← Book details Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan ya fita bai tsaya ko ina ba sai gidan aliyu ya kirashi a waya sannan yace ya shigo bayan ya shiga Sun gaisa da xulaihat matar aliyu sannan aliyu yace xo muje dakina nasan bakin nan naka akwai magana,
Aliyu ya kafe affan da idanu yaga duk ya rame ya fita hayyacinshi sai yaji wani tausayin shi yana shigarshi aliyu yace affan kaganka kuwa kaga yanda ka koma duk karame wlh inda nine tuni saina cika Burina tab
Affan yayi shiru duk yaxama wani silent yace aliyu umma bataso
Aliyu yace to fada mata xakayi ne?
Affan yayi murmushi yace bakasan halin umma ba Amma gsky nima haqurina kai qarshe Dan wlh idan tayi wasa xata rasa karatunta kasan abba shine Wanda nakeda tabbacin xai bani goyon baya saboda inason matata ta tare a gida na kaga idan taje can babu wanda ya isa ya hanani
Aliyu yace hakane, yanxu yaushe abban xai dawo?
Next week insha Allah
To Allah ya dawo dashi lafiya
Sukace amin su dukansu

Afra tana xaune kusa da umma suna kallo sai afra tace umma inason kiyimun ixini inason naje xamfara kinga na dade banjeba
Umma tace
Lalala babu ruwana kitambayi mijinki idan ya barki sai kuje tare idan yanada lokaci
Afra tace aa ni banason tambayanshi
Saboda me inji umma
Afra tayi shiru batace komaiba
Umma ta dafata tace karkiji komai idan ya dawo kije kitambayeshi
Afra tace to umma

Daddare Affan ya dawo yanason yayi magana da afra Amma ya rasa yanda xaiyi dan ya shiga dakinta bai ganta ba saida ya shiga dakin umma sannan ya ganta sai yaji sanyi a ranshi umma tace
Yauwa affan dama afra tanason magana da kai
Affan ya kalli afra yace to muje dakinki ko
Afra tace aa nan nakeson muyi maganar dama inason xanje xamfara shine umma tace wai intambayeka
Affan yaga rainin hankalin afra yayi waya wato a gaban umma xata fada mashi buqatar ta nason xuwa gida kuma yace suje dakinta taqi xuwa umman tana kallo batace komai ba sannan tana yimashi magana babu ladabi takaici ya isheshi aiko yabata ansa
Babu inda xakije ko qofar gida ban yarda ki leqa ba
Umma tayi saurin dago fuskarta cikin mamaki affan saboda me baxaka bari taje xamfara ba?
Bai bata ansaba ya fita daga dakin fuu
Afra ta kalli umma kamar xatayi kuka umma tace kinsan halin affan kije kibashi haquri afra ta tashi taje tsakar gida bata ganshi ba sai taje dakinshi ta iskeshi xaune ya dafe kanshi ko tunanin me yake Oho
Afra tashiga dakin da sallama ya dago da kanshi ya xuba mata idanu afra ta tsaya daga bakin qofa tace
Umma tace inxo inbaka haquri
Affan yace afra inason magana dake
Inajinka
A matsayina na mijinki yakamata Mu fahimci juna afra ba kowace magana xaki rinqa fadawa umma ba tsakanin miji da mata akwai sirri kina JINA
Tayi shiru ta juya mashi baya yaci gaba da cewa Dan Allah afra kixo kibani haqqi na wlh a matse nake kinsan babu kyau fa abunda kike maka ikun rahama suna tsine wa duk wadda mijinta ya kirata xuwa shimfida taqi xuwa banason ki kasance daya daga cikinsu
Wai afra qiri qiri tace sai dai yayi wa axinshi yagama Amma baxataxo ba
Ran affan ya baci yace to bara nafada maki ba tsoronki nakeji ba da kikaga ina lallashinki wlh ko kinqi ko kinso next week xaki tare a gida na baxan iyaba idan ina biye maku xaku kaini ga halaka inje in fada xina
Da gudu afra tabar gurin taje dakin umma ta sameta nan inda tabarta umma tace yayarda da tafiyar?
Afra tace aa
Bata rufe baki ba saiga affan ya shigo dakin ko xama baiyi ba yace
Umma a gsky nagaji kiyi haquri da abunda xan fada maki next week nakeson abani matata gsky nayi haquri
Umma tasaki baki tana kallonshi tace haba affan karatunfa
Umma bata biyo hanyar arxiqin da xatayi karatu ba dan haka matata nake buqata wlh haqurina ya qare
Babu yanda umma batayi da affan ba akan ya janye maganar tarewa Amma yaqi yarda yace aure bai hana karatu tun tana lallashinshi harta dawo fada Amma inaaa affan yace matarshi yakeso Dan yana cutuwa
Ummma tarasa yanda xatayi da affan a qarshe tace yaje ya kwanta da safe xasuyi magana haka ya fita daga dakin yana kallon afra ko a jikinta bata damuba cikin ranshi yace wlh kitausayawa kanki Dan yanda bakiji tausayina ba haka nima baxanyi tausayinka nan yabar dakin yana tunani kala kala cikin ranshi Amma yasawa ranshi duk lallashin da umma xatayi akan ya qyale afra baxai yarda
Affan yana shiga dakinshi ya kira abba a waya bayan Sun gaisa affan yace abba dama akan maganar afra ne inason ta tare cikin satin nan
Abba yayi shiru yana naxarin maganar shi yasan affan gsky ya fada qara ya cire kunyavv ya fadi ra ayinshi akan yaje ya aikata xinà Dan yasan Dan nashi ba maxinaci bane
Abba Dan Allah kataimaka inji afra
Abba yace no wannan ba matsala bane afra ai matarka ce ko gobema xaka iya tafiya da ita
Affan yaji wani mugun dadi baisan lokacin dayace ngd abba Allah yabarmu tare ya kashe wayar

