← Book details Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'DAN MILLIONAIRE YUSRAH MUSA ABUBAKAR Page 07 to 08 Iya tsananin damuwa Al'ameen ya shiga domin bai taba tunanin kiyayyar mami zata sa tace kila anyi mata canjinsa a asibiti lallai dole ya samu daddy koda son Abni zai kashe shi ya hakura". Fita yai daga part din nasa yana shiga bangaren daddy cikin sallama zaune ya same shi a palor yana duba takardu masu yawa zama yai a kasan carpet yana kallon daddy cikin dauriya dason ganin ya jure yace. "Daddy na fasa auren Abni na hakura basai kunje ba Allah zai musanya min da mafi alkhairin ta dama ba komai mutum keso ya samu ba". Batare da alhaji Mustapha ya dago daga kan aikin da yake ba yace " me kake cewa banji sosai ba hankali na ya kasu gida biyu". Sauke numfashi Al'ameen yai yana cewa daddy na hakura da auren Abni na fasa". Murmushi daddy yai yana dan kallonsa yace saboda Aisha ko "?. Shiru yai domin gaskiya badan mami ba babu abinda zai hana shi auren zabin ransa". Dawowa daga tunani yai jin daddyn na cewa" nace saboda mamin ku. Ka hakura ko"?' "Eh daddy domin mahaifiya ta tafi min komai mahimmanci tace duk cikin yaran ta nine batai sa'ar haihuwa ba ina wahalar da ita ni kuma banason saba mata na fasa auren amma bazan auri kowacce yarinya ba". "Ni kuma ban fasa ba Aminu ina nan akan bakana saina baka abinda kake so aure meye baya samarwa dan tana yar wata kasar saiya haramta ka aure ta ka kwantar da hankalinka idan yarinyar nan matar kace saika aure ta ba gida daya zaka zauna da mamin kaba balle kace kana can gurin ka daban". "Daddy na sani cewa tai idan na aure ta bata yafe min ba". "Zata yafe maka idan taga abinda auren ya kawo mata kaga bar bata wa kanka lokaci wajen tunani da damuwa ranar monday zamuje London babu fashi". Sauke ajiyar zuciya Al'ameen yai cikin tunanin ya zai kare da mami baya son hayaniya ko kadan. Washe gari suna zaune a palor mami ta fito daga part dinta tana waya ganin su a zaune yasa bayan ta gama tace. "Al'ameen kadau mota yanzu kaje airport ka taho da Zainab munyi waya da hajiya Binta tace min driven ta ba lafiya". Tun kafin Al'ameen yai magana Sadiq yace amma mami ga direbobi da yawa anan mezai hana daya yaje ya dauko ta yarme iyayi ta fito ta tari motar haya man a kaita gida". Cikin harararsa mami tace to uban yan shishshigi banyi dakai ba kaiba asibiti zakaje ba meye ya biyo dakai tanan gidan". "Mami nida gidan mahaifina kice meya kawo ni dan kawai aure yasa nabar gidan". Bata bashi amsa ba ta kalli Al'ameen tana cewa kaji dai na fada maka ko tana can tana jiranka"?. "Jiwai tana jiran ka kamar wani driven ta wato wannan yar iskar yarinyar hajiya Bintan ce ta dawo". Cikin yanayin tambaya Al'ameen yace wace ne yarinyar wai yar gidan umma kanwar mami dai ina take da yar dahar take fita waje". Daidai sun mike Sadiq yace kai amma Zainab wata yarinya me shegen tsiwa kodan ba a hannun hajiya Bintan ta girma ba tana dangin babanta amma kai da yar uwar ka". Shiru Al'ameen yai suna tafiya yana tunani amma gaskiya ya manta yarinyar saidai yanzu idan ya ganta. Tana tsaye tadau wankan riga da wando wanda sunyi bala'in matseta gashi tasa wani dan mayafi wanda dashi gara babu tana sanye da glass . Sadiq da yake shike driving yace kalli to gata can wani irin kallo Al'ameen ya bita dashi ganin shigar datai arniya sak ba wanda zaiyi tunanin yar musulmai ce. Tsaki yaja yana fita a motar daidai ta karaso ta zare glass din idonta tana kallon su sai kuma tadan murmusa cikin yanga tace Sadeeq ashe zan iya gane ka tsawon lokaci bamu hadu ba". "Eh shigo muje" abinda yace kenan domin shima shigar datai ta bashi haushi". Juyawa tai saitin da Al'ameen yake tsaye tace driver samin kaya a bayan mota kayi sauri nan, da minti biyar na ganni a gida". Zaro ido Sadiq yai ke driver fa kika ce ya miki kama da driver"?. Yatsina fuska Zainab tai mezai hana direbobin aiba kamace dasu ba". Kai Sadiq ya jinjina bai sake magana yace Al'ameen shigo mu wuce". Katseshi Zainab tai wai dan Allah Sadiq nice zansa kayan cikin mota shi meye amfanin sa". Banza Sadiq ya mata jin motar ta tashi tsoron karsu tafi su barta yasa dole tasa kayan da kanta sannan ta shiga motar". Sun danyi tafiya kadan tace gaskiya ne haka nake son driver babu sanya amma Sadiq ina wannan 'kanin naka mejin kannan naji umma na tace yanzu ya zama soja ko"?. Lallai yarinyar nan ba karamar yar iska bace Sadiq ya. Fada a ransa yana kallonta tta mudubin mota yace. "Ga miciji ai ba a neman ja ki tambaye shi da kanki". "Oh shine wannan sorry nace maka driver ya kake". Babu wanda ya kula ta zuwa wani lokaci