, da ya auna maganar ta, sai ya fahimci ta fishi gaskiya dan haka ya mata sallama.
*Shashin Kilishi*
Kawunta shine Malamai ya shigo har cikin gidan, ya mata nasiha sannan ya tambaye ta ko ta san wani gari ya tsaya rangadin shi na ƙarshe?
Shiru tayi sannan ta dubi Yaranta mata kanana, kafin ta ce mishi.
"Ban sani ba, amma anan ya sauka bayan ya dawo daga rangadin."
Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata.
"Nahira nasan halin ki, ba zaki fada bane kawai amma kin san inda Mai Martaba ya tsaya rangadin shi na ƙarshe "
"Wallahi ban sani ba Kawu" ta fada tana kallon kasa. Karkabe hannun shi yayi sannan ya fita tunda bata sani ba, babu amfanin dolanta mata, a bangaren Fulani Karama ita bata samu me tuhumar ta ba, domin kuwa ita din Bafulatana ce daga Masarautar Moddibo Adama wato yola.

Haka akayi ta binciken bayi da kunyangi da suka raka Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye rangadi amma ba a samu wanda zai ce ga inda suka tafi ba.

Shima wannan ba karamin tashin hankali bane, gashi Ya Musa an nime shi sama da kasa ba a gan shi ba.
Ranar da ya cika kwana uku, aka samu wata baiwa da aka yi tafiyar da ita.
Sai dai wani abin almara, koda ta zo babban zauren gidan ana sauraren ta, sai ta kasa magana, haka buga mata tsawa ta zabura tana zare idanu. Tana buÉ—e baki zata yi magana baki daya muryan ta, ya dishe. Tayi tayi ta fadi inda suka tsaya kafin sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya sallame su ta kasa fada.
"A zane ta, sai a korata karya take"
Dayawan manyan Fadar basu yarda karya take ba, masu idanu a duhu sun fahimci inda matsalar take ba zata tab'a fada ba, domin akwai mutanen boye masu bawa Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye kariya musamman abin da ya shafe shi.
Haka tana ji tana gani aka zane ta, sannan aka fitar da ita. Fitar da wani kundi aka yi Sarkin Gida ya mikawa magatakarda ya fara karantawa.
_"Ina farin cikin rubuta yar karamar labarina domin isa inda nake bukata! A raina da zuciya ta. Naji ina son nayi rangadi a cikin duniyar nan domin shan iska! Duk da akwai ciwo da kuma zafin da nake ji a tsawon shekarun saba'in da takwas da nayi ina mulki. Sai dai na kasa fahimtar A ina matsalar nakasar da Ahalin sarauta suke samu? Nayi bincike ga aljanu da mutane sai dai al'amarin da daure kai! Amma na kuma fita ko zan samu maganin ciwon Ahalin Noye da suke rab'e a cikin Masarautan Deehar _
Daga nan ya kuma buÉ—e shafi da aka yi rubutu da tawada a kai sannan ya cigaba da cewa.
_Tabbas a iya shekarun da suka rage min zan yi kokarin kawo karshen rikicin da yaki ci yaƙi cinyewa na matsalar nakasar Ahalin masarautar Deehar. Sai dai bani da tabbacin hakan me yiwuwa ce domin na fahimci akwai musababbin da mafarin haka! Zan yi kokarin ganin nayi koyi ga Magabata na! Ko Allah zai saka a samu wanda zai hana haka? Sai dai nasan baki daya zuri'a ta, nakasassu ne! Da wannan nake muku fatan Alkhairi _
*HAYATUDEEN ABDULLAH NOYE*
Kallon juna suka yi ba tare da sunce kala ba, domin ya tabbata dai ya boye wata kusurwa.
Haka Alkali yayi gyaran murya sannan ya ce musu.
"Marigayi Hayatudeen yayi tafiya ga manyan masarautun ƙasar Hausa, dan haka zamu fara bincike ta can za a tura jakadun mu, ko ina idan yaso idan aka samu ya ajiye sad'aka a tawo da ita domin ta haifi abin da take dauke da shi, domin samun damar yin adalci ga kowa dan haka babu rabon da za ayi dole sai an samu inda ya ajiye sad'akar shi sai a san abin yi"

