Sashe 6
Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
zakuyi ba dawo wa zatai ba". Kai Afeeyah ta girgiza batare data sake magana ba Zainab ce tai sallama da dumemen akwatin ta bayan ta driven gidan sune daya kawo ta dauke da wani akwatin. Cikin mamaki Afeeyah ke kallonta yayin da mami ta washe baki cikin murna tace tun shekaran jiya da Binta ta kira ni tace zaki zo kimin kwana biyu nake zuba ido saiyau sannu da zuwa". "Yauwa mami ina kwana Zainab tace tana zama kujeran dake facing din Afeeyah a fakaice ta nuna Afeeyah da yatsa tana maganar kurame". Tsaki Afeeyah taja cikin tsanarta ta mike zata bar gurin mami tace ke Afeeyah ja akwatunan nan ki kai mata su part din ki acan zata zauna cikin daya daga bedroom din part din". Matukar takaici ne ya kama afeeyah har bata san sanda hawaye ya zubo afuskarta ba amma ta goge tana rike hannun akwatin ta wuce kamar yadda mami ta umarce ta". Zaunar da Zainab mami tai tana cewa kinsan me yasa nace ki dawo gidan nan da zama "?. Kai Zainab ta girgiza mami taci gaba babu komai zan fada miki ba yanzu ba wani aiki zaki min". Daidai Afeeyah ta dawo tadau dayan akwatin Zainab tace hay madam kidan hada min ruwan wanka no hot no cool". Cikin bacin rai Afeeyah ta juyo muryarta da fushi tace ko kinfi uwarki kokari baza ki samu abinda kike so ba ni ba sa'arki bace nafi karfin yi dake jaka kawai". Zanci uban ki fa Afeeyah jimin shashashar yarinya". Mami ta fada tare da kallon Zainab tace rabu da ita dama fushi take bari zansa a hada miki yanzu". Afeeyah na shiga bedroom dinta ta fada kan gado tana fashewa da kuka tace" ya Allah kaine ka fimu son Abni ka karbi kayar ka kayi mana canji da mafi alkhairin ta ka tausayawa dan uwana ka bashi mace ta gari me share hawayen mijinta". Hayaniya ce sosai ke tashi da shewar mata a gidan su Abu domin anzo nemawa ilya aurenta. Lami makwafciyar su dake duba kayan da komai kala bibiyu ne ta rafka gud'a kamar zata cire hancinta tace. "Kai masha Allahu Allah yasa Jamila ta tayi 'kashin arziki kamar Abun ki Saude ni ina Salamatu ne". Saude dake rausaya kai irin uwar 'yar nan tace wai ta tafi gidan su tun safe munafika". Aliya ta amshe da cewa ba wani bakin ciki take saboda 'yarta zatai kwantai tunda dame Abun ta fita yan watanni ne". Gadoji tace humm aiko bakin ciki zai kashe ta don tunda nake ban taba ji ance ga wani yana san fatin taba inaga bakin jinin daga sune". Mukam biki zamusha mu gwangwaje matsalle me kalangu zamu gayyato yazo ya buga mana gangar cahiya Laraba tace ni kuma hankalina be kwanta da fitar Salamatun nan kar muje munna nan mun bude baki da hanci tana can tana gunbudowa Abuwa asiri". Zaro ido Saude tai tana dafe kirji tace Allah ko 'kawata har kinsa naji nima nawa hankalin ya tashi". Tsomo baki tabawa tai to meye muma sai mu tashi tsaye ko taki ko taso aure sai Abu nada 'ya'ya Fatima bata samu mashinshini ba ehe "Kunga mubar wannan maganar bari na duba mana jalaf din shinkafar kota nuna muci" cewar Saude tana mikewa. Lami na ganin Saude ta wuce kitchen ta rike baki cikin munafirci tace" jama'a yau nake ganin wani ikon Allah mutuwar zuciya ta 'kare a dangin su ilyasu kalli wai komai biyu". Tabawa na kallon kofar kitchen tace hum abinda yake cin raina kenan yar uwa kika riga ni furtawa mutum da hankalinsa bazai kai yarsa wannan gidan ba". Gadoji tace nima sheda ce ina marsida yar gidan Bala sai daga gida ake kai mata abinci mijin ya kasa riketa kuma ai kinsan mijin nata Sado (Sa'idu) dakin su daya da ilyan". Laraba tace mukam ai taushe zamu zo mu kwasa ina ruwan mu dama irin su abuh ai sai ana basu tantirai kuma nasan zataci ubanta a gurin Halima domin ita bata zama lafiya da surukai". Aliyah tace yo matar da ko naman miya ne sai a gaban ta ake rabawaa dan kar a cuceta duk cefanen da yayanta zasuyowa matan su saita burkice kowacce leda idan kaje kasuwa baka biyo ta dakin taba kuna zaune zata fado muku daki ba sallama Lami dake dariya tace kice Saude abar hankata baki Abuh karamar bazawara za ai sakin uwar miji ba sakin wawa ba". Duk gurin dariya suka kaure daidai Saude ta fito da katon tire fal da abinci ta ajiye tana cewa dariyar me kuke"?.. Lami tace dariyar farin ciki kawata sai aurar da yaran mu muke asirin mu a rufe tuna hakan ne ya samu dariya". "Wallahi kuwa lami ai abin da dadi zuma da madara muci kartai sanyi dan nasa mana kitse a ciki . Hummm ayya Saude kin 'baro