Sashe 3
Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ta tsane taba. Da tazo gidan nan ta rako mahaifin ta mami ta zage ta ta aibata ta ta kafurta ta sannan ta mare ta amma batai zuciya dani ba saboda tana sona". Cikin mamaki daddy yace ita Aishan ce ta mare ta ". "Eh daddy wai tazo har gida zata cinye ni". Murmushi daddy yai kuma an fada mata mayun 'kiri da 'kiri suke kama mutum su cinye shi yanzu dai me za'ai". "Daddy abin da za'ai shine zan aure ta ina sonta da ita zan zauna dan Allah daddy ka fahimce ni itace komai nawa banajin zan samu madadin ta". "Ok yanzu kana so aje nemar maka auren tane "?. Eh daddy wannan shine damuwa ta ka taimaka min". Hannunsa daddy ya rike karka damu zan yi kokari akan hakan zamuje london cikin satin nan domin kudi ba sune kwanciyar hankali ba". Tashi zaune Al'ameen yai ba shiri yana cewa a satin nan na gode daddy Allah ya kara daukaka". "Amin daddy yace yana kallon yadda lokaci guda fuskar Al'ameen din ta washe da farin ciki". Lokacin da mami taji wannan maganar kuka ta fashe dashi na bakin ciki tana cewa yanzu alhaji tsakani da Allah aura masa arniya zakai karya fa take bata sallah". "Shine damuwar ki"?. Shiru mami tai tana goge idanunta da sukai jawur saboda kiyayyar Abni. Ganin taki magana daddy yaci gaba inda rashin sallah shine matsalar me sauki ne zata musulunta tunda tana sonshi kuma ba haramun bane danya aure ta". "Dan haka ranar monday jibi kenan ki shiri za muje london nema masa auren ta kiyi fatan itace alkairi a rayuwarsa". Hannu mami ta dora akai tana sake zunduma wani ihun cikin burgima tace wallahi bada yawu naba kuma ko kofar gate bazanje ba balle naje wata london gurin shegun arna naje su bawa gunki jini, na". "Bazai auro min wata baturiya ba saidai ya mutu baiyi aure ba". "Aishaa" daddy ya fada a tsawace tare da nuna ta da yatsa yace. "Idan ke bakya sonsa ni ina sonsa kuma na amince ya auri wannan baturiyar tunda itace zabun ransa kece zaki zauna masa da yan mata da kike kawo masa"?. "Shashancin banza kin girma amma kina shiga daji bakisan kaddara ba na biye miki kina neman kashe min yaro kamar ba kece kika haife shi". "Saiya aureta idan har matarsa ce saiki dau mataki kuma umarni nake baki ki shirya tafiya ranar monday nan da kwana hudu na gama yanke magana". Yana fita ta mike da gudu tana shiga part din Al'ameen yana zaune ruwan ya kusa karewa tana zuwa cikin karaji da ihu da yage yage kamar me ciwon hauka ta fisge ledar ruwan tana wurgi da ita sannan ta fadi kasan carpet tana shure shure. "Tace Al'ameen ka cuce ni nayi asarar haihuwa Sadiq bai taba sani nayi bakin ciki ba balle kuka haka kanwarka Afeeyah daka girmeta da shekaru sosai bata bani wahala ba. "Amma ka sani kuka na zubar da hawaye saboda kai idan har kana so na yafe maka kaje ka samu daddyn ku kace ka fasa auren wannan banzar yarinyar". Al'ameen dake mata kallon mamaki ganin yadda take kuka kamar yarinya ya mike tare da dago ta yace mami lafiya wani abu ne ya sake faruwa". Fisgewa tai tana cewa ban sani ba wallahi Al'ameen nayi asarar haihuwa amma ba lallai kai dana bane ne tunda haihuwar asibiti nai kila an canza min kai dan da na haifa bazai rika wahalar dani haka ba ". Zaiyi magana ta daga masa hannu babu abinda zakace min baka da wani abu da zaka fada min kaje ka karata" tana fadin haka ta fice a bedroom din. Typing