BABI NA HUÆŠU (4)
Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Tabbas haka ne, mu uku ne tare da Sad'akar Mai Martaba " Waziri ya fadi haka,
Shiru yayi yana kallon can gefe guda, sannan ya ce musu.
"Me yasa kuka dawo da ita? Me yasa baku bar shi a can ya rayu lafiya lafiya ba? Kun manta inda muke ne? Bai zama dole ya kai labari ba. Dan haka Ya Musa hakki ne a kan na kare rayuwar shi."
   Kamar wadda aka watsa musu ruwa, suka yi shiru suna kallon shi. Fitowar Fulani Karama ta kalli Kubra da take tsaye. Sannan ta juya ga Waziri.
"Baba Waziri lafiya?"
"Ita ce sad'akar Marigayi shi ne nayi tunanin kawo ta kafin a gyara wancan wurin."
Sake kallon Kubra tayi, yarinya ce karama ba babba ba, dan haka ta kalli Yarima Shehu. Kamar yasan tana kallon shi ya ce mata.
"Ki daina kallona Ammah, ki kalli abin da yake gaban ki." Lumshe idanunta, ta yi sannan ta kwalawa baiwarta kira ta ce mata.
"Shiga da ita d'akin da yake gefen turakata."
  "Toh uwar ɗakina" sannan tayiwa Kubra Jagora har dakin da yake shirye.
"Allah ya saka da alkhairi, Kubra da abin cikinta, amana ce a gare mu don Allah."
Mikewa tayi tana faÉ—in.
"Abin kasuwa na mai ciniki ne, idan ta iya ta tsira. Idan ta fadi a rasa kowa ya huta."
Jinjina kai Waziri ya yi sannan ya ce mata.
"Na gode Fulani, fata na gari lamiri." Sannan suka fita, cak ta tsaya a bakin kofar shiga cikin bangaren ta.
"Ammah lokaci ne yayi da zaki cika wasu mafarkan, domin masu iya magana sun ce ba ni in ba ka, shi ne tanka."
Juyawa tayi ta zuba mishi idanu.
"Mafarkina akan ku yake!" Ta fada a fusace.
"Bikin Magaji bai hana na Magajiya, wannan fa so min tab'i ne." Ya fada yana me tafiya da sander shi har bangaren shi.
Bin shi tayi tana kallon shi, tabbas akwai boyayyen al'amari a cikin kan d'an nata, sai dai kuma al'amarin yana bata tsoro. Ranar da Mai Martaba zai rasu da tafiyar shi da abin da ya faru sai da ya labarta mata. Tare da bata shawaran boye wasu abubuwan a ranta. Har ya kusan fita ya ce mata.
"Kin zata haka kawai na ce miki ki amshi kiran da zai zo daga gare su Ammah? A ranar da Abba ya dawo naji ba na jin al'amarin d da yake fita a jikin shi idan ya kusanto ni. "
Murmusa mata ya yi, sannan ya juya yana kallon inda take tsaye duk da baya gani kuwa.
"Koda aka ce ya rasu naje dakin ni da sauran Yan uwana, amma ban ji haka daga gare su ba. Matar da suka gabatar a fada ban ji tana da nasaba da haka ba, murmusa mata yayi sannan ya ce mata. Mafarin ya iso dole ki tsaya a tsakiyar su, domin iftila'in da yake tafe ya wuce sanin me tunani. Ki taya Abba yaki."
Â
       Juyawa yayi a hankali yana tafiya, yayin da yake lalube da sandar shi. Ta jima tsaye a wurin kafin ta wuce ta bawa Barirah umarnin ta kai mata abinci, har cikin dakin ta same ta. A takure kanta a sunkuye.
"Gashi inji uwar gijiyata." Amsa tayi tana me cewa.
"Na gode" sannan ta ajiye abincin tana kallon shi, juyawa Barirah tayi zata fita, Kubra ta ce mata.
"Akwai mutanen da nazo da su, ba zan iya cin abincin suna can a waje ba." Shiru Barirah tayi sannan ta fita zuwa wurin Fulani karama ta gaya mata yadda suka yi. Kallon juna suka yi kafin ta ce mata.
"Ki musu iso, zuwa dakin."
Daga haka ta cigaba da gyara abin da take, abin ya bata mamaki domin dai nan iyakarta ce, kuma taya za ayi ta zo mata har da nuna ga yadda take so.
★‡★
Tsoma isga yayi me É—auke da gashin saniya, ya watsa a jikin wuta.
Kurawa wutar idanu yayi, kamar wadda aka wurgo shi ta shigo dakin.
"Samu taya haka zai faru?"
Watsa isgar ya yi cikin wuta, sannan ya kuma tsomawa cikin jinin da yake cikin kokon kan mutum ya watsa a wutar.
"Kwantar da hankalin ka! Ai inda ba kasa nan ake gardaman kokuwa."
Inji Samu,
"Amma kasan mun yarda da kai? Kuma a tsawon shekarun nan mun alkawarin ba zaka tab'a barin ya hadu da wata mace."
Mutumin ya fada yana kallon bokan,
"Ƙaddara da rabo!" Ya furta yana kallon mutumin.
"Idan har a kwai su toh babu abin da zamu iya, sai ma mu rasa yadda muke so, dan haka tunda an samu haka zamu yi kokarin da zai saka duniya ta girgiza."
Tashi yayi sannan ya ce mishi.
"Tabbas ina son mu ji sabon labarin nan da gobe da safe!"
"Toh bari mu ga, amma dole sai an d'aga kafa domin ka'idar masarautar ku ce" Samu ya faÉ—a a hankali yana sauke numfashi.
