← Book details Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bayan arba in affan yacewa afra yakamata taje xamfara dama yayi mata alqawarin saita haihu Dan haka da kanshi ya kaita afra murna take xataje gida dan lokacin da affan yayi parking din mota da gudu ta shiga gidan dama ansan da xuwanta gida ya ruďe da murna sannan aka kaisu dakin Hutu aka kai musu abinci a can
Saida suka kammala cin abinci sannan affan yace shi xai tafi jibi xaixo ya dauketa
Afra tace haba hubby na yaushe rabon da inxo kuma kace kwana biyu xanyi ni wata daya xanyi
Affan yace xakisa yanxu injuya dake idan kikace kiyi wata
Da qyar affan ya bari afra tayi sati daya
Yan uwa da dadi afra ta shiga cikin Dangi inda ta dade bataje ba kowa sai murna yakeyi kuma tunda ta tafi ake bata kayan mata anyi mata kaxar amare tasha tsimi da gumba harta gaji
Bayan sati daya saiga affan da sassafe yaxo daukar afra sai kace Wanda ya kwana a hanya dama ta shirya kayanta Dana Aryan basu bata lokaci ba suka juya sai kaduna
A hanya affan yake cewa afra shifa ya gaji da xamanta gidan umma gidanshi xai wuce da ita
Afra ta marairaice Dan tasan halin affan ba qaramin aikinshi bane ya wuce da ita gidanshi tace Dan Allah hubby na kayi haquri kar ace munyi rashin kunya
Affan yace gsky na gaji da kwana ni kadai
Afra kamar xatayi kuka tace ni dai wlh kunya nakeji ina gidan umma ina wankan jego kuma kace xaka kaini gidanka
Affan yace ai kingama jego tunda kinyi arba in
Da qyar afra ta lallashi affan akan ya haqura ya kaita gidan umma tunda ta kusa komawa ita kanta tayi kewar mijinta sannan ya haqura ya kaita gidan umma
Bayan Sun dawo da kwana biyu umma kamar tasani tace affan ya dauki matarshi ya tafi da ita gida dama affan jira yakeyi dan haka bai bata lokaci ba ya dauketa da kayansu ya Maida gidanshi
A daren saida affan ya kusa sumewa Dan dadi yanata sa mata albarka washe gari ya biya masu aikin hajji afra tayi murna sosai tace nikam nayi sa ar miji Allah yabarmu tare Allah ya qara daukaka shima yana murmushin jin dadi yace amin sannan suka qara fadawa duniyar ma aurata

*BAYAN SHEKARA BIYAR*
Afra ta xama babbar mace Dan yanxu tana karatu a *KASU*
yanxu yaranta uku Aryan sai amina taci sunan mahaifiyar afra suna kiranta *MEENAL* ta uku taci sunan mahaifiyar affan suna kiranta *HANAN* yanxu duniya tayi masu dadi basuda damuwa suna xaune lafiya kowa bayason bacin ran kowa...........

*ALHAMDULILLAH*
*Anan na kawo qarshen wannan littafi nawa ina roqon Allah kura kuren dayake cikinshi Allah ya yafe mun*

*Sai kun sake jina a sabon littafi na mai suna *BANSAN ITA BACE*

*Taku ummu Meenal*🖊
Chapter 16 · 0% Book details