← Book details Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 16

Sashe 3

Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Duk Abun nan da akeyi afra nacan kwance babu lafiya xaxxabi mai xafi ya rufeta ba a saniba saida umma shiru sannan tace affan naji afra shiru koxakaje kaduba ta umma tanayin haka Dan su Saba kuma su shirya a matsayinsu na ma auratan sati na sama
Affan kamar baxaijeba amma tunda umarni na mahaifiyarshi ba yanda xaiyi dole yaje
Aiko yana shiga dakin yaga kamar babu kowa gashi kuma cikin duhu saida ya kunna wuta sannan ya hangota can qudundune da bargo sai rawar sanyi take cikin sauri ya isa inda take ya yaye bargon yajishi da dumi yataba jikin afra kamar garwashi da sauri ya dago kanta xafi rau idanuwanta a rufe daukar jarirai ya mata da sauri ya kaita gurin umma
Umma tana ganinshi hankalinta ya tashi tafara kuka tana cewa lafiya affan meya sameta?

*yawan comment yawan typing*

*taku ummu Meenal*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*NA MRS SADEEQ (Ummu meenal)*

*DEDICATED TO AYSHA GALADIMA*

*Short story*

*page 21-25*

*WANNAN SHAFIN NAKUNE ❤ DANIDA MIJINA FANS*❤

Umma tana ganinshi hankalinta ya tasha tafara kuka lafiya affan meya sameta?
Shikanshi affan baesan meyake faruwa da itaba saboda haka bashida ansar da xai bata
Can yayi qarfin hali yace umma bara nakira baba yaxo da mota aje asibiti
Umma tace hi sauri kakirashi kada afra ta mutu
Kafin affan ya kira baba afra ta farfado tana fadin
Ruwa ruwa muryanta duk ta dushe da alama taci kuka harta qoshi
Umma cikin sauri ta dauko pure water tafasa tabata aiko tasha ruwan sosai ahankali ta koma kan cinyar umma ta kwanta ita kuma umma tasa affan ya dauko mata towel tana sawa cikin ruwa tana dafawa afra cikin ikon Allah xafin xaxxabin ya tafi
Shi kuma affan sai kiran wayar baba yakeyi Amma bai samuba daga qarshe ya tsaya yana kallon soyayya tsakanin umma da afra affan yayi murmushi cikin ranshi yace umma ko kinaso ko bakiso saikin rabu da ita nan da kwanakki kadan xataje makaranta
Ita kuma afra barci ta koma abunta sannan umma tace mashi Naga kamar jikinta da sauqi tunda tasamu barci kaje kasiyo mata magani idan ta tashi saita sha
Haka ya fita da niyyar siyo magani akan hanya ya hadu da wasu abokanansa suna ganishi suka fara
Ango ango
Cikin mamaki yace waya fada maku ni ango ne
Aliyu daya daga cikin abokanansa yace
Aini wlh baba ya burgeni da yayi maka haka ace kayita xama babu aure yanxu ko da yayi maka haka aiya kyauta
Affan cikin jin haushi yace idan banyi aure ba ina ruwanka kai bakayiba
Aliyu yayi dariya yace affan bakasan ni imar da take tartare da aure ba shiyasa amma yanxu ranar da aka kaimaka mata washe gari idan munxo xamuga canji
Affan yace Dan Allah kubarni da maganar auren nan ni wlh ba a son raina xanyi auren nan ba duk daga baba ne
Aliyu yace affan waiko bakada lafiya ne
Affan yayi murmushi yace kafi kowa Sanin lafiya ta Lau saboda idan sha awa na yatashi kai kake siyo mun magani
Aliyu yace ai yanxu matarka itace maganinka
Affan yace kai mexanyi da wannan yarinyar afra ce fa xan aura
Dariya sukayi gaba dayansu
Affan yace wannan yarinyar tayimun qarama ai sai inraba biyu
Dariya suka sake gaba dayansu

Ana saura sati daya biki mutanen xamfara sukaxo harda yayyen amarya da abokanan arxiqi aunty Asma u harda guxurinta na kayan mata sai dai umma ta hana abata a cewarta sai lokacin tarewa yayi
Afra kam tasha kuka harta godema Allah shima affan ya barwa Allah komai tunda dai ba fasa auren xa ayiba

