← Book details Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'DAN MILLIONAIRE #Comment #Fallow. ANNURI WRITER'S ASSOCIATION Home of hospitality and harmony. Yusrahms Abubakar Mrs Al'ameen Ahmad ce. Page 03 to 04. Sati biyu da faruwar haka Al'ameen na zaune shi kadai a palor yaji wayarsa na kara wakar da Abni ta dora masa ce tun a London . Yana kallon screen din wayar saida gabansa yai mummunar faduwa ganin sunan Abni din baro-baro. Bai daga ba saida ta katse ya kira ta amma abin mamaki data daga saiya kasa ce mata komai kawai yai shiru yana sauraronta". Jin yayi shiru yasa tace dear lafiya kwana da yawa wayar ka a rufe kasan irin tashin hankalin dana shiga kuwa please kada ka sake". Sauke ajiyar zuciya yai muryarsa kamar yana mura yace fatan kina lafiya ina mom da saira ko kina ma'aikata ne kamar naji hayaniya". Dariya tai domin tana da yawan fara'a tace a'a kawai dai zan baka mamaki ne". "Kamar ya wanne iri"?. "Idan nace maka ina kasarka Nigeria zaka yarda ". Zuciyarsa na harbawa sosai kamar zata fito waje yace zan yarda amma da gaske kike kina Nigeria"?. Allah dear ina nan Abujan ku ba nan kace state naku ba na rako daddy na ne wani aiki baifi sati zamuyi ba". "Ok you are welcome". "Thank dear amma yanzu ina ne zan same ka domin na sanar da dad dina zamu zo gidan ku"?. A firgice da karfin gaske har saida ya tsora ta yace "what you mean........ "Yes ta katseshi batare daya karasa ba tace ka sanar dani addresss din gidan ku". Babu yadda ya iya dole ya tura mata kamar yadda ta bukata tare da dafe kansa cikin damuwar mezai iya faruwa". Fitowar mami kenan ganin a yadda yake yasa ta fasa wucewa ta tsaya tana cewa "lafiya meye ya faru na ganka a haka kodai wannan banzar yarinyar kad'anin kake tunani da wahalar da kanka a kant.......... Bata karasa ba taji anyi sallama da wata irin murya da ba hausa ba kanaji kasan yare ce". Juyawa mami tai ganin mace tsaye bakin palor fara tar jawur baturiya yasa cikin kaduwa tace" wace ke ya akai me kike nema anan din"?. Dan murmushi tai idonta nakan Al'ameen da shima ita yake kallo tace "barka da gida mah suna na Abni Jonah daga London nazo gurin dear ne" ta fada tana nuna Al'ameen. Wata irin zabura mami tai tana jefar da glass cup din hannunta ya fadi ya tarwatse idonta kamar zasu fito waje dan razana tace". "Me Abni Jonah wato kece wannnan matsiciyar yarinyar da kika lashe kurwar dana ko baya ganin ko wacce mace saike shine yanzu kika biyo shi har kasar sa ki cinye shi ko mayya "?. "Kallon Al'ameen Abni tai tana tambayarsa akan me mahaifiyarsa take cewa". Kafin yai wani yunkuri mami tace ubanki nace tsinanniya la'ananniya harda me nace da yake ya zama sako tumaki saiya fada miki jaka kawai". Cikin takaici Al'ameen yace wai mami me kikeyi haka haba dan Allah ki daina zagin ta ". Bazan daina ba kazo ka dake ni saboda na zagi wannan shedaniyar arniyar". Mami ki daina kafurta ta musulmace fa"?. "Au a haka shine ta sako wannan dan mitsitsin hijab din kila ma wanda take zuwa coci ne". Fahimtar da Abni tai kamar bata samu karbuwa agurin mami ba ganin yadda take magana da fada duk da batasan me take cewa ba yasa ta kalli Al'ameen ba tare da nuna wata damuwa ba tace" suje waje ko gardan suyi magana". A tsawace mami tace idan ka fita ka bita ban yafe maka ba saina tsine maka wallahi,". Iya rudewa yayi cikin yanayin ladabi Abni ta roki mami cewa ta kyale suyi magana amma mami tace ya fita ya gani". Dafe kansa Al'ameen yai jin lokacin guda yayi mugun sara masa da hanzari Abni ta karasa tana tambayarsa lafiya"?. Wata hankada mami ta mata wanda saida ta buge da kujera cikin tsawa tace fice daga nan idan ba gidan ubanki bane bakadaddiya karuwa wato a gaban nawa ma fayde zaki masa" Abni zatai magana mami ta sakar mata wani zazzafan marin dayasa ba shiri ta fita a palon da gudu tana kuka". Al'ameen dake numfashi dakyar muryarsa na rawa yace mami me kika aikata kin aibata kin zage ta kin mare ta me tai miki dan Allah mami meyasa kika tsani Abni ni kuma baki tsane niba domin nine ita itace ni kowa ya kita ya kini". "Ai kai yanzu na fahimci mahaukaci ne bakasan ciwon kanka ba idan ba mayya bace kalli mana kafin tazo kana irin wannan numfashin ne shashasha ana maka gata da yake idonka ya rufe baka gani". Barin gurin tai yayin da Al'ameen yake yunkurin tashi yabi bayan Abni ya kasa. Abni na zuwa hotel inda suka sauka ita da dad dinta tasha wani marin a gurinsa yana huci yace dole soyayya dashi kina neman kashe kanki ga samarin ki can ki zabi daya mana Abni ina kika kai tunanin ki,"?. Kuka Abni ta fashe dashi tana rungume mahaifin nata tace kayi hakuri dad Al'ameen na sona kada