Sashe 1
Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Root Entry
WordDocument
0Table
Data
[23/06/05, 12:30pm] Yusrah Musa
Abubakar
'DAN MILLIONAIRE
('Dan miloniya)
WHATAPP NO:
+2349055273614
YUSRAH MUSA ABUBAKAR
Mrs Al'ameen Ahmad ce.
(*)(SHORT STORY)(*)
LITTATTAFAI NA
Yarima Abdul-maleek
Rayuwa biyu
Safreeyyah
Haskena sauban
Mina-Umer
Karuwar boye
'Dan millionaira.
Ga me bukatarsu ya tuntube ni ta wannan number
09055273614 littattafai na free book ne ga duk wani masoyi na a duk inda yake afadin duniya I love u with all my body and heart
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION
home of hospitality and
harmony.
In the of Allah the most benefits and the most merciful we love our nabeey s a w we like him and peace be upon him ameen
Some say hello some say hay but in islamically said assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatihu.
Tofa reader's na kumin afuwa wannan karon son kai zan nuna sosai first page na yan group dina ne Annuri ina alfahari dasu may Allah help them any where they are amin.
Page 01 to 02
Wani irin 'kayataccen ginannen gida ne wanda hatta fetin gidan gwal aka nike akai fetin dashi da safe ne amma ko'ina 'kyal'kyali ne ke fita a jikin bangon gidan da dare kuwa har dauke ido yake .
Tsararran palor ne dankarere daya sha kayan alatu na more rayuwa iri daban daban wanda wani abin ma na'ura ce ke sarrafa aikin sa ba mutum ba.
Zaune suke su uku samari ne guda biyu fitattatu na ajin farko yan gayu tsaf dasu kyawawa farare tar dasu kamar larabawa sai mace a tsakiyar su wacce kallo daya zakai mata kasan itace mahaifiyar wadannan zukakan samarin.
Amma kana ganin fiskokin su kasan akawai matsala domin a samarin wanda yafi hasken ransa a mugun bace yake kallo daya zakai masa ka fahimci haka .
Saidai bacin ran bai hana kyansa bayyana ba da kuma annurin fuska.
Cikin fad'a matar ta kalleshi tana cewa "kasan Allah Al'ameen ka fita idona na rufe idan banda shashanci me zakai da wannan banzar yarinyar wacce ba yaren kaba ba jinsin kaba 'kabila tubabbiya yar wata kasar ba zaka je ka yayo min masifa ba duk yan matar kasar ka da jihar ka saika haura wata uwa London to bari kaji bada yawu na ba ban amince ba kuma ko bayan raina ka aure ta ban yafe maka ba sai ka zaba koni ko ita".
Cikin tsananin firgici da tashin hankali wanda ta kira da Al'ameen ya dago kyawawan idonsa yana kallon mahaifiyar tasa jin furucin da take akan wacce bazai iya hada sonta da kowacce mace ba bayajin zai samu madadinta.
Iya kallon da yake mata ya tabbatar mata da cewa Abni ce numfashin sa bazai iya rayuwa ba tare da ita ba wanda hakan yai matukar firgita ta.
Cikin 'kunar rai ta mike bata sake cewa komai ba jin yawun bakin ta ya kame yasa da sauri tabar gurin zuciyarta na turiri da zafin al'amarin yaron nata wanda ta damu dashi .
Dafa shi dayan yayi cikin tausaya masa da halin daya tsinci kanshi na jarabtar soyayya yace "Al'ameen dan Allah kayi hakuri da halin mami tunda bata son wannan baturiyar ka daina furta koda sunanta ne a gaban ta domin mami idan ta fadi magana bata sauyawa kaifi daya ce nasan baza ta taba bari ka aure ta ba".
A damuwance Al'ameen ya dago yana kallon dan uwan nashi yace" ni da kaina na fada mata cewa babu kyau karya alkawari a addinin musulunci saboda ni tabar nata addinin ta musulunta bata yarda tayi imani ba saida na mata alkawarin zan aure ta sakamakon nima ina sonta yanzu me kake tunanin zata dauke ni idan nace tayi hakuri na fasa auren ta wanne irin hali zata shiga dan Allah ka taimaka min".
Kai Sadiq ya jinjina shikenan 'kani na zan taimake ka insha Allahu tamkar ka auri Abni ne domin bana son rasa ka kuma na fahimci itace bugun zuciyar ka".
Wata karamar yarinya ce tazo da gudu tana kuka ta fada jikin Al'ameen cikin rashin walwala yace" momy na me akai miki"?.
Da yatsa yarinyar ke nuna wajen dinning tana cewa he spoiled my shirt".
Kallon farar rigar ta ta yai ganin duk miya ya bata ta yasa ya kalli wajen dinning din wani yaro ne tsaye rike da spoon a hannunshi karasowa gurin yai yana cewa small dad ban sani ba na shafa mata miya a jikin rigar ta sorry sister".
Kafada ta make wallahi bazan hakura ba saika biya ni riga ta kona rama".
Zare mata ido yaron yai yana cewa baki isa ba tunda na baki hakura kuma bazan wanke rigar ba ".
