← Book details Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 17 OF 18

BABI NA SHA BAKWAI (17)

Dashen Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Baki daya idanunta da ƙwaƙwalwarta ya tsaya cak da aiki, tana zaune ne amma idanun ta da tunanin ta abu daya suke ta maimaita mata. Wato kashe Baban su da Nahira tare da dan Gidan Nalado. Maza uku da suka nime kare ta, domin kar a kashe ta a kan idanunta aka kashe su.
Duk gaggara da rashin jinta, sai da ta kai tana tsanar kanta.
Fisgo kafarta badakaren yayi da karfin tsaya ya fara kokarin zare mazargin wandon shi. Tare da jan ta gefen da babu hayaniya, ita kuwa sai bin shi take, yana kai ta wurin ya ture ta ta fadi ƙasa kanta ya bugu da wani dutse, "dumm!" Kan ya mata tana jin yadda yake ratsa cinyoyinta da abin da bata san meye shi ba idanunta a rufe suke rub. Sai dai jin karar da taji da zubar ruwa me dumi yasa ta bude idanunta.
Tana kallon gawar badakaren wanda ya zube a jikinta matacce. Ajiyar zuciya ta ja daga nan bata kuma sanin me yake faruwa ba, sai da rana ya kwala sosai. Ta bude idanunta tana kallon inda suke a katon jirgin ruwa suke.
A hankali ta tashi zaune tana jin Jikinta kamar an daureta, ga kayan da bata san irin shi ba, an daura mata.
Kallon matan garin Nahara yasa ta rarrafawa zata nufi wurin su.
"Tsinanniya mara albarka karki zo inda muke kar mu ma rashin albarkanki ta shafe mu."
Inji Mama Uwa,
Cak ta tsaya tana kallon su, koma tayi ta kwanta tana haki, tare da rungumar kafarta tana kuka.
Sautin kukanta ne yasa Sarkin Yaki takowa har inda take, ya durkusa ya mika mata wani gurasa.
D'ago kai tayi tana girgiza kanta.
"Amsa kici" ya fada yana mika mata, tashin hankali da damuwar da take ciki ya ishe ta, ko yunwar bata ji.
Amsa tayi ta ajiye a gefenta.
Tana ganin yadda aka bi sauran matan da b'antaren gurasan,
"WaÉ—annan matan baki dayan su, mallakar Deehar ce kar wani yayi gigin tab'a koda hannun su ne, domin suna karkashin kulawar Masarautar Deehar ce. Kamar yadda ya faru da Fairoz haka zai faru da duk wanda ya kusanci daya daga cikin su, wannan sakon Galadima ne da Fulani Babba."
"Mun ji, mun amince." Suka fada baki dayan su.
Mika mata goron ruwa yayi ta shige abin shi, domin bata wuce sa'ar Yar shi Rayyanah ba. Ruwan tasha ta wanke fuskar ta.
Sannan ta kalli yadda suke cin gurasar hannu baka hannu ƙwarya, sannan ta fahimci ita yar gata ce domin ba a daure ta ba, kamar su yadda aka saka musu igiya aka daura su.
Rarrafawa tayi ta turawa Abigail gurasarta. Sannan ta koma ta kwanta. Kafin ta mike tana tafiya a hankali, har ta isa bayan jirgin. Tana kuka kamar ranta zai fita, tare da dukar kirjinta. Tana kallon yadda suka bar garin Nahara wuta naci da alamu an shafe ko ina babu wannan Albarkan da ake da yakinin suna da shi.
Jin shashekar kukan ta yasa shi lekata.
Yana ganin yadda ta rike kirjinta tana kuka.
Yasa shi fitowa har inda take.
"Yarinya me yasa ki kuka?"
"Garin Nahara" ta fada tana kallon shi.
"Me yasa kuka mana haka? Meye muka muku da zafi haka? Bamu tab'a cutar da kowa ba, hatta dabbobi suna da ikon tafiyar da rayuwar su yadda suke so me yasa?"
"Shekaru ashirin da takwas, an kawo wani mara lafiya garin ku, tun daga lokacin ake son sanin ta ina za a karya garin ku, domin laifin su na amsar mara lafiya"
Jiri ne ya kwashe ta kamar zata fadi.
Ta koma ta zauna a ƙasa, sai hawaye shar da yake zuba mata.
"Laifin mu kawai taimakon da Nahira yayi?" Ta tambaye shi tana kallon shi.
"Ba shi ne laifin ba, akwai wata gaskiyar da ya boye akan Yaron, dan haka ake niman shi a lokacin ruwa a jallo, ba a samu shiga Nahara ba. Karshen Yaron mara lafiya ya mutu."
Wani irin razana tayi tare da ja baya.
"Shima ya mutu?"
"Eh Deehar bata daukar reni, sannan bata daukar ganganci. Tana aiki ne bisa fasalin da ta zama Yarinya ta kar ki kara tambaya ta"
"Kun kashe min Babana! Kun kashe Nahira min, sannan kun kashe shi a daidai lokacin da ya bada rayuwar shi domin ceto na! Idan har na shiga ina kace toh Shegiya aka haife ni " kafin ya fahimci abin da take nufi, ta fada ruwa tsundum.
"Ina kuke!" Da gudu dakarun suna iso, dan haka suka fada ruwa, domin ceto ranta.
Koda suka fada tasha ruwa sosai, cikinta yayi tirtsitsi, tana fitowa yasa aka kunce wasu mata biyu, suka matse cikinta, sai ga ruwa ta hanci da baki.
Sai da tayi ta aman shi, sannan barci yayi gaba da ita. Lokacin da ta farka sun isa garin Deehar, a bakin ruwa suka tsaya, shi yasa aka tashe ta.
Ganin wata duniya, da bata tab'a ganin shi ba. Yasa ta koma zata lumshe idanu, Abigail ta ce mata.
"Wasan kwaikwayon ya isa haka." Sake bude idanun tayi, taga suna mikewa, sai lokacin ta lura itama daure take da igiya hannu da wuyar ta,  suna shiga kofar garin aka fara rangad'a gud'a, ana jifar su da tumatur, ana musu bakar magana.
Kafin su bar cikin talakawan Deehar, an wulakanta su, haka suka wuce har zuwa lokacin masarautar Deehar.
Rike hannun Abigail Mama Uwa tayi tana faÉ—in.
"Na gaya miki, kina da farar ƙaddara, shi yasa muka samu kan mu da shigowa cikin Deehar, idan har muka yi biyayya toh wata rana sai kin haifa mana jinin gidan nan."
Tana jin su bata yi mamaki ba, domin tun a jirgin ruwa ta fahimci bata da kowa sai ita É—ayan ta.

