← Book details Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kyauta Saddiqu ina iyalin taka ne Ri'kayye ko tana gida nasan da daita kuka zo da yanzu ta karaso" Cikin mazu Sadiq yace bansan wata Rikayye ba idan mata na kike nufi sunanta Ru'kayyah". "Ita nake nufi mana saboda bakin ciki shine ka 'ki zuwa da ita". Batare da Al'amin ya dago ba yace hajiya meye abin bakin cikin dan kawai baizo da ita ba"?. Hajiya data balli goro tace kai kuma kamin shiru ba dakai nake ba tuzurun banza kalleka kato dakai idan anan ne kana da 'ya'ya wajen biyar". "Ai hajiya daina fada 'ya'ya biyar sai kace na hada dangi da kaji uku ma sun isheni shiyasa bazanyi aure da wuri ba". "Ashsha kayi ta banza bari ai Mustaphan zaizo ya same ni zanji idan shine ma yake karanta maka kada kayi auren da wuri saiya bani amsa". Page 17 to 18. Basu bar gidan hajiya ba sai bayan sallar isha a kofar gida saman dakalin Al'ameen ya zauna sa'banin sadiq daya shiga cikin gida". Yana nan a zaune Sa'adu yazo yasha wanka ya sako gwanjola irin takalmi sau ciki na roba"'. Kallon sa Al'ameen yai tun daga kai har kafafu lokaci guda murmushi ya 'kwace masa ganin sai wani buda kafada yake". Fati ce ta fito tana nufar inda yake tsaye wanda ko minti biyu basuyi ba Abuh ta karaso gurin da 'kawayenta tana haki tace". "Amma Sa'adu me nace maka ba nace kada ka sake zuwa gurin Fati ba nice nake sonka ba ka amince rannan a dandali ba saboda kai mun rabu da ilya". Shiru Sa'adu