Maganar kayan daki babu abunda aka siya sai lokacin tarewa yayi tunda yanxu karatu xata cigaba dashi bayan daurin aure
Ranar jumma a abokanan affan Sunxo har gidansu affan Sun iske gida ya cika da mutanen biki da qyar sukasamu suka shiga dakin ango Sun sameshi kwance ko tunanin me yake Oho
Aliyu ne ya dauko wata baqar leda ya bashi
Affan yace menene wannan?
Kayan daxakasa kaje daurin aure ne
Affan ya hade rai yace Kaga malam ni anfada maka xan tsaya sa wani sababbin kaya ne ni qila daurin auren baxan samu xuwa ba
Dariya sukayi abokanansa sannan shima affan yace
Ana daura aure xata kama gabanta Dan makaranta xataje ni kuma xanje bautar qasa

Ranar assabar misalin qarfe goma sha biyu dubban mutane suka shaida daurin auren affan da afra akan sadaki dubu hamsin inda ango yasha manyan kaya babu laifi ya dan saki fuska Amma a cikin ranshi ko kadan baya murna da wannan auren
Ita kuma afra tanajin labarin an daura aurenta da affan ta fara kuka sosai tana fadin nabani an daura mun aure da mugun mutum yau nashiga uku wlh baxan xauna dashiba tunsu aunty fatima suna bata haquri har Sun gaji Sun fara yimata fada
Aunty Asma'u cewa tayi
Afra bawai affan baya sonki bane halinki ne bayaso idan kin gyara halinki sai kiga kun xauna lafiya
Afra taqara fashewa da kuka tace ni banason Shi
Duk abunda takeyi affan yanajinta saboda masu karatu kunsan gidansu daya
Ran affan ya baci da kalamanta bawai Dan tace bata sonshi bane jin haushi a'a wai shi take kira da mugu lallai xataga mugunta
A hankali ya qaraso inda take yace
Ke nikike kira da mugu ?
Tayi shiru saita turo Dan madaidaicin bakinta
Bata saniba ashe su aunty fatima sun bar dakin lokacin daya shigo
Aiko gabanta ya fadi tayi saurin tashi da niyyar fita ya riqo hannunta yace
Ina xakije
Dakin umma
Affan yace ni kike kira da mugu ko?
Afra tayi shiru idanunta suka fara cicciko da hawaye
Ba tambayar ki nakeyiba? Waye mugu?
Nanma tayi shiru
Affan yace to tunda kince mun mugu xakiga mugunta baxakici gabada karatunki ba kuma sati na sama tarewa
Afra ta xaro idanuwanta ta dafe qirji tace
Dan Allah yaya affan kayi haquri wlh baxan sakeba Dan Allah
Murmushi yayi Dan dama wasa yakeyi mata
Bani kike cewa mugu ba
Natuba baxan qara ba Dan Allah tasaki sabon kuka afra kenan kuka baya mata wahala

*ummu meenal
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*NA MRS SADEEQ ( ummu Meenal)*

*DEDICATED TO AYSHA GALADIMA*

*short story*

*page 26-30*

*MASOYA NA A DUK INDA KUKE INA GODIYA SOSAI DA MASU SON NOVEL DINA DA MASU YIMUN MAGANA A PRIVET DUK INA GODIYA*

*TUKWICI GAREKI AYSHA*

Haka akayi taron biki lafiya dukda dai ba wani taron akayiba saboda cewa akayi sai a tarewa xa ayi taro
Amarya afra ta rame dama gata ba qiba gareta ita yanxu tunda an daura aure burinta ta cigaba da xuwa makaranta kada affan ya hanata dan tasan ba qaramin aikinshi bane
A bangaren affan kuwa yanacan dashida abokanansa sai xolayarshi sukeyi tun baya tanka masu harya fara maida masu
Affan yace ni cikin satin nan xan kaita makaranta a huta danni ko ganinta banasonyi
Bello daya daga cikin abokin affan yace haba malam ai dai yakamata kabari ka angwance a daren yau koba hakaba ya tambayi sauran abokanansu
Aliyu yace a a qara ta tafi tun yanxu saboda idan ya tare yaji yanda aure yake ai saiya tauye ma yarinya haqqinta yace baxata cigaba da karatunba
Affan duk firan da sukeyi yanajinsu haushi ya hana yayi magana

Yaune affan yaxo da transfer na makarantar afra yana fadawa umma angama komai ko yauma xata iya xuwa G G S S JIBIYA
Umma tace bangane ko yau xata iya xuwa ba ina kayan provision?
Yace umma bansan me take buqata ba kitambayeta
Umma tace ni xan tambayeta kenan daukarta xakayi kuje ta xabi abunda takeso
Affan yace umma taje dai ta siyo tunda ba mota gareni ba
Dan bakada mota shine baxakaje ku hau napep ba
Ran affan ba haka yasoba Amma babu yanda xaiyi dole ya amsa mata
Umma to tashirya anjima xamuje Mu siyo umma tace to Allah ya kaimu
Chapter 3 · 0% Book details