ka raba mu nima ina sonsa ba laifinsa bane". Cikin tausayawa daddyn ta ya rungume ta shima yana cewa shikenan naji yi shiru haka na gama komai a cikin kwana biyu saboda ke gobe zamu tafi". Zaro ido tai tana mikewa tsaye zatai magana ya girgiza mata kai yana cewa". "Bazan barki ki sake komawa wannan gidan ba kada ki batawa kanki lokaci Abni auren ki da yaron nan bamai yuwuwa bane". A rude tace dad zai yuwu dan Allah ka kara min lokaci zanji da komai"'. "Na sake baki lokaci amma wannan shine na karshe idan aka sake samun matsala bazan daga miki kafa ba". Murmushi tai eh dad thank you na yarda". Mrs Al'ameen Ahmad ce. Yma Dutse new world new life and new style sabuwar duniya NAJA'AT MUSA ABUBAKAR ZARAH MUSA 'DAN ADAN THIS PAGE IS FOR U I LV U EVERYTHING ABOUT YOU IS SO GOOD BUT ONE THING IS WRONG THAT YOU ARE NOT MIND. Page 05 to 06 Wani karamin kauye wanda yake cike da mutane iri daban daban wani gida ne daya sha fenti harta waje kamar yana cikin gari gidan yayi kyau sosai kana gani kasan me gidan nada abin hannu a kauyen. Wata mace ce ta fito daga daki tana rawa tayi daurin kwalin soke irin ture kaga tsiyarnan tace. "Ahayye nanaye yan gidan nan ku fito kuyi kallo Zainabu abu na me 'kashin arziki ce ba irin su o'o da ba'a da farcen susa ba". Jin shiru yasa tace Salamatu kina ina ne kodai bakin ciki ya kashe ki a daki lallai kina da aiki ". Fitowa wata farar mata tayi daga wani guri da hayaki ke fita wanda kana gani kasan dakin girki ne ta kalli waccan dake rike da atamfa tana cewa". "Akan me zanyi bakin ciki saboda Zainab ta samu atamfa kowa ai da nasa rabon Allah ne ya bata". Dariya Saude tai tana tafi tace tofa masu tawakkali kamar gaske kina magana a salihance nan kuwa zuciyar bakin kirin take"". Murmushi Salamatu tai an fada miki kowa irin ki ne ni abin wani bai dame niba Fatima bata rasa kaya ba". "Humm karyar banza kayan gida ba badan ubansu meyin suturar bane idan ta samari za a biye wata rana saidai ta fita yawo tsirara". Salamatu dake shirin komawa kitchen tace Allah ya kiyaye kedai tunda kinbi son zuciya ki taka a sannu ina gargadin ki". Kugu saude ta rike jimin munafikar mata koke kika samu duniya yarki tai farin jini haka sai kinci kudin samari". Sallama wata budurwa tai tana sauke fantekar dake kanta tace gaskiya nifa na gaji da wannan tallar ehe "'. Baki saude ta bude ke baki da hankali yi kasa da muryar ki kada salamatu taji tai min dariya dama yanzu ita da shegiyar yarta suka gama kukan bakin cikin atamfar da ilya ya kawo miki ". Dariya Abu tai lallai ahe bakin ciki zai kahe su dan wallahi yace saniyarsa ta haihu idan ina dan zai bani". Da sauri kamar wani zai rigata Saude tace kice kina so dan ubansa tunda bashi da hankali ki wanki gara "Ai dama taliyar murjin da kika dafa min yau shi kadai ya saye ta". Zaro ido saude tai sadaka yayi a dandalin". Baki Abu ta tabe a'a kawai yaji da manjan ya juye a cikin fantekar ya cinye shi kadai sai yar kadan daya bawa wani almajiri Saude tace kaji jakin mutum wannan kada ayi auren ya kasa rike ki mahaukaci ne shi zai cinye taliyar rabin kwano da kofin wake". Hade rai Abu tai nifa ina sonsa ki daina zagin sa yace min gobe zai turo iyayensa". Cikin murna Saude ta rafka guda tana cewa abin yazo yar albarka ta kusa tafiya daki bari muntarin ya shigo muyi magana". Mikewa Abu tai tana cewa nifa yunwa nake ji saude dake kirga makudan kudin da ilya ya baiwa Abun tace ki buda daki yana nan a langa". Kai Salamatu ta girgiza tana daga kitchen tana tuka tuwo tace Allah ya shirye ku kada wata rana kuci kudin matsafi". Kwanan Al'ameen goma baida lafiya gashi yana so ya koma gurin aikin sa amma babu dama dole ya hakura zuwa wani lokaci idan yaji ya dawo daidai". Daddy na zaune kusa da Al'ameen bayan Sadiq ya duba shi ya daura masa ledar ruwa cikin lallami yace. "Aminullahi meke damun ka Sadiq yace min har yanzu bugun zuciyar ka bai dawo daidai yadda yake ba ka fada min matsalarka". Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai domin maganar dazai fada ba lallai daddyn nasu ya amince ba yace. "Dan girman Allah daddy ka dube ni da idanun rahma ka tausayawa zuciya ta ka fahimcr cewa danka ya fada cikin jarabtar soyayya kamin maganin damuwa ta". "Me kenan zanyi maka Al'ameen ka fada min kada kaji shakka niba mami bane babu abinda zai gagara". "Daddy na roke ka ka duba Allah ka amince min na auri Abni yarinyar nan ta sadaukar da rayuwar ta saboda na samu farin ciki ta kula dani lokacin da bansan kowa ba a London. Ta musulunta saboda ni ta yarda zata aure ni ta zauna dani sannan mahaifanta basu nuna min kiyayya kamar yadda mami
Chapter 2 · 0% Book details