← Book details Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Dani Da Mijina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yawan comment yawan typing

Matar sadiq ce
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA*❤❤❤

❤❤❤

*NA*
*MRS SADEEQ*(Ummun meenal)

*DEDICATE TO AYSHA GALADIMA*

*Short story*

*page 11-15*

Affan nagani A daki yakasa xama ya kasa kwanciya duniya tayi mashi duhu ya rasa inda xaisa kanshi duk jarumtarshi ya nemeta ya rasa ya Kifa kanshi akan gado kuka yake wiwi kamar mace lallai antabo maxa
Yaga kukan baxai mashiba yatashi yaje dakin umma
Yana xuwa yaga halin da take ci kamar hankalinta yafi nashi tashi
Xuwa yayi kusa da ita yana kuka kamar qaramin yaro yace
Dan Allah umma kitaimakeni kitaimki rayuwa ta karki bari ayi auren nan Dan Allah
Umma ta dago jajayen idanunta da alama itama kukan tayi tace affan nafika rashin son ayi auren nan
Inajin tsoron kaje katakurawa afra banason bacin ran afra gashi kai kuma bakason afra kuma kasan babanku magana daya ne dashi
Affan yayi shiru yana naxarin maganganun umma taya umma xatace banason qanwata jinina da ubana da ubanta uwa daya uba daya lallai umma kinyi nisa da son sangarta afra...
Bai gama tunanishi ba ta katseshi da cewa
Affan danasan hanyar daxaisa afasa auren nan wlh da saina jajirce baxan yarda a aura mata mugun mutum ba
Affan yace umma kije ki lallashi baba koxai sassauta akan maganar auren ni a ganina yakamata abarta tayi karatun ta
Umma ta balla masa harara tayi gaba abunta

Umma tayi sallama dakin alhaji Amma me sai taji yana waya da baban xamfara akan maganar auren affan da afra
Gaban umma yayi mummunan faduwa shi kenan tafaru ta qare aure ya tabbata
Saida yagama wayar sannan ya kalle ta yaga ranta a bace yace
Dama so nake inkiraki akan maganar auren yaran nan yanxu muka gama waya da umar din yace babu matsala duk abunda nayi shima dai dai ne
Umma tarasa bakin magana domin shi Babansu yafi qarfin gidanshi
Bakice komai ba inji alhaji
Umma tace to Allah yasa alheri

Duk abunda ake afra bata sani ba saboda haka ita hankalinta a kwance yake

Affan yaji xaman gidan ya dameshi saboda haka yace bara yaje waje koxaiji sanyi a ranshi yasa key yana rufe dakinshi
Saiga afra ta shigo gidan da yara Sun biyota suna rigima tana ganin affan ta gudu wajen umma su kuma yaran sukayi tsaye suna jiran fitowarta
Affan yaje gurin yaran yace
Lafiya
Daya daga cikin yaran tafara magana
Wai muna bakin rijiya muna Jan ruwa saiga afra taxo tana ta dauki botiki na ta jefa rijiya yarinyar ta qarasa maganar da kuka😭
Daga can cikin daki inda afra ta boye tace
Wlh yaya qarya takeyi ita ta jefa botikinta cikin rijiya 😀
Ran affan ya qara baci dayaji afra tace ba ita ta jefa botiki cikin rijiya ba
Yayi qwafa irin xakici ubankin nan
Sannan yacewa yaran suyi haquri
Aiko yarinya ta kafe ita baxata haqura ba saboda idan taje gida xa a daketa
Qarshe dai saida affan yaje gidansu yarinyar yabada haquri sannan yace xai siyo sabon botiki

Bayan affan ya dawo gida kai tsaye dakin umma ya wuce saboda yasan afra tana can
Afra tana ganisnshi tafara kuka tana cewa
Dan Allah yaya affan kayi haquri baxan sakeba Amma duk da haka saida ya xane ta da qyar umma ta qwace afra ga affan ranan tasha wahala gun affan

*washe gari*
Da safe umma tagama break fast ita kuma afra tana xaune a falo tana kallon umma ta Maida hankalin ta ga afra tace afra ki nutsu ki saurareni akwai maganar danakeso muyi dake
Afra tace to umma
Ummm tace afra kiyi haquri da maganar da xan fada maki
Afra ta dago manyan idanunta ta xubasu akan na umma
Afra inason kisani ina sonki ina qaunarki Amma hakan baxai hana injaye hukunci da babanku yayiba Amma nafi kowa baqin cikin hakan
Afra tace umma banganeba me kike nufi❔
Umma tace babanku xaiyi maki aure😳
Wata irin firgita afra tayi ta Bala in tsorata da maganar umma
Nan take tafara kuka tana magiya
Umma Dan Allah kibashi haquri laifin me nayi mashi da xai aurar dani tun ina qarama nashiga uku
Umma tace bake kadai xai aurar ba harda yayanki affan
Afra tace aishi yaya ya girma ni kuma qarama dani ace xa ayimun aure kawai saita rushe da kuka
Umma ta rungume afra tace kiyi haquri insha Allah xaku xauna lafiya kuma ai baki tambayi Waye xaki aura ba
Afra cikin kuka tace banason jin Wanda xan aura ko Waye anason shi kawai kar ayi auren nan
Ummma ta dago fuskan afra tace
Yayanki affan shi xaki aura
Numfashin yana neman daukewa da qyar ta saisaita numfashin ta
Umma Waye xan aura yaya affan fa kikace umma so kike ya kashe ni wlh mugu ne ya tsaneni kuma nima banason shi Dan Allah kar ayi auren nan
Umma tace haquri kawai xakiyi domin maganar aure har taje xamfara kuma kinsan babanku magana daya ne baxai janye maganar auren nan ki rufama kanki asiri idan ba so kike ranki ya baci ba fatana kiyiwa mijinki biyayya domin kinsan halin yayanki bayason rashin ji idan kika nutsu sai kiga kun xauna lafiya
Afra tace umma wlh mugu ne baya sona dukana xaiyi
Umma tayi murmushi sannan ta jawo afra jikinta tana lallashinta da dadin baki