Kuka ta kara fashewa dashi cikin lallashi dason raba rigimar hayaniyar da suke Al'ameen yace" muje na sai miki wata momy na rabu dashi".
Goge hawayen fuskarta tai tana dariya suka fita daga palon yayin da Sadiq shima ya mike yana cewa Ameer meye abin bata ran kaga kada kayi kuka muje kaima na saya maka".
Tsalle Ameer yai yana rungume Sadiq yace thnk dady " rike hannunsa yai suka fita wanda mami najin kara tashin motoci yasa taja tsaki cikin takaici tana bude window ta daga labule tana kallon su har suka fice daga gidan".
Sauke numfashi tai tana cewa amma wallahi Al'ameen sam bashi da hankali ina yabar ajin nasa wata shegiya take neman mayar min dashi shashasha duk yabi ya susuce akanta ko yar uban waye ita a London nata isa ta rabe muba duk kudin su saita raba su kota halin 'ka'ka.
Fita tai daga nata part din tana shiga wata kofa ta bude bedroom tare da lekawa tace" wato Afeeyah baki da hankali ko sai ulcer ta kama ki zaki gane gata ake miki tsabar iskanci kisa waya agaba ki manta da komai bari dadyn naku ya dawo zansa ya karbe wayar ne".
Cikin shagwaba wata budurwa dake kwance a wani makeken gado ta dago tare da cewa kai mami bafa wani abu nake ba kuma indai breakfast ne nayi tun karfe bakwai".
"Hum haka ne da gaske kinyi"?.
Eh mami nida wafer na karya ba abinci naci ba".
"To yayi miki kyau ki fito haka zama ni daya a palon ya ishe ni".
Shikenan to muje mami yadda kika ce haka za'ai mikewa tai suka fito tare yayin da mami ta danna wani karaurawa dake palon".
Da sauri wasu masu kaya iri daya su biyar suka shigo palon cikin ladabi jikin su na rawa suka durkusa tare da gaishe da ita bata amsa ba sai wani kallo datai musu tana cewa.
"A cikin ku wadanne banzayen ne masu lura da dinning mikewa hajar tai tana cewa mune nida ma'u ".
A tsawace mami tace sannu yayan talakawa wato daula tasa zaku fara shagala da abinda ya kawo ku uban waye ya zubar da miya akan farin carpet din can"?.
Zaro ido hajar tai wallahi hajiya ban sani ba tunda mukai servingg dinku ban sake fitowa ba".
"Saboda gaki isashshiya ko ke nana baki karanta musu ka'idojin gidan nan bane domin ba irin kowanne gida da suka sani bane sai wane da wane".
Nana dake shirin magana mami ta katse ta rufa min baki nan gaba aka sake samun kuskure daga wadannan 'kazaman new comer bazan daga miki kafa ba".
Hakuri nana ta taba domin marar abu baya zuciya sannan ta mike da kanta ta gyara dinning din da komai tana komawa bangaren ma'aikata ranta duk ba dadi ta gaji da wulakancin da mami ke mata".
Koda dare lokacin da daddy ya dawo haka mami ta cika ta kumbura tai fam taki sakin ranta akan lamarin dazu".
Kallonta alhaji Mustapha yai cikin mamaki domin da ba haka take ba yace" uwar gida ran gida ya akai ne naga kina fushi meya faru".
Kamar jira mami take ta ture plate din abincin gabanta tana cewa nida Al'ameen ne mana yana neman dora min hawan jini ya kashe ni lokaci na baiyi ba".
"Tofa meya miki haka auta na akwai hakuri kodai kece da tsokana"?.
"Kaji irin abin ko babu dama a fadi laifinsa a gaban ka saika wanke shi tas ".
"Ba wannan ba fada min meyai miki".
"Ranta a hade tace wai dan Allah kaji shi da wani hauka yaje wata kasar ya hadu da yar arna ta kaishi church sun burkita masa kwakwalwa ya dawo ya susuce".
"Subahanallahi da yaushe wani abu kika ga yana yi wanda ya saba hankali"?.
"Yo meye ma baiyi ba alhaji dazun nan na gama cin kaniyarsa akanta ala dole ita yake son aura duk Nigeria baiga wacce tai masa ba saiya debo mana masifa da bala'i sun zuge mana jini".
"Gaskiya ka sameshi ka masa fada tunda ni na gaza yaki fahimta ta".
"Ok yayi shikenan karki damu uwar gidan Mustapha Aminu zan same shi as you wish kamar yadda kike so".
Murmushi mami tai cikin farin ciki yauwa alhaji yanzu naji magana nina manta sunan shegiyar yarinyar ma sunan kalar amai"
Ki daina rage mata alhakin data deba a cocin tunda kince kirista ce".
Allah wallahi abin ne da haushi duk gayun sa da tsananin kudin ka maimakon ya nemi yar shugaban kasa nasan duk inda yaje neman aure da gudu za'a bashi".
Kai alhaji Mustapha ya jinjina yana mamakin mami daga anyi magana saidai ta ambaci kudi
BY MRS AL'AMEEN AHMAD CE.