Sashe 9
Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace kowa ya kwana lafiya shi yaso" murmushi yai yana rokon Allah daya shirya masa mahaifiyar tasa. We will meet again. you next time Typing +234 905 527 3614. Yusrah Musa Abubakar Gimba. Page 19 to 20. Tun asuba Saude da Abu suke gyaran agwagin nan kamar wanda suke gyaran saniya gari na wayewa Abu takai markade aka dafe su"'. Wani abin mamaki a fanteka aka zuba guda uku wai gidan me gari za'a kai haka suke yi biyun sune na budurwar . Dariya sosai Afeeyah tai ita bataga abin farin ciki dan an baka wadannan agwagin ba tunda babu riba". Kai da kafa harshi Saude ta dafe duk kayuwan ta debo a wata langar kwano me tsatsa tana kaiwa Salamatu ". Kai Salamatu ta girgiza tana cewa" a'a alhamdulillah na gode". " iheee bakin ciki kike ne Salamatu dan 'yarki bata samo ba kome"?. "Eh shi nake yi". "Aiko zaki mutu da bakin ciki domin Abu sai zaman gidan me gari su o'o kuwa bamusan inda za'a hara ba ko kuturu ko makaho waya sani". Ta fada tana dariyar mugunta tare da daukar langar kayukan ta koma dakin ta". Daddy na zaune tare da Muntari daren da ana gobe zasu koma Abuja muntari ke cewa'. "Nikam yaya inaso yara na suyi ilmi sosai amma sa idon 'kauyen nan ya hanani sakat gashi ita Zainaba har ana zancen aurenta". "Daddy yace toba tana da 'kanwa ba 'yar gidan Salamatu ko har ita za'ai auren"?. "A'a iya zainabun ce ita har yanzu bata samu tsayayye ba tukuna dai". "Ok mezai hana mu tafi da ita tunda kana so tai ilmi sai a sai mata makaranta". Muntari yace da naji dadi yaya wallahi inason dana yai karatu". "Shikenan babu damuwa ka sanar da mahaifiyarta gobe da wuri kafin mu wuce ya kamata ta sani". "Eh zan fada mata duk da nayi shedar Salamatu bata da matsala". Washe gari jin harda Fati zasu tafi yasa saude tace tab kace su Aisha zasu debi masifa yarinyar da kauye ma idonta a tsaye yake balle tana birni . Nasiha sosai Salamatu taiwa Fati duk da a ranta bata son rabuwa da yarta ta kamar yadda itama Fatin bata kaunar binsu. Da kukan ta tashiga mota suka tafi yayin da Afeeyah ke mata dariya tana cewa ayya keda dawowa sainan da shekara uku Allah sarki". Da fati iya hawaye take jin abinda Afeeyah ke cewa yasa ta soma shashsheka". Al'ameen dake driving Sadiq na kusa dashi ya joya yana cewa mene haka zan sa'ba miki ba jiya kika gama cewa she's our sister ba". Murmushi Afeeyah tai tana kallon Fati tace sorry sis ita kam Fati babu bakin magana har sukaje gida". Cikin fushi na sun taho da Fati yasa mami ta fice fuuu daga motar daddy ko kasheta baiyi ta shige cikin gida". Afeeyah kam bedroom dinta takai Fati tana cewa sannu da zuwa gidan mu ki kwantar da hankalin ki nan tamkar gidan ku ne ki dauke ni matsayin 'kawarki". Murmushin dole Fati tai tana cewa nagode". "No baki da matsala Afeeyah ta fada tana shiga toilet tayo wanka da alwala sannan ta fito tana cewa fati kema kije kiyi wanka". Shiga toilet Fati tana mamakin kyausa kamar ka kwanta a kasan tayis din sai 'kyalli yake kamar mirror. Ganin bata ga ruwa ba ta leko tana cewa wai ina ruwan kuma banga baho ba sai wani kwale-kwale ko a ciki ake wanka"?. Dariya ce ta kama Afeeyah saida tagama shiryawa sannan taje ta kunna mata ruwan ta fito. Sanin datai cewa bada son ran mami Fati ta biyu su ba yasa tasa kawai aka kawo musu abinci part dinta". Kwanan Fati biyu daddy ya sai mata school ta fara zuwa itama driven ta daban . Korar yan aikin gidan mami tai mutum uku tabar biyu cewa meye amfanin fatin idan ba bauta ba". Tasa ta a cikin 'yan aikin batare da sanin daddy ba hakan datai ya 'kona ran Afeeyah dan haka itama take shiga kitchen din tana koyawa fati wasu abubuwa. Ina Fatima ban ganta ba jiya da yau lafiya kuwa"?. Kau dakai mami tai tana cewa tana kitchen ita da su nana". Cikin mamaki daddy yace me take yi a kitchen din"?. Rasa abinda zatace mami tai ta kama kame-kame daidai Afeeyah sun fito ita da Fatin jikin su duk a 'bace. Daddy da ransa ya soma baci ganin yadda suka fita hayyacin su ya kalli mami cikin fushi yace". "Aisha yanzu sune kika mayar kitcinonin ki yara nane fa amma zaki wani tura su kitchen sun zama kuku ne". Ganin daa Afeeyah tai daddy ya damu da yawa yasa cikin son kare mamin tace. "Lah daddy ba ita ta tura muba kasan ban iya girki ba kuma gashi kullum lokaci yana ja gidan wasu zanje shine nace bari na koya abin kunya ne ace kamar ni ban iya komai ba". Sauke ajiyar zuciya mami tai a boye jin Afeeyan ta ceceta mikewa daddy yai yana cewa shikenan amma ku rika aikin baya baya sannan ku rika lura da wuka kada ku yanke. "To