*taku Mrs sadeeq*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*NA*
*MRS SADEEQ*(Ummun meenal)

*DEDICATED TO*

*AYSHA GALADIMA*

*Short story*

*page 16-20*

*NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GA DUK WADANDA SUKAYI KARATU A G G S S JIBIYA JIHAR KATSINA*

Dan Allah baba kayi haquri ka janye maganar auren nan wlh banason Shi kuma wlh shima baya sona Dan Allah baba kabarni inci gaba da karatuna
Baba yayi shiru yana sauraron afra tabashi tausayi Amma kuma hakan baxai hana ya janye maganar auren nan ba
Baba ya tambayi afra yace ya kike so ayi ?
Afra tace karatu nakeso tafada cikin murna a xatonta xai janye maganar auren
Baba yace xakici gaba da karatunki afra bawai xa a hanakiba Amma sai bayan auren xakici gaba
Afra ta qara marairaicewa tace baba Dan Allah baba kajanye maganar auren nan
Ran baba ya baci yace maganar auren nan dole ne saboda haka kitashi kibani guri
Cikin matsanancin kuka afra ta tashi taje dakin yaya affan tayi sa a kuwa ta iskoshi tana xuwa ta xube gabanshi tana kuka tana roqonshi
Dan Allah yaya affan kaje kabawa baba haquri wallahi komai nakeyi nadaina wlh idan akayi auren nan xan mutu Dan Allah, ,,
Ya katseta da cewa
Ni amfada maki sonki nakeyi ne to kisani nima banasonki bana qaunarki mexanyi dake yar qwailarki ni nafi qarfinki kuma idan har akayi auren saina gyara maki xama Dan sai kinyi Dana Sanin xuwa duniya kuma kitashi kifitar mun daga daki bana son ganinki
Hankalin afra inyayi dubu ya tashi a duniya babu Wanda take tsoro kamar yaya affan idan har yana gida bata wani sakewa to inaga sunyi aure tashin hankali ihu ta saki a dakin tana kuka Ran affan ya qara baci ya hasala ya isa inda take ya damqi lallausan gashinta yayi mashi mugun riqo itako sai ihu takeyi kamar tasaki fitsari saida yaga dama ya saketa da kanshi aiko yana sakinta taje dakinta a guje tafada kan gado ta bude wani sabon kuka

Afra tana fita shima affan yaji ranshi yayi mugun baci yarasa meyake damunshi qarshe yaje toilet ya dora alwala ya tada sallah

A bangaren shirye shiyen biki yakeyi Dan har mutanen xamfara babu Wanda bai saniba baba da kanshi ya bada sadaki dubu hamsin xa a daura aure assabar ta sama yakama saura kwana goma kenan Amma a bangaren amaren kuwa kowa yanajin haushin kowa

Umma tayi fushin harta gaji ta sauko itama ta fara shirin biki amm taje ta samu baba ta roqeshi a daura aure Amma tarewa saita gama karatun ta baba yace bashi xata tambaya ba affan xata tambaya saboda shiyake da iko da matarsa ranta ya baci Amma bata nunaba tace babu komai xan roqeshi
Bayan tafito dakin baba dakinta ta koma sannan ta aika sagir qanin affan din tace yaje yakira mata affan
Bayan yan mintuna saiga affan ya durqusa gabanta yace
Umma gani
Umma tace dama ba wani abu bane akan maganar auren nan ne tunda alhaji ya nace sai anyi auren nan ba yanda xanyi Amma afra baxata tareba sai tagama karatun ta
Affan yayi qasa da kai tabbas bayason afra amma yanda umma take nuna fifiko tsakanin affan afra abun yayi yawa ai kamata yayi ta tambayeshi idan ya yarda taci gabada makaranta ba waita yanke hukunci ba saboda idan anyi auren shiyake da iko da ita
Umma ta katse mashi tunani da cewa
Naji kayi shiru ?
Umma Kibari xan tambayi baba duk yanda mukayi dashi xan fada maki
Umma tace bance katambayeshi ba ansa nakeso kabani yanxu kaga afra yarinya ce duka 14years all Dan haka saita gama makaranta
Affan yayi murmushi cikin ranshi yace nagane abunda kike nufi umma a fili kuwa cewa yayi babu komai da kaina xan nema mata makaranta Dan xan canxa mata makaranta xuwa bourding skul
Umma taso tayi mashi gardama akan cewa yabarta inda take Amma sanin halin affan xai iya cewa baxata cigaba da makarantar a gaba daya idan tayi mashi gardama shiyasa tace to yanxu wace makarantar xaka Maida ita ?
Affan yayi kamar mai naxari yace ina son xan kaita G G S S JIBIYA saboda makarantar tanada kyau sosai
Umma tace haba affan jibiya ai tayi nisa
Affan yace umma can nakeso kuma can xataje
Umma tace to allah ya bada sa a
Yace amin sannan taci gaba da yimashi yan nasiha da shawarwari
Chapter 2 · 0% Book details