← Book details Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba yau saboda alhaji yadau fushi bansan mezai faru ba muje gurin Binta" mota suka shiga suma suka bar gidan. Sosai Sadiq ya duba Fati duk abinda ya dace ya mata kuma Alhamdulillahi babu abinda ya samu babyn. Sosai daddy da Afeeyah sukai murnar jin haka kuma suka godewa Allah. Kwanan mami uku a gidansu Zainab bata koma ba saboda tsoron haduwarta da daddy saiyau ta shirya taje asibiti gano Al'ameen. Tana shiga dakin ta ganshi a zaune fati na gefenshi wata uwar harara ta wurga mata tana cewa. "To sarkin kinibibi mahaifiyarsa tazo saiki fita ki bamu guri zanyi magana dashi kinzo kin gurbata mana zama kin zama ba'kar ashana fita nace me idanun mayu kosai kin lashe min tawa kuruwar nima kamar yadda kika lashe tasa mayya kawai". ? Mikewa Fati tai cikin takaicin maganganun da mami ke fada mata ta fita waje tana share hawaye haduwa sukai da Sadiq ganin tana kuka yace. "Zarah lafiya ina zakije ko wani abune ya samu Al'ameen din"?. Kaita girgiza" babu komai gida zan tafi". "Amma Zarah meyasa? ki bari sai dare mana". "Mami tazo itace zata wuni a wajensa". Kallon tsaf Sadiq ya mata haba shiyasa take kuka yasan da dalili. "Ok muje na kaiki to"fita sukai domin ya mayar da ita yana kuma sake bata hakuri. Page 35 to 36. Fati na palor a zaune bayan Sadiq ya ajiyeta ita kadai tai shiru ta nutsa cikin tunani da mamakin wacce irin 'kiyayya mami ke mata abin ya wuce ma hankalinta. Jin karar bude kofa yasa ta dago mami ta gani ta shigo jikinta ne ya soma rawa kamar taga hallaka. Zama mami tai tana kallonta fuska babu wasa tace" ba wata tsiyar ta kawo niba na baki minti biyu ki shiga ki tattaro kayan daud'ar ki kibar gidann nan yadda kikai silar fitar Zainab to kema ya zama haramiyarki saidai ya auro wata yasa". Hawaye suka gangarowa Fati da sauri ta goge tana juyawa ta shiga part dinta bata dade ba ta fito mami na zaune tana kad'a kafa ganin ta fito yasa ta mike tana sakata gaba da, tsinuwa suka fita harabar gidan. Karbe key din gidan tai a hannun Fati sannan taiwa driver umarni cewa. "Ga wannan bagidajiyar ta nuna maka hanyar kauyensu ka mayar da ita yau sai kwanan tabarma cikin 'kunci da zafi ba a.c sai ai ta fama da mafici daula kinyi bankwana da, ita". Tana gama fadin haka ta shige motarta ta fice daga gidan Fati na kuka ta shiga mota bangare guda tana farin cikin barin masifar mami datai. A ranar Al'ameen yabar asibitin Sadiq ne ya kaishi har gida sannan daya huta ya tafi nasa gidan. Karfe goma daidai Al'ameen yace zai tafi gidansa tari mami batai masa ba balle ta nuna masa cewa ta koreta. Tana kallonsa ya fice daga palon dariya tai tana cewa "hummm yaro man kaza ai kaida wannan shegiyar yarinyar har abada je ka dawo ina daidai dakai saika saketa". Kamar an jefo Al'ameen haka mami ta ganshi murmushi tai tana dauke kanta daga saitinsa tace "a'a me kuma ya dawo dakai"?. "Mami ina Zarah"?. "Tambaye nidai baba tunda ajiyarta ka bani". "Mami I know what u have done to my wife na roke ki daki fada min inda take me kikai mata". "Ban sani ba zo ka rufe ni da duka saina fada maka inda na kaita". "Dan Allah mami mubar wannan maganar ina key din gida na"?. cikin gadara mami dake zaune tasa glass da laptop gabanta tana aiki tace". "Wanne gida kake dashi daya wuce nan ai daga yau ka dawo gidan ku da zama zansa a gyara maka part dinka gobe". "Meyasa mami bayan ga gida nacan da matata taya zan barta ita kadai na dawo nan". "Allah ko sannu me mata karka batawa kanka lokaci na kora ta garinsu". Wata irin juyowa Al'ameen yai yana kallon mami cikin tsananin mamaki yace mami kin kora ta garinsu saboda me"?. "To babana matse ni saina fada maka dalili kuma ban yafe maka idan kaje wannan matsiyacin kauyen balle kace zaka dawo da ita yadda ka ci mutuncin Zainab ka wulakanta ta ka saketa haka itama nake so ka rubuta mata takardar saki uku ba maganar kome saidai ka auro wata". Wata iriyar hajijiya ce ta debi Al'ameen da sauri ya zauna tare da dafe kanshi maida hankalinta mami tai akan aikin da take tana cewa". "Kome zakai saika saketa bazan taba daukarta matsayin suruka taba". Jin tafiya yasa ta dago ganin daddy ne tadan zaro ido tana fatan Allah yasa baiji zancen da suke da Al'ameen ba. Shi kuwa ya riga ya gama jin komai muryarta nadan rawar rashin gaskiya domin tun ranar da ta daki Fati basu sake haduwa dashi ba saiyau tace. "Sannu alhaji". Banza yai da ita ya dauke mata wuta kamar baiji ba ya karasa inda Al'ameen ke zaune yana dago kansa. Ganin hawaye a fuskarsa abinda ya manta yaushe rabon daya gani tun yana yaro saiyau cikin tsananin bacin rai da fushi ya juyo inda mami take yana kallonta yace. "Yau tafaru ta kare Aisha kullum ina miki gargadi dajan kunne bakya dauka to yau zakiga sakamakon abubuwan da kike aikata min". Part dinsa ya shiga mintuna biyu ya fito da takarda a hannunshi yana cilla mata cikin kakkausar murya yace". "Ita kin bata minti biyu ni kuma minti daya na baki kada ki kuskura na fito na sameki kibar min gida na". Mikar da Al'ameen yai yana shigar dashi part dinsa sannan ya fito ganinta zaune tana kuka yasa yace ki fita a gidan ko a hanya sai kiyi domin na gaji da ganinki". Cikin kuka mami tace alhaji kayi hakuri bazan sakeba na tuba". Kai ya girgiza ai Aisha bazan iya sake zama dake ba kina lalata min zumunci da hana zaman lafiya ya zaga ahli na". "Wallahi alhaji kaban dama na karshe zan gyara hali na tun muna kuruciya banje gidan mu da sunan yaji ba saiyau naje da takardar saki wannan abun kunya har ina alhaji ka dubeni". "Ai Aisha abinda ya dace dake na baki hukuncin ki kenan". "Kayi hakuri kamin sutura alhaji zan gyara kuskure na namaka alkawari". "Aisha bazan miki uziri ba a yanzu rayuwa ta bata bukatar ki na datse duk wata alaka dake tsakanin mu"'. Cikin kalar tausayi mami ta durkusa gabansa tana masa magiya amma sam ya dauke kai daga saitin ta. Mikewa tai ganin babu alamar zai karbi bada hakurinta tana kallonsa tace" na baka hakuri amma alhaji ka 'ki.............. Katse ta yai "ki barmin gidana bana son jin komai daga gare ki" bar mata falon yai . Dole mami tahau tattara kayanta kamar yadda taiwa wata itama ta nufi gidansu cikin bakin ciki da kunyar yadda zata fuskanci mahaifanta. Ranar kwana cur mami tai a zaune bata ko runtsa ba tana kuka har zazzabi da ciwon kai suka rufeta. Washe gari ma haka ta wuni rim a kwance babu cin abinci babu shan ruwa ga fadan da tasha gurin dattijon mahaifinta. Nadama iri iri babu wacce mami batai ba da dana sani domin a rayuwarta tana matukar son daddy kamar ranta. Fati na zaune a kofar dakinsu tana gyarawa umman ta waken da za'ai abincin rana Saude ta fito daga dakin ganin Fati zaune yasa tace. "Humm yan birni har dubun naku ta cika asirin da kukai musu ya karye ko kuma kinyi halin 'bera sun fatattako ki ko"?. "Meye gaskiyar al'amarin fada min gashi zaki abin kunya ki haihu a gida tir da wannan abu ina tausaya miki domin zilamar uwarki dason zuciyarta ne ya jawo miki". "Koma dai ba cikinsa bane shiyasa suka koro ki iye fada min naji domin yadda idonki yake a tsayen nan zaki iya aikata komai maganin son banzar ku kenan kunga kudi shine kuka rude saida kuka shiga jikinsu ai dama duk wanda yahau motar kwad'ayi yasan baida gurin sauka sai tashar wulakanci". "Kiyi addu'a kada ki haihu su 'ki karbar d'an yan kauyen nan su samu abin gori kI shafawa danginku ba'kin fenti". "Koda yake nasan me za'ayi zan taimake ki na karbo miki magani kawai kisha d'an ya mutu ko idan kin haifeshi ki sha'ke masa wuya bada sanin kowa ba kinji zan rufa miki asiri babu wanda zai sani amma kudin da kika sato musu daga can zamu raba idan kin yarda"?. Ko dagowa Fati batai ta kalli Saude ba balle tayi tunanin zata bata, amsa kawai aikinta take". Tsaki Saude tai ke dalla gafara don ma za'ai miki sutura shine kike min wani gani gani wato ke uwar dabaa lamba d'aya ko"?. "Aiko kin shiga uku a gurina dan saina zaga kauyen nan na sanar dasu kinyo cikin shege a birni". " ta fada tana saka hijab tare da rufo dakinta tai hanyar waje tana cewa" bari na fara daga makotan mu su tabawa da Aliyah" da kallo Fati ta bita tana share hawayen daya zubo mata". Shigowar Salamatu ganinta haka yasa ta tambayeta" Fatima lafiya kike kuka? kiyi hakuri kaddararki kenan ki dage da addu'a babu abunda ya gagari ubangiji shine mai bayarwa,". Kukan Fati ne ya fito fili cikin damuwa tace "umma ba laifin Al'ameen bane baisan ma na taho ba yana asibiti mami ce ta min komai". "Duk da haka kinga ki kwantar da hankali komai yai farko wata rana zaiyi karshe idan Al'ameen mijin zaman kine zaki koma". Kai Fati ta girgiza tace "nifa umma wannan ba shine matsala taba damuwa baba Saude yanzu tasa hijab ta fita wai seta zagaye garin nan tace ba wani aure danai cikin shege ne". Kirji Salamatu ta dafe tana kallo Fati tace" ita Sauden ce tace haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah gamu gareka kaine gatan mu". Fati data sauke ajiyar zuciya tace" amma umma ya kamata a dakatar da ita kinsan halin kauyen nan da kama abu ina tsoron sharrin su". "Ya zamuyi Fatima waye zai iya dakatar da ita baban kune kuma baya nan sharrinta bazai tasiri ba domin muna da gaskiya ita kuma 'karyarta koda tayi fure bazatai 'ya'ya ba dan 'karya 'karya ce koda an lullubeta da sutura". "Shikenan umma zan dage da addu'a Allah ya saukaka min abinda ke damu na yasa karshen wahala ta kenan". "Yauwa Fatima
Chapter 17 · 0% Book details