*ummu meenal*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*STORY AND WRITING BY MRS SADEEQ* (Ummumeenal )

*DEDICATED TO*
*Aysha galadima*

*short story*
*61-65*

*DUBUN GAISUWA GARE KU*

1- *jameela*
2- *Matar hamza*
3- *Barrister*
4- *ummu Khalil*
5- *zee*

*GAISUWA TA MUSSAMAN GA*

*Duniyar makaranta group*,
*Atk Hausa novels group, Ummu Hanan novels group, ya shaekh fans group*

Washe gari afra ta tashi da wuri tayi wanka ta shirya masu break fast takai dakin umma sai tasamu umma itama har ta tashi afra ta gaishe ta umma ta ansa cikin jin dadi tace afra badai har kin tashi ba ai naxaci xakiyi barcin gajiya
Afra tace aa umma babu wani barcin gajiya ai yanxu nasaba tashi da wuri kinsan a makaranta idan mun tashi tun asuba bama komawa barci
Umma tace hakane aini yau naji dadin tashinki da asuba saboda yau inason inje gidan biki Amma bawani dadewa xanyi ba
Afra ta bata fuska tace umma jiya fa nadawo kuma ace kitafi bamuyi firan makaranta ba
Umma tace tafiyan dole ne afra kuma nasan muna tare tunda hutunku yanada yawa karkiji komai
Afra tace umma kitafi dani nima inga gari kinsan makaranta bama fita kullum daga hostel sai class kamar yan gidan yari
Umma tace aa kitsaya kinsan halin affan baxai bari kifita ba
Afra ta kwabe fuska Dan ita harta manta da affan a matsayin mijinta
Afra tace unma xan tambayeshi yana ina? Umma tace yana dakinshi , afra ta juya da sauri taje dakin yaya affan tasameshi kwance da alama ciyon ya tashi . Tace ina kwana cikin qarfin hali yace lafiya
Afra tarasa ta ina xata fara tambayar fita biki kawai saitace yaya umma xata fita kuma inason xan rakata
Affan yace banyarda ki leqa ko qofar gida ba
Afra tace pls yaya inason infita
Wata harara ya balla mata sannan yace tafitar mashi daga daki kuma bai yarda taje ko ina ba
Afra ta fita daga dakin tana maganganu qasa qasa Dan Shi kanshi Affan baiji abunda tace ba
Tana xuwa daki umma tace ya akayi?
Afra tace ya hanani wai ko qofar gida karnaje
Umma tace aina fada maki affan Dan rigima ne ki qyaleshi ai ba wani dadewa xanyi ba kinga saiki Dora mana girki
Afra tace to umma
Chapter 9 · 0% Book details