← Book details Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nemawa d'anki aure kika zo". "Nidai wallahi ba ason raina nazo ba gaskiya ka biya min kudin jirgi na tafi gida". "Aisha idann kinga na biya miki kudin jurgi munyi abinda ya kawo mu muddin baza ki jira muba saidai ki biya kudin jirgi da kanki". Bakin ciki ne sosai ya mamaye mami ga koshi ga kwanan yunwa dole ta hakura dan bazata zare wadannan mmakudan kudin ta bbiya jirgi ba". Satin su guda babu wani labari don haka mom da daddyn Abni suka roki alfarma a bari su shiga su ganta ko minti biyu ne". Tare da Al'ameen suka shiga Abni na kwance akan gado ganin Al'ameen yasa tadan juyo saitin sa muryar ta can kasa tace" Al'ameen kaga halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashin ka ko na sani ba tashi zanyi ba inai maka fatan alkairi ka kasance cikin farin ciki Allah ya baka madadi na". Kai Al'ameen ya girgiza" a'a ki daina cewa haka kece nake so Abni zaki warke muyi rayuwa tare bana fatan na raasa ki tare da mahaifa na nazo domin su karba min auren ki please A bni ki tashi muyi rayuwa me kyau". Dan lumshe ido tai tare da budewa tana kallonshi ta riko hannunshi muryarta kamar bata me jinya ba tace. "kada ka damu zaka kasance cikin farin ciki koda babu ni bazan taba rabuwa dakai ba muna tare bazan taba barin ka ba". Tari ne ya kama ta harda jini ke fita a bakin ta da sauri su mom suka yo kanta kallon su tai bata ce komai ba". Al'ameen wanda tashin hankali da rashin nutsuwa sun mamaye shi ya sake rike hannunta wani zobe ne a yatsan ta tacire shi tana baiwa Al'ameen . Ganin tai shiru yasa da karfi Al'ameen ya kira sunan ta bude ido tai tana murmushi a hankali ta furta" I LOVE YOU AL'AMEEN". Daga haka bata sake cewa komai ba sai kallon da yaga ta koma yi masa wanda bai gamsu dashi ba jin ta sake hannunsa yasa yace Abni Abni Abniiiiiiii da mugun karfi yaja sunan. Ji yai daga bayansa mom ta fashe da kuka domin shakka babu Abni ta rasu". Ganin dayai daddyn ta ya matso ya lullube ta yasa hannu zai bude rike masa hannu daddyn yai yana girgiza kai". Wanda hakan ya tabbatar masa da mutuwa tai a take ya fadi a gurin ya suma [23/09/05 12:44pm] Typing ANNURI W ASSOCIATION Home of hospitality and harmony YUSRAHMS CE Page 11 to 12 Fitowar Afeeya kenan zata tafi makaranta Zainab tasha gabanta tana cewa ke dan rainin hankali wato ke isashshiya ko maza ki koma saikin gyara bedroom din idan ba haka ba ki hakura da zuwa makarantar". Wani kallo Afeeyah ta mata. cikin rainin hankali tace Allah ko mami da gaske kike"? To bazan gyara ba makaranta zanje ba irin kice me zaman kashe wando a gida ba zan fita idan kin isa ki dakatar dani ko kidau mataki". Da kallo Zainab ta bita lallai yarinyar nan zaki ci ubanki bin bayan ta tai da sauri daidai Afeeyah ta tashi mota tasha gaban motar. Afeeyah bata fasa ba tayo kanta zata bigeta da gudu Zainab tai tsalle tana fadawa cikin fulawoyi Dariya Afeeyah tai tana lekowa ta glass din motar tace au dama zaki gudu dakin tsaya saina maida ke gurguwa nakasashshiya nasa ki zama mabaraciya a cikin gari amma a juri zuwa rafi mu zuba nida ke dan halas ka fasa". Tana gama fadin haka tai kofar gate tsaki Zainab tai tana mikewa ganin yadda ta taba farar rigarta domin ba a dade da yiwa flowers din bayi ba". Tana komawa ciki hajiya binta na fitowa ganin kayanta a bace yasa tace daga ina meye ya bata miki riga"?. Cikin takaici Zainab tace waye zaimin haka idan ba wannan shegiyar yarinyar Afeeyah ba". Toke meye damuwar ki da ita kuna yan uwa amma jinin ku bai hadu ba". "Yo umma dan ubanta waye jakin ta da zata kwanta da safe bazata gyara gado ba". "Ok akan haka ne amma dai aiba wani ne ya hana kiba kece kikai ra'ayi" . "Allah ni umma bana son yar aiki tana shiga daki na tana kallon asiri na". "Yayi masu asiri karki sake cewa ta gyara miki gado bansan shashanci". Cikin jin haushi Zainab ta mike tana 'ku'kuni tabar palon hajiya Binta data bita da kallo tace humm Zainab kenan indai Afeeyah ce tana daidai dake". Kwana Al'ameen yai a sume baisan inda kansa yake ba sosai daddy ya shiga damuwa mami kam suman Al'ameen bai d'ara taba saima wani irin farin cikin data tsinci kanta aciki na muutuwar Abni din ji take kamar ta taka rawa Wanda dole sai a asibitin suka baro shi domin bai dawo hayyacin saba Abni kuwa tun jiyan akai mata sutura Abuh da 'kawayen ta suna zaune a dandali suna musu akan samarin 'kauyen suka hango Fatima tsaye a 'karkashin wata bishiya tana dariya". Rabi tace lah Abu ga hegiyar gidan ku can tana dariya ita kadai kamar me aljannu". Abu data kalli gurin tace barni da yar iska tunda bata da samari dan ta fini kyau a banza". "Ahayye ji tsinannun munafikai wato kun zauna kuna gulmar 'kawata ko inji uban waye ya fada muku bata da saurayi ita data fi kowa sa'a ma tunda Sa'adu ne yake sonta dan gidan me gari". Juyawa sukai inda ake maganar suka ga Asabe tsaye da itace a kanta alamar gida zataje daga gonar baban su take". 