Ai kuwa suna isa cikin Masarautar, aka fara nuna musu hanyar da zasu nufa.
Yan mata aka raba su da iyayen su, tare da nuna musu wani hanya.
Su kuma iyaye mata aka nuna musu hanya.
"Mama!" Abigail ta fada da ƙarfi, tana niman isa wurinta.
Janta aka yi tare da labta mata bulala, ihu ta tsalla, wani bafade mara imani da tausayi ya daka mata tsawa.
Hadiye kukan ta.
Easter ta riko hannunta, suka nufi hanyar da ake nuna musu.
"Kyautah Mama Uwar!"
"Kar ki samu za a dawo mana da ita." Ta fada tana share mata hawaye.
Haka suka nufi wani babban gida me ɗauke da wata ƙatuwar zaure.
Sannan aka watsu kamar dabobbi.
Kaya aka kawo aka bisu da shi ana basu, kafin aka ce musu.
"Ku tashi, kowacce ta ajiye kayan ta, sannan akwai zanin wanka a can dakin ku yi tafiyar jerin gwano, zaku kowacce ta dauka ta dawo wurin kayanta"
"Toh"
Haka suka yi ta shiga dakin, suna daukar zanin wankar me kyau da kauri.
Sannan suka dawo wurin kayan su.
Suna tsaye aka nuna musu wata ta kofa.
"Zaku shiga wancan dakin, za a duba yan matancin ku!" Kallon juna suka yi, Abigail ta rike hannun Easter hankalinta a tashe.
"Kyautah"
"Meye?" Ta tambaye ta,
"Zasu bude gaban mu ne su duba,"
"Toh ba shi kenan."
"Kyautah ki taimaka min, kar su gane ni"
"Wannan Alƙawarina ne!"
Haka yan matan suka yi ta shiga, sai da aka zo kan Abigail,.tana shiga da Easter ta fasa wata irin kara, ta zube a wurin tana hauka da bori. Dole ba a duba Abigila ba, aka turota masu dubawan suka leko.
"Wacece yar Uwarta."
"Nice" Abigail ta fada Jikinta yana rawa.
Ta kama Easter ta kaita gefe, ganin murmushi akan Abigail yasa ta, fahimtar ba a duba ta ba. Dan haka ta ware ta koma layin karshe.
A hankali yazo kanta.
Tana shiga suka sakata ta cire kayan jikinta.
Sannan suka bude kafarta, tare da saka wata karfe me kama da halittar da namiji, a tsorace.
Sakamakon azabtar da ta ji.
Haska wurin suka yi, suka samu kofar a rufe take da angurya yayi kaca-kaca a wurin.
"Tashi ki daura zanin wankar ki"
Tashi tayi a hankali.
"Kande ita zamu sakata a cikin sunayen masu zuwa bangaren waye kenan?"
Kallon Easter tayi sannan ta ce mata.
" A kaita shashin Yarima Shehu, dama suna niman me yiwa Fulani Aliyah hidima! Sauran da daya ta dazun a kaita bangaren Fulani Babba, yan mata uku a kaisu bangaren Kilishi. Guda uku akai bangaren Magajiya. Sai biyu a kai su ɓangaren kwarkwarah Biyu Zinaru da Zuwairah. Sauran a duba kosassun cikin su a kai su ɓangaren Yarima Arshan a can zasu yi ta mishi hidima."