"Kwana uku na bada ayi duk uwar da za ayi, domin rashin mutunci biki ne, kowa ya yi maka ka rama masa." Gyada kai Samu ya yi, sannan ya ce masa.
"Hmm rikicin duniya da me rai ake yin shi, don haka kwantar da hankalin ka zamu yi kome a hankali."
Fita yayi abin shi, sannan ya bar boka Samu yana aikin tsubacce tsabuccen shi.
★‡★
Tunda suka isa masarautar, Magajiya ta samu labarin ai Waziri ya kai sad'akar Marigayi wurin Fulani karama, ranta ya tab'o. Shigowar Amintacciyar baiwar ta, Zuwaira ta zube a gaban ta, Zuwairah tasan sirrin gulma da munafunci. Gata ba ta cika magana ba, amma ta iya had'a husuma ta koma gefe tana dariya.
Duk da Allah ya mata baiwar kyau da sura me kyau amma ya zama a banza, tsabar munafuncin ta.
"Uwar dakina a kace min kina kirana."
Shiru Magajiya tayi mata, kafin ta ce mata.
"Kina da labarin sad'akar Marigayi a wurin Fulani karama ta ke?" Murmusa mata ta yi, sannan ta ce mata.
"Hmm! Sandar dukar gurgu, yana kallo ake saro shi. Uwar dakina ai wannan ba sabon labari ne, domin dai Mahaifin ki ya dauki sad'akar Marigayi ya kaiwa wacce munafukar matar."
"Tabdijam lallai saniyar da bata da Jela, Allah ke Kore mata kud'a." Magajiya ta fadi haka cikin jin haushi, a ce mahaifinka shi zai zama tsanin ruguza ka.
Kamar Zuwairah ta san abin da Magajiya take tunani ta ce mata.
"Ai wasu dangin al'ajabi ne, suna tare da kai suna maka yankar baya. Allah na tuba, ai tsuguno bata kare ba, an sai da kare an sayi mage. Yo wannan ai shi ne burmawa kai wuka."
Sake cika tam Magajiya tayi tana kallon Zuwairah da take kara mata ingiza me kantu ruwa.
Mikewa Magajiya tayi sannan ta sallame Zuwairah.
Domin kara mata zafin kai take akan wanda yake cikin shi.
Sai kai gwauro take tana kai mari, ta rasa meke mata dadi domin tana hango yadda mahaifin ta, ya ci amanar ta, a kan idanunta ya tafi ya dauko matar da suka haÉ—a miji da ita, sannan ya dauke ta, ya kai wa matar da suke asalin kishi kamar zata mutu. Domin ko ba a gaya maka ba, lokacin da sarki Hayatudeen Abdullahi Noye yake raye yafi nuna kaunar shi a kan Fulani karama, da Yaran ta.
---
Sauran dakunan cikin gidan, sun ji labarin abin da ya faru. Sai abin ya zama kamar da ba'a da isgilanci, yadda aka fara sakewa bayin Magajiya magana marasa dad'i.
Wannan ya kara fusata Magajiya, domin wannan ai cin mutuncin ta ne, dan haka ta saka aka kira mahaifin ta, shiru suka yi.
"Baba me ka aikata haka? Kasan yadda ake zaman kishi a gidan nan, amma har zaka dauko wata sad'akar Marigayi, ka kaiwa Fulani karama ai sai a watsar da ita idan taso ta rayu ko ya mutu"
"Ikon Allah, amma ke na fara kawowa Kubrah kika ce baki bukata ko? Toh ita da ba ni na haife ta baki ga ta amshe ta ba?" Kura mishi ido tayi, kwafa tayi sannan ta mike tana faɗin.
"Umma, umma biyu, ta fi umma ɗaya. Kuma ina baka shawarar ka warware batun ajiye ta wurin Fulani karama."
Murmusa mata ya yi, sannan ya ce mata.
"Yau da gobe kayar Allah, komai gudun mutum ta kamo shi, dan haka babu gudu babu ja da baya a can zata zauna."
"Baba har da kai, za a min zagon kasa?"
Kwafa tai ta wuce dakin ta, kad'e babban rigar shi yayi ta wuce abin shi duk abin da tayi ita ta sani ba zai fasa kudirin shi ba.
--
Kwana biyu a tsakanin, Kubrah ta koma sabon bangaren ta, inda aka zuba mata bayi da kunyangi, bayan waÉ—anda tazo da su, Ya Musa yana kan ta, ita da abin cikin duk wani abun da ake bukata yana tsaye.
Kwanan ta uku da shigowa Masarautar.
Da dare, tana barci sai wani irin take, mafarkin ga wasu kuraye sun taso ta, a guje sosai suke bin ta da gudu.
Dakyar ta fada wani rami.
ramin kuma ruwa ne a cikin shi, tana kokarin fitowa taji kamar an daki cikinta. Zafin dukar ya saka ta bude idanun ta a zahiri.
Tana me share zufar da yake karyo mata, a tashi ta yi tana me nufar meke wayin ta, ta kama ruwa sannan ta fito, inuwar mutu ta gani, da sauri ta koma wuce gadon ta, ta kwanta.
Dakyar barci ya yi gaba da ita. Cikin barcin ta fara jin ciwon ciki kamar zata mutu. Haka ta yi ta dungure. Har kusan asuba, asuba nayi ta samu barci me dadi ya dauke ta..har ta fara barcin, ta ji kamar tana fitsari a kwance. Dakyar ta mike sai dai ta kasa tafiya, kara ta kwala.
.....
Fri/Nov/2022
#Mai_Dambu
*A HAUSA HISTORICAL ANCIENT*
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *......DASHEN ALLAH 🌳*
        Mai_Dambu...