daddy mun gode zamu kiyaye" cewar Afeeyah. Barin gurin yai mami dake shirin tashi ita ma tace tunda kin biyewa wannan yar kauye wahala yanzu kika fara shanta ". Kai Afeeyah ta girgiza ba tare datai magana ba shigowar Zainab kenan ko zama batai ba ta kalli Fati a 'kyamace tana cewa". "Ke village girl dauko min abin sha a fridge sannan ki wuce kitchen ki zubo min abinci me zafi". Wani kallon baki da hankali Afeeyah ta mata tana cewa itace zatai miki bauta aiba yar aiki bace idan bazaki nemi nana ta kawo miki ba ki barshi". Ke na sako dake ne gada wacce nake yinan". "Kin sako dani tunda kika ambaci yar uwata bazatai ba kinji na fada miki". Tsawa mami ta saki tana hararar Fati tace ke dalla wuce ki mata abinda take so sa'ar kice ita". "Maamii" Afeeyah ta fada ranta a bace. Ke kuma zaki ci ubanki Afeeyah idan baki min shiru ba". Barin falon Afeeyah tai yayin Fati ta wuce kitchen ta zubo mata abincin tare da dauko juice ta kawo mata . Banza jaka yar kauye akuya" zainab ta fada tana dauko spoon. Juyowa Fati tai tace duk sunan kine gaskiya kin more jaka akuya toga dusa nan da ruwan tsami na kawo miki saiki fama". "Keee tsaya dan kan uwarki". A haba dai na tsaya saboda ke baki da wannan matsayin babyn daud'a jeki wanka da brush kafin na saurare ki, domin wari kike" Sai kuma ta fashe da dariya tana kallon Zainab tace ki fama ina zuwa idan dusar bata isa ba akwai wata a kitchen kice meeeyyy zan zo na karo miki dan wallahi ganin ki ya tuna min da tinkiya ta Tana fadin haka ta bude kofa ta shige tana cewa sorry idan kinji haushi na kinsan mu villagers bamu iya magana ba". Cizon yatsa Zainab tai cikin takaicin tsayawar datai ta zuba ido Fati ta fada mata son ranta amma bari ta shiga part din saita fasa mata baki. Al'ameen dake tsaye a kofar palor ya jinjina kai yana karasowa zai wuce ganin sa da uniform din army yasa Zainab ta fahimci tafiya zaiyi cikin sauri tace". "Yaya Al'ameen". Cikin mamaki ya juyo jin yadda ta kira sunan a tausashe yasan akwai abinda zata ce". Mikewa tai tana zuwa har gaban shi ta ciro wani zobe daga cikin karamin abu me kyau tana mika masa". Batare daya karba ba yace na mene"?. Murmushi tai cikin karya murya tace kaima ka sani kawai ka fuske ne Allah Al'ameen ina cikin matsala na rasa yadda zanyi da rayuwa dole na fada maka cewa na kamu da ciwon sonka Wani irin kallo ya mata zai wuce bai tanka ba ta sake shan gaban sa idon ta da hawaye cikin magiya tace". "Na roke ka Al'ameen ka soni ko kadan ne kaji tausayi na kada zuciya ta tabuga na mutu". "Da kin huta da matsalolin duniya ke dan kin raina min hankali nine zan soki are you out of your sense A'a ina cikin hankali na koda na zauce to lallai sonka ne ina kaunar ka kuma da aure". "Ashe zaki mutu baki aure ba babu abinda zanyi da mace irin ki kada ki batawa kanki lokaci zuciya ta tamace daya ce kuma bata raye dan haka na kulleta". "Dan Allah Al'ameen ka bude ta gani nazo zan maye maka gurbin wacce ka rasa". "Ta ya kenan". Zoben ta mika masa amsa yai yana jifa dashi yace ko mata sun kare saike bazan aure kiba babu abinda zanyi dake bakya cikin kalar matan da nake son kasancewa dasu". Kuka ta saki lokacin daya wuce ta yana shiga part dinsa hannu ta dora aka tana cewa . Na shiga uku zuciya ta baki min adalci ba meyasa zaki kamu dason mutumin da ko kadan jinin mu bai hadu ba". Bayan wasu watanni Fati harta saba da tsangwamar mami data Zainab domin duk wanda zasu kare ta basa nan Afeeyah taje gidan su mami Al'ameen bayanan daddy ba zama yake ba". Kullum zuba ido Zainab keyi da kwadayin ganin Al'ameen amma shiru wai mushiriki yaci shirwa . Suna Zaune a palor Afeeyah data fito ganin yadda zainab ta barbada kwalliya a fuskarta zata fita gurin bikin 'kawarta yasa cikin tsokana tace. "A'a yau kuma harda su biri muka samu a gidan namu lallai kice zamuje wasa". Cikin alamun tambaya Fati tace biri dai? Ke kuma a ina kika ganshi"?. Afeeyah dake shirin fita tace gashi zaune akan kujera ya dora kafa daya kan daya yana kallon fuskarsa a mudubi". Kallon Zainab dake duba mudubi Fati tai sai kuma ta kalli Afeeyah suna hada ido suka kwashe da dariya". Cikin bacin rai Zainab tace ke dan uwarki nice birin"?. Dakatawa da dariyar Afeeyah tai tana nuna ta da yatsa tace" kul kada ki kuskura na sake ji kin ambaci uwata saina zubar miki da hakora". Fita Afeeyah tai daga palon yayin da fati ta mike zata bar palon itama taji ance "Zarah". A firgice ta juyo ganin Al'ameen tai tsaye sanye da kananun kayan da sukai matukar yi masa kyau kuma ya kara kyau da 'kiba. Dan murmushi tai tana cewa