Duk da an raba basu, amma sai da aka banbanta su daga kayan sakawan su.
Abigail an basu koriyar doguwar riga. Sai wasu jajjayen riga, Easter an bata kalar zinari domin kalar ita É—aya ce da shi.
Sannan aka tara su a wuri guda.
"Zaku fara aiki daga gobe! Sannan dokokin masarautar Deehar, ta haramta Sata, idan kayi sata za a yanke maka hannu. Idan kabi namiji matukar ba wanda aka zab'a maka ba, sai an maka bulala, idan aka kama ka da laifin cin amanar masarauta za a kashe ka. Idan aka same ka da É—aukar zancen wani bangare a kai a kai wani bangaren toh a kai ka gidan Yari, sannan kowacce ta zauna inda aka kaita ban da yawon duba inda aka kai yar uwarki, ban da Gulma da yad'a labarin da ba haka ba. Abin da ya kawo ka shi za a kayi idan har aka same ka da laifin haka toh hukuncin ka kisa ce. Sannan lallai dole kullum ana zuwa amsar abinci a wurin girki muje ku ga wurin"
Haka aka saka su a gaba suka tafi.
Sannan Kanden ta ce.
"Wajibi ne idan inda kika aiki suna nemi ki kwana kizo, ki sanar mana bayan gari ya waye kin gama aikin ki, toh ki dawo wurin nan, domin akwai gyare-gyaren filin masarautar Deehar da Harabar shi."

Suna isa wurin girkin shima zaure ne babba.
"Barka da zuwa, Uwar Bayi Kanden" jinjina kai tayi, sannan ta juya ga Yan matan.
"Nan ne wurin abincin ku, kowacce ta dauki kwanon ta kuma ban da hayaniya." Ta fada haka suka yi ta dauka. Kallon Easter tayi da take tsaye.
"Ke!"
"Baki ji bane?"
"Naji" ta fada dan haka tana isa wurin daukar kwanon, ta dauki nata ta koma gefe.
Kallon yadda doguwar rigar ya kwanta a jikin yarinyar, duk da yanzu ta fara girma, amma tana faɗin kafin nan da wasu shekaru kugunta yafi haka fadi da bunƙasa. Zata tsaya sai yarinyar ta isa matakin mace. Amma ba zata yarda ta barta a haka ba.
Hango Mama Uwa Abigail tayi, da sauri ta nufi inda take tana cewa.
"Mama na" itama Easther ta nufe su.
Dakatar da Easter tayi tana faÉ—in.
"Kar ki tako inda nake! Tsinanniya wacce ba zata yi albarka ba."
Kallon Easter matan dakin suka yi.
"Garin mu ya haramta mace ta bawa namiji kanta. Amma wannan tsinaniyar ta ja mana bala'i. Duk wanda ya rab'e ta sai ya fada masifa."
Takawa Uwar Bayi tayi iyaka wurin ta.
"Wace ce miki ita?"
"Yar mijina ce"
Mama Uwa ta fada da kwarin gwiwa.
"Toh ki adana kiyayyarki, domin ba zamu dauka ba....
🤣😭 Yau kamar wacce kuka min asiri nayi typing dayawa!
500N
Mai_Dambu
1/7/23, 09:49 - Buhainat: *.....DASHEN ALLAH 🌳*

               Mai_Dambu...
Chapter 17 · 0% Book details