"Allah ya hutacce da mutane wahala."
Haka aka wakilta amintattun dakarun Masarautar aka raba su tare da tabbatar da an basu nan da kwanaki arba'in su kawo duk matar da aka tabbatar da ita din sad'akar sarki ce.
Abin da ya dagula musu lissafi ba kome bane sai b'atar dabbon da Ya Musa yayi domin dai babu shi babu labarin shi. Dan haka
A kowanne bangaren kokari suke ace an samu nasarar samun matar sai dai abin mamaki tsawon kwanakin da suka dauka da yawon da suke na bin masarautun yankin baki daya babu labarin haka. Sannan an yi matukar bincike masu bin bokaye da yan bori suna yi, masu bin kome ana yi amma babu labarin kaf hankalin su ya tashi.

★
A gaban wani kasungurmin boka suke zaune wanda ya raba kasa da sama yana zaune akan iska ya kyalkyale da dariya sannan ya ce musu.
"Ku gama wahalar ku, tabbas haka zai faru kuma ma nace ya samu, sai dai zamu yi kokarin tura wakilan mu a duk inda suke su kawar mana da su, amma kusani mulkin nan da kome zai iya zama a hannun ku. Amma bai zama dole ku samu yadda kuke so ba.

Ba mamaki hakkin jinin shi ya saka ya bibiye bakar inuwa, wacce zata haifar da masifa da bala'i, idan kuka yi imani da haka zaku cika dukkan muradin shi zai iya zama kariya a gare ku"

"Ya shugaban mu, mu masu biyayya ne ga duk abin da ka saka mu akai koda kuwa haka zai kai ga bada rayuwar mu ne, so muke Deehar ta zama gaggarabadau ga tsararrakinta, tafi kowacce masarautar mulki yadda za aji shakkar tunkarar mu."

"Anyi muku lamani"

★

Yau kwanaki hamsin da rasuwar Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, a hankali mahaya dawakan suka isa cikin masarautar, suka  shiga cikin sassarfa sannan suka nufi bargan dawakai suka ajiye dawakan. Suka nufi kofar fada.
Suna shiga suka zube tare da kwasar gaisuwa.
Kallon Juna suka yi sannan suka ce.
"A bisa binciken da aka tura mu, toh zamu iya cewa Alhamdulillahi sannan gefe guda wasu Wuraren babu nasara, sai a wani ƙaramin gari ne da muke tsaya kafin mu isa masarautan kwantagora. Mun samu labarin Marigayi Sarki Hayatudeen ya tsaya a garin inda ya sayi wata baiwa suka wuce. Sannan muka shiga ga masarautar kwantagora inda muka samu wannan baiwa me suna Deli.
Sai dai mun so dawowa da ita amma Sarkin kwantagora ya hana mu dawowa da ita inda ya ce mana.
Ba zai bada ita ba, domin sai ta haihu ko kuma a turo wasu manyan da zasu tafi da ita gudun kar a halaka da abin ita da cikin ta"
Shiru fadar ya dauka wato duk yadda aka so hana dauko wannan al'amarin sai da aka samu waÉ—anda suka binciko ta. Dayawan ransu yayi mugun B'aci dan haka suka boye domin kar su fitar ya zama matsala...
*NAHMIFAK*
_Collections_

```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```
*Ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare*
Taku har kullum
#Mai_Dambu
Saturday/November/2023
*Hausa Historical Ancient*
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*

EXQUISITE WRITERS FORUM
```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan  Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```

               Mai_Dambu...
Chapter 2 · 0% Book details