Sashe 11
Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aure. Kamar tasan abinda ke ransa sai ranar tafiya tace zataje baiso haka ba amma ya rabu da ita a tari gaba. Harda Rukayya Zainab ma ta bisu wai zata gano kauyen su Fati wanne kalla ne. Ranar daurin aure sukaje kwana biyu zasuyi Rukayya kam suna sauka ta debi yaranta ita da Sadiq suka tafi gidan hajiya acan zasu zauna domin sun saba sosai. Fati da Afeeyah gari suka shiga Zainab da batasan garin bama haka ta fita yawanta ita kadai har kasuwar garin. Lokacin da suka dawo Fati ta tsaya a gurin babarta Afeeyah kuma ta shiga gurin mami cikin fada mami ta kalleta tana cewa. "Wato Afeeyah kin biyewa wannan shegiyar yarinyar ko wai kune har kasuwa wani ya sai muku nama dan ubanki saiya sa muku magani a ciki. Cikin mamaki Afeeyah tace ni kuma mami da yaushe waye ya fada miki"?. "Nice domin na ganku da idona" Zainab ta fada tana sakin murmushi tare da yimata gwalo. Takaici ne ya kama Afeeyah wato sharri Zainab ta kulla musu jin mami tace wallahi kika kara binta yawo saina ci ubanki". Yasa ranta a bace tace nifa mami ba muje kasuwa ba karya tayi min". Ita kike cewa ta miki karyar saboda baki da kunya wannan yar 'kauyen ta koya miki rashin arziki". Shiru Afeeyah tai karshe ma ta mike zata bar dakin mami tace gidan uban wa zakije ko yawon barbadancin zaki koma". Kamar Afeeyah zatai kuka tace babu inda zanje fa kawai cikin gidan zan shiga". "To cikin gidan da zaki shiga kin aje wani abu ne"?. "Gurin yan uwana zanje". "Dakyau sannu me yan uwa mu kuma daga gidan marayu muke ko? to dawo ki zauna har gobe da zamu tafi babu inda zaki sake fita" dawowa Afeeyah tai tana kwanciya akan katifa cikin tsantsar bacin rai. MRS AL'AMEEN AHMAD CE Page 23 to 24. Washe gari suka koma Abuja Fati da kukanta ta shiga mota dan cewa tai baza ta bisu ba ta dawo gida kenan saboda tsangwamar mami da take sha dakyar dady ya lallameta suka tafi". Wanda suna komawa mami ta hura wutar sai daddy ya daurawa Al'ameen aure da Zainab wani lokacin har kuka take da hawaye a gaban sa. Afeeyah na zaune a palor misalin karfe bakwai da rabi na safe Fati ta fito ganin ta yasa ta tsaya tana cewa . Na dauka kina kitchen muje kada lokaci ya 'kure ". Afeeyah dake duba abu a waya tace a'a ke kadai zaki nan da kwana hudu domin ina period idan yayana yaji sai yafi kwana goma baici abinci a gidan nan ba". "Wanne yayan naki"?. "Al'ameen mana ya Sadiq yana can gidansa da matarsa me zai kawo shi yin breakfast gidan nan. 'Yar dariya Fati tai tana zama kusa da ita daidai Al'ameen ya fito batare daya kalli inda suke ba yace. "Naji abinda kika ce " yana fadin haka ya fita a palon rufe baki Afeeyah tai". Fati dake kallonta tace to kinji abinda yace" mikewa tai suka shiga kitchen din dama saboda shi ne bazata taba kayan aiki ba. Al'ameen gidan Sadiq ya wuce a dinning ya same su Amir da Aisha sai fada suke kamar kaji ga driver yana jira zai kaisu makaranta. Zama yai yana hada tea bai kalli kowa ba cikin tsokana Sadiq yace sannu matashi ziyara ka kawo mana da safen nan kenan". Al'ameen dake shan tea yace no breakfast nazo yi kawai". "Ina na gidan ku" cewar Sadiq. "Yana nan kawai na fito naji yaran nan suna zance period shiyasa bazan iya cin abincin gidan ba". "To ai nima period din nake" Rukayya ta fada cikin boye dariyarta. Aje cup din Al'ameen yai tare da sauya fuska zaiyi magana sai kuma ya fasa yana mikewa ya fice. Da kallo suka bishi Sadiq ya girgiza kai yana cewa Al'ameen na rasa wanne kalar 'kyan'kyami gareshi ace mutum bazai ci abincin me period ba saboda me"?. Dariya Rukayya tai tunda haka kawai idan yayi aure basai ya dauki yar aiki ba saiya samo namiji". "Tab Al'ameen dinne zai dau namiji dan aiki a gidansa lallai har yanzu bakisan waye shiba bari na wuce hospital kada na makara da yawa". Al'ameen na zuwa gida ya soma sheka amai kamar ba gobe karshe ma zazzabi ne ya rufe shi amma duk da haka bai fasa ba domin Lagos zasu wuce yasa kayan army dinsa kawai ya tafi". Kwana uku da faruwar haka suna zaune shida Sadiq a palor ranar weekend cikin tsarguwa Sadiq ya kalli Al'ameen yana cewa". "Wai kai na tambaye ka mana murmushin me kake tun dazu"?. "Babu murmushin jin dadi ne kawai saboda na fahimta na gane wata gaskiya". "Gaskiya ta me kenan". "I am in love". Zaro ido Sadiq yai cikin mamakin furucin Al'ameen din jin zancen nasa kamar mafarki yace. "Da gaske kake ka samu wacce kake so"? Lallai zanso ganin yarinyar me sa'a data sace min zuciyar dan uwa na wacece ita a ina take ka sanar dani"?. "Ok zan fada maka amma ba yau ba saboda tsaro ita din tauraruwa ce me haske zuciya ta saida ita ina sonta so me tsanani ma". Sadiq da dadi ya gama cika shi cikin farin ciki yace mene sunan ta"?. Dan shiru Al'ameen yai kamar me tunani sai kuma yai murmushi yana kallon sadiq yace Zarah "' "Zarah yar waye" Sadiq ya tambaya. Al'ameen yace no zaka santa ba yanzu ba tana da daukar hankal........... Bai karasa ya dakata tare da kafe guri daya da ido muryarsa cikin wani yanayi yace" Zarah no one but you, I love u with all my body and heart bana iya hada ki da kowa". Kallon inda yake kallo Sadiq yai wanda har saida yadan zabura yana dafe Al'ameen cikin mamaki yace" wai dama Fati na nan gidan kake nufi"?'. "Eh ita bansan ya akai ko kuma yaushe bane haka nan rana daya na tashi naji na kamu da ciwon sonta kuma zan aureta ina da ra'ayin zama da ita zuciyata ta Abni ce amma yanzu ta Zarah ce . "Wow gaskiya na taya ka murna ka kuma yi dacen mace idan har ka aureta domin tana da tarbiyya. "Haka ne kyawawan dabi'unta ne suka rinjaye ni amma alfarmar da nake nema a gurin ka shine ya zama sirri tsakanin mu kada kowa ya sani". Murmushi Sadiq yai cikin tsokana yace babu wanda zan fadawa masoyi zasu sani da kansu". Bayan watanni uku Al'ameen na zaune a gaban su mami yana sauraron kiran da sukai masa'. Daddy yace" wato Aminullahi dama batu ne akan aure ka samu wacce kake sone"?. Kai Al'ameen ya girgiza a'a daddy babu". "To maminka ce tace ya kamata a hada ku aure kai da Zainab shin me kake gani hakan yayi maka". Caraf mami tace wanne irin yayi masa bashi zamu biye ba . Daddy da hankalinsa ke kan yanayin da Al'ameen ya shiga yace bake na tambaya ba saiya yarda idan bai amince ba dole abar batun". Kuka mami ta saka tana cewa shikenan nikam na kade na gama yawo alhaji meyasa kake min haka ne. Hade rai daddy yai yana cewa Al'ameen tashi kaje kada ka damu Allah ya baka wacce kake so ta maye maka gurbin waccan. "Amin daddy na gode" Al'ameen ya fada cikin jin dadi yana mikewa ya fita. Mami dake goge hawaye tace yanzu alhaji haka ak......'. Katseta daddy yai saurara Aisha bansan shashanci mubar maganar shiru mami tai tana sauke ajiyar zuciya takaici ya gama cika ta. Yau da gobe tafi karfin wasa daddy ya gaji da nacin mami ta hana shi sakat tabi ta hargitsa kanta ta hargitsa gidan saida ya amincewa abinda take so. Suna zaune Zainab ta fito cikin shiri zata fita tana kallonsu babu gaisuwa sa'kam-sa'kam tazo zata wuce. Cikin tsawa mami tace ke gidan ubanwa zakije da yammar nan. Dan tabe baki Zainab tai tana cewa bikin kawata ake zanje mata gurin event data gayyace. Mikewa tsaye mami tai koma ciki babu inda zakije". Zaro ido Zainab tai tana cewa tabdijan kinsan yadda muke da ita kuwa. Mami tace dan ubanki ni kike cewa tabdijan ina matsayin yayar mahaifiyarki zaki iya fadawa Binta. Zainab dake kad'a key din mota tace sosai ma saidai idan batai min abinda zance matan bane kinga ni kina bata min lokaci na wuce dan banga me hana ni naje ba . Tana fadin haka ta bude kofar palor ta fita tana wa'ka mami data bita da kallo tace jimin shegiyar yarinya zaki dawo ki same ni ne". Wani irin kallo daddy ya mata wato wannan yarinyar take son aurawa dansa yarinya mara tarbiyya amma bari ya kyaleta tayi gaban kanta babu ruwansa. Batare da Al'ameen ya sani ba domin bayanan aka karba masa auren Zainab a gurin mahaifinta ranar mami kamar ta zuba ruwa a 'kas tasha dan farin cikin har ta 'kagu lokacin biki yayi ta ganta tare da Al'ameen muradinta. Afeeyah kam iya damuwa tayi saidai ba yadda zatai har daddy ta samu da kukanta amma yace tayi hakuri matar mutum kabarinsa komai me wucewa ne. Al'ameen yasan da zancen domin Afeeyah ta kira shi a waya ta fada masa amma yai burus kamar abin bai dame shiba saidai bazai taba kallonta matsayin mata ba. Biki ya matso ya kankama sai shiri akeyi mutari ma da tawagarsa sukayo mota guda harda hajiya ranar farin ciki a gurin Fati ganin mahaifiyarta. Suna zaune a bangaren baki sai kalle-kalle suke mami tasa nana ta kai musu abinci da abin sha me kyau wanda basu taba ganin irin saba. Shigowa mami su gaisa da yake a cikin farin ciki take saita saki fuskarta har tana tambayarsu. "Sannun ku da zuwa hajiya fatan kunzo lafiya akace tun asuba kuka taho amma baku zo da wuri ba. Saude data yago cinyar kaza tace" wallahi nake fada miki da wuri muka taho 'yan ro santi ne suka tare mu". "Ro santi kuma"? Mami ta fada cikin rashin fahimta. Saude tace eh wallahi sune suka tare mu sunaiwa driven mu rashin arziki". Dariya Afeeyah tai sosai tana cewa wai yan road safety kike nufi"?. Mami tace" oh sune yan ro santi"? Gaskiya ne bari na dawo" ta fada tana mikewa domin zama dasu ya isheta . A ranar