tace yauwa na tuna shakka babu sunan ka Aminu na manda'ko "Dariya ce ta kama sadiq lalli Zainab taci kai amma bari ya kyale ta Al'ameen na daidai da ita". Cigaba tai ko shekarun baya na tuna ya tsani zuwa kauyen mahaifin ku wata rana zakuje ya fadi a kasa yana burgima shi bazai jeba daddyn ku ya ciro bulala a garden ya zane sh...........' Wani irin taka burki Al'ameen yai wanda saida ta gwaru da kujera a fusace yace "fita a motar nan". Zaro ido tai baka karaso ba ga gidan can dan kawai na fadi gaskiiya na tuna maka da baya"?. Cikin tsawa yace "get lost". Kallon Sadiq tai ko zai magana taga yayi banza ya dauke kansa daga saitin su dole ta fita daga cikin motar tana daukar kayan ta"". Wata irinn 'kura ya buleta da ita yaba bawa motar key tari ta kamayi sosai har saida idonta yai ja". Dakyar ta samu ta daaina barin kayan tai a gurin da sauri ta shiga gidan su tana zuwa ganin ummanta a palor yasa ta fada kanta tana kuka". Cikin tashin hankali hajiya Binta tace lafiya dota daga dawowa ina murnar ganin ki sai naga kina kuka meya faru ina su Al'ameen din kosun tafi". Cikin shagwaba tace ba shinee ya ajiye ni a wajen gidan alhaji Faruq ba kuma ya tule ni da ''kura a gaban mutane dan kawai nace masa ya karaso dani gida kayan nawa ma suna can". Cikin bacin rai hajiya Binta tace kan uba amma wallahi yaron nan baida mutunnci wato ya tule miin ke da 'kura bari zan kira auty Aishan na fada mata". Kayan hajiya. Binta tasa ma'aikatan gidan suka dauko mata sai bala'i take. Ita kadai. By mrs Al'ameen Ahmad ce. Page 09 to 10 Kamar yadda alhaji Mustapha ya fada haka ce ta faru ranar Monday sukai shiri suka wuce london Afeeya kuma tace gidan Sadiq zata zauna gurin matarshi kafin su dawo sai kuma ta fasa ta tafi gidan kanwar mami hajiya Binta idanuwan mami a kumbure sakamakon kwanan datai tana kuka kamar ranta zai fita. Da yake Al'ameen yasan gidan kuma saboda kada a samu matsala yasa bai sanar dasu ba Saira kanwar Abni na zaune a tafkeken palon su sai ganin mutane tai cikin mamaki ta mike tana cewa bros kaine sannu da zuwa". Dan murmushi Al'ameen yai tuna rayuwar da sukai lokacin yana nan cikin yan mintuna tasa aka hada musu kayayyakin ci dana sha na alfarma". Fafur mami taki shan koda ruwa ne zama ma dan ba yadda zatai ne amma yadda take jin tsanar mutanen nan da wuta zata kone gidan sai tafi kowa farin ciki". Tambayar Saira yai ina mom domin yasan Abni da daddyn suna gurin aiki. Sauyawa fuskar Saira tai daga yar walwalar da take zuwa damuwa tace" mom na asibiti bata zama a gida". Waye baida lafiya "? Ya tambaye ta cikin faduwar gaba. Kuka ne ya kwace mata tana girgiza kai tace" Abni ce ". Wata ba'kar hajijiya ce yaji ta kwashe shi lokaci guda idonsa ya rufe luuuu ya tafi zai fadi da sauri Saira zata tare shi mami ta ture ta tana cewa. "Karki taba shi arniyar banz...... "AISHA" daddy ya fada da karfi cikin fushi yace wato kinzo gidan su ma saikin nuna rashin arziki ko kinga ki kiyaye ni ". Jijjiga mami keyi tana huci yayin da Saira taja baya daga gareta Sosai cikin jin tsoro". Da murya a nutse daddy yace" kinga Saira karki damu muje ki kaimu asibitin". Kai ta jinjina tana shiga ta shiryo tare da dauko key din motarta ta fito suka wuce". Dukda su mom suna cikin damuwar rashin lafiyar Abni din hakan bai hana su nuna matukar farin cikin su da ganin familyn Al'ameen din ba kuma sun karbe su hannu biyu". Tambayar inda take Al'ameen yai cikin damuwa mom tace " son Abni tana ICU". "Mom muje na ganta". Kai mom ta girgiza babu dama muma basa bari mu shiga balle mu ganta saidai ta na'ura". Tabe baki mami tai tana dauke kai daga kallon su domin ko ganin su bata son yi". Haka suka zauna har dare a asibtin ganin lokaci zai kure yasa mom tace Saira kuje gida ki basu masauki gobe sa dawo". "Ok mom" Saira tace sannan ta dauko su a mota suka dawo gida a ranar Al'ameen bai runtsa ba ko kadan kwana yai akan Sallaya har asuba yana rokon Allah". Kwanansu uku da zuwa iya gajiya da bacin rai mami tayi bata da buri kamar taga ta dawo gida gashi basa zance tahowa". Samun alhaji Mustapha tai ranta a hade tace waini sai yaushe zamu koma gida ne kawai munzo garin mutane mun zauna". Ko karasa kallonta alhaji Mustapha baiyi ba yace sai ranar data warke idan bazaki iya jira ba ga hanya nan". "Gaskiya bazan jira saita warke ba kamar wasu dangina tafiya zanyi saikun taho". "Ki gaida gida Allah ya kiyaye amma ki sani bada kudina zaki koma ba ki biya da naki". Zaro ido mami tai dan akwaita dason kudi kamar me tace" haba alhaji da kudi na kuma dama nice na kawo kaina". "Oh da wa ya kawo ki gurin
Chapter 4 · 0% Book details