'Duuuu sukai kanta zasu rufe ta da duka ta sauke icen tana zaro guda daya tace naga hegiyar da zata taba ni saina fasa mata kai". Duk tsayawa sukai cikin huci Abu tace idan kin isa ki aje itacen mana wallahi saina fasa miki baki". Aje itacen Asabe tai tare da shakar wuyan Abu wacce batai zato ba tana cewa" na aje da kina nufin dan kina tare dasu yasira bazan iya dukan kiba zanji tsoronki". Idon Abu sun fitfito sakamakon Asabe jibgegiya ce dakyar ta samu su Balki suka babbare hannun Asabe daga wuyanta". Tari ta kama yi babu kakkautawa kamar zata shide Asabe data dau kayanta tace nan gaba ki sake kawo min raini saina kusa kahe ki shashasha". Saida Asabe ta tafi sannan rahma ta samu bakin magana kiyi hakuri Abu bamusan zata shake kiba amma nan gaba zamu shigar miki Tsaki Abu taja ke dalla matsa gefe matsoraciyar banza duk yawan ku mutum daya ta gagare ku". Ihu suka sa mata suna wakarsu ta dandali suka ce dama waye ya tsokane ta tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka. Mikewa Abu tai a fusace tana kallonsu tace kada hegiyar data sake kula ni a cikin ku tsinannu kawai". Dariya suka kwashe da ita suna tafawa to sai me dan mu daina kula ki wata uwar kike bamu. Daukar fantekar abincin ta Abu tai tana barin gurin dama a wuya take domin tayi kwashe ilya baizo ya sayi abincin ba". Mrs Al'ameen Ahmad ce Page 13 to 14. Satin Al'ameen guda aka bashi sallama ya dawo gidan su Abni nan sabon ciwon sonta ya bude babi ganin da daddy yai ba warkewa Al'ameen zaiyi su dawo Nigeria ba yasa yace wa su mom kawai zasu koma gida". Anan daddyn Abni yace mr Mustapha mezai hana ka amince a bashi 'kanwarta Saira". Al'ameen dake gefe tun kafin daddy yai magana yace a'a daddy na hakura bazan yi aure ba a rayuwa ta". "Me yasa my son? da Abni da Saira daya ne"?. Kai Al'ameen ya girgiza yana cewa" daddy bazan iya auren Saira ba badan bana son hada jini daku ba dan Allah ka fahimce ni aure ya fita a raina". "Shikenan son ba komai na fahimce ka" alhaji Mustapha ya kalla cikin fara'a yace babu komai ai muna tare mun zama dangin juna Allah ya tsare hanya yasa kuje gida lafiya". Anan mami ta gane cewa da gaske Al'ameen yake ashe gidan su Abni musulmai ne amma itafa duk da haka gara da Abni din nan ta mutu hankalin ta ya kwanta yanzu d'anta zai dawo daidai. Sosai alhaji Mustapha ya tausaya musu kuma ya sake yi musu ta'aziyyah da godiya akan abinda sukai musu "gaskiya kuna da karamci mun gode sosai Jonah mu zamu tafi". Har airport sukai musu rakiya sannan suka sake yin ban kwana da juna. Wanda Al'ameen baisan lokacin daya rungume Jonah ba hawaye na zuba a idonsa". Mami taji haushin rungumar dayai masa Allah-Allah take su tafi kamar tana kan 'kaya dakyar Al'ameen ya saki Jonah suka shiga jirgi domin dawowa Nigeria. Mutuwar Abni hatta Sadiq da yazo gidan washe garin da suka dawo mutuwar ta taba shi wani irin mugun tausayin dan uwan nasa ne ya kama shi". Yace" Al'ameen kayi hakuri dan Allah kada kasa damuwa aranka ka zama musulmi me daukar kaddara da cinye jarrabawarka Allah ya canza maka da mafi alkhairin Abni a rayuwar ka". "Amin" kawai shine abinda Al'ameen yace dan bai cika magana sosai ba Afeeyah tayi kuka sosai domin ya taba bata wayarsa sunyi vidio call da Abni kuma sun saba da ita sosai". Tana kwance akan kujera tai ruf da ciki idonta a rufe kamar me bacci saidai zurfi kawai tai cikin tunani mami dake tsaye a kanta tana kiran sunan ta . Ganin bata amsa ba yasa afusace ta sakar mata duka wanda a razane ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya me karfi tace " mami lafiya". Tsaki mami tai tana cewa wato kema ashe sakarya ce ban sani ba ko dan ubanki wannan yarinyar dangin kice zaki dorawa kanki masifa kullum kina cikin tunani wanda kila koni na mutu bazaki damu haka ba". Hade rai Afeeyah tai tana kau da kanta gefe cikin takaici tace mami ko makiyin kane ya mutu jikinka yana sanyi balle Abni me ta tare miki wanda tabar duniyar baki daina ambaton taba". "Kwarai Afeeyah zage ni zamani ne yaya su zagi iyayen su kwalliyace duniya tazo karshe dan jakin ubanki har tambaya ta kike me tai min ta kusa kashe min yaro ta mutu ma ban huta ba kema da baki je ba gashi nan ta hada da kurwarsa da taki ta tafi dasu lahira meye na bata lokacin ki wajen tunanin ta kome
Chapter 5 · 0% Book details