← Book details Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*A KADUNA*
Service din affan ya fito Amma abun mamaki sai aka turashi G G S S JIBIYA 😨 wato makarantar su afra
Umma kam murna tayi sosai a cewarta xai Kula mata da afra*
Shikam affan hakan ba qaramin jin haushi yayiba saboda yana murna tayi nesa dashi gashi kuma yanxu Sun dawo kusa
Lokacin dayake fadawa su aliyu an turashi service a jibiya ba qaramin murna sukayi ba har xolayarshi sukeyi wai shima yanaso yana nuna bayaso
Aliyu yace nasanma har gida anbaka a makarantar
Affan yace to Dan anbani gida a makarantar sai akayi me?
Saika dauko matarka daga hostel kamaidata dakinka tunda a skull dinne Kaga da safe kushirya kushigo aria skull 🤣
Affan yace wlh kunfara kaini ga bango banason wannan game din babu abunda xanyi da wannan yarinyar Allah ya sauwaqe nafi qarfinta ya fada cikin fada😡
Aliyu yace idan xakaje sai kaje da maganinka kada jarabarka ta tashi ka afkawa yar mutane 😜
Affan Dan haushi ko magana yakasayi haka suka rabu suna xolayarshi
Ana gobe xaije service suna xaune da umma da affan sai nasiha take mashi
Dan Allah affan kariqe qanwarka amana karka biyewa halinta Kaga matarka ce kuma qanwarka Dan Allah ka Kula kuma ka Kula da karatun ta Dan Allah karka takuramata kasan dai yarinya ce
Affan yace ai umma dakinsu daban dakina daban sai skull eria ne kawai xamu hadu da ita
Umma ta dauko dambun nama tace gashi kabata kace ina gaisheta
Yace to xataji
Ranar da xai tafi saiga aliyu da mota yace shi xai kaishi jibiya
Affan yace xakaje dai gulma kawai
Ya tuntsure da dariya yace aa wlh Kaga bodar Niger nakeson xuwa to Naga duk hanya dayane shine nace bara kawai Mu wuce tare
Affan yace kai kasani kayi gulmar ka kagama
Cikin ikon allah sun sauka lafiya Dan aliyu har dakin affan ya rakashi sannan yayi mashi fatan alkairi ya wuce gaba
Shi kuma affan ya tsaya yana Dan gyare gyaren gurin Dan yayi qura sannan yaje ya kwanta saboda gobe Monday xaije fara xuwa karantarwa kuma ya gabatar da kanshi wajen dalibai. ......

*kubiyoni*
*ummu meenal ce*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*STORY AND WRITING BY*
*MRS SADEEQ (ummu Meenal)*

*DEDICATED TO*
*AYSH GALADIMA*

*short story*

*36-40*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana baxan iya qirga sunayenku ba saboda kuna da yawa da masu bina pc suna nuna qaunar nevel din DANI DA MIJINA duk ina godiya muna tare🤝🏻*

Da asuba afra tana barci can cikin barcin taji ana tashinta kamar a mafarki ta farka sai taga duk yan hostel sun tashi itama tayi saurin tashi ta dora alwala danyin sallah asuba

A bangaren affan kuwa ya shirya cikin kayan nysc kayan ba qaramin kyau suka yimashi ba sai qwarjininshi ya qara fitowa saida ya gama shirinshi tsaf sannan ya fito xuwa area skull

Ita kuma afra bayan Sun gama share sharen su ta koma guri guda ta xauna saboda yunwar data dameta har wani jiri take gani batasan lokacin da tafaďa tunanin gida ba lokacin da tana gida umma har lallashinta take taci abinci Amma saita gadama takeci Amma yanxu gashi tana son abinci Amma babu sai dinning kuma sai 10am ake badawa kuma babu dadi uwa uba baxai isheta ba
Batasan lokacin da tafara hawaye ba sai kuma ta tuna lokacin da sukaje shopping da yaya affan yace ta xabi abunda takeso tayi banxa dashi yau gashi tana nema bata samu ba tana cikin tunanin ne sai taga wata mai irin kayan ta uniform taxo ta gabanta xata wuce afra tace
Sister Dan Allah xan tambayeki
Dalibar ta juyo tace inajinki sister
Afra tace Dan Allah inane shop ni baquwa ce bansan ko ina ba sai class da hostel yan kwanar mu kuma sun fita bansan inda sukaje ba
Dalibar tace eyyaa sannunki da xuwa ni sunana xainab gide kefa ?
AFRA
Xainab tace xomuje dama nima can xanje suna tafiya suna Dan taba fira har suka isa shop din
Afra ta dauko kudin da affan yabata dubu biyar ta siya madara da Milo sai bournvita da cabin ta siya suga daganan kudi ya qare baifi yan canji suka rage mata ba

*ASSEMBLY*
Principal tsaye a gaban assembly tana jawabi kamar yanda ta Saba dalibai suna sauraronta kamar a mafarki afra ta hango affan cikin kayan nysc saidata qara bude idanunta ta gani kodai mafarki takeyi aiko ba mafarki bane a xahiri ne sai taji principal tana gabatar da affan a matsayin malamin makaranta xai koyar da maths kuma a j s s 2 😳 ajinsu afra kenan
Principal ta cigaba da jawabi akan uncle affan tace dafatar dalibai xasu bashi hadin kai kuma suyi mashi ladabi da biyayya
Afra har cikin ranta taji dadi saboda taga na gida kunsan yan bourding da son ganin na gida😜
Cikin daliban j s s 3 taji wasu suna cewa wallahi kyakkyawa dashi ni ya burgeni afra sai tayi murmushi tace bakusan Waye yaya affan ba
Bayan an tashi break fast afra taje dinning har tabi kayi ta tuna da batada cup din karbar koko kuma gashi tanajin yunwa dama nana balki ce ta ara mata dayan cup dinta kuma an sace gashi yanxu tanason karbar koko babu cup
Kawai wata xuciyar tace kije wajen yaya affan ko xaki samu aiko batayi musu ba ta koma office dinshi da gudu knocking batayi ba tashiga office din saboda kada koko ya qare tana haki ta shiga
Shi kuma yana xaune lokacin ba a dade da kawo mashi waina ba sai tururi takeyi da xafinta taji nama da qashi xai faraci kenan sai ganin afra yayi tashiga a guje
Kallonta ya tsaya yanayi ita kuma ta sunkuyar da kanta qasa saida suka danyi mintuna haka sannan dayaga batada niyyar yin magana yace
Ke lafiya kika shigomun office babu sallama fuskar shi a daure
Afra cikin in in na tace
Am um Dan Allah naxo ka aromun cup xan karbi kunu kada ya qare
Saida dariya taxo mashi Amma gudun raini saiya qara daure fuska yace
Anfada maki ni sa ankine da xanxo da cup?
Ubanwa yace kishigomun babu sallama
Afra gabanta yana faduwa tace wlh yaya yunwa nakeji Dan Allah ka taimaka mun tafada tana kallon wainar gabanshi
Dan murmushi yayi ya fara takowa xuwa gurinta ita kuma tana ja da baya harta kai jikin bango dama shine wurin qofa
Cire mata hijabin yayi ya riqo gashinta da qarfi aiko ta saki ihu yayi saurin rufe mata baki da dayan hannunshi yace
Xaki qara shigomun office?
Girgixa kanta tayi alamar a a saboda ko magana baxata iya ba
Ke yarinyar nan Dan kin rainamun da hankali shine kikaxo wai in ara maki cup ko ?
Me kika maidani?
Hawaye kawai sukebin idanuwanta kukan ma yaqi fita
Saida yaga dama sannan ya saketa sannan yace duk Wanda ta fadawa xata gane batada wayo sannan yace ta fita tabar mashi office
Cikin kuka ta juya xata fita kuma saiyaji masifan tausayinta ya cika xuciyar shi koba komai matarshi ce dukda baya sonta haqqinshi ne ciyar da ita
Harta kai bakin qofa yace
Afra xo nan
Batajeba saita tsaya a bakin qofa
Yace umma tabani saqo inbaki gobe kixo ki karba
Batace komaiba saita bishi da manyan idanunta
Sannan yace bisimillah xokici waina kinci darajar aure
Afra cikin tsiwa tace baxanci ba (ni ummu Meenal nace abakin qofa xakiyi tsiwar kishiga ciki mana😀)
Affan yace xaki iya tafiya
Bata jira ya qarasa maganar ba ta rufe qofar da qarfi sannan taje dinning
Allah ya taimaketa ta hadu da xainab gide wadda sukaje shop tare ta ara mata cup tayi saurin shiga layi
Ankusa kawowa kanta Sai taga mutanen gabanta kowa ya kamata gabanshi ita kuma tayi tsaye saida wata tace mata sister koko ya qare
Kuka tafarayi sosai kitchen master yaxo yace lafiya?
Afra tace yunwa takeji
Kitchen master yace meyasa bakixo dinning da wuri ba
Afra tace banida cup
Kitchen master yace daga yanxu kinajin an buga dinning kiyi gaggawar xuwa inba hakaba baxaki samuba sannan ki nemi cup afra tace to

Afra suna gaban fanfo yau kwanasu antashi da matsalar ruwa basuda konasha kuma sun dade a fanfo Amma basu samuba dayake layi akeyi kuma har yanxu layin bai kai garesu ba kuma ga qishirwa tanaji haka taje ta kwanta da qishirwa Amma taci alwashin indai taje gida baxata dawo ba
Chapter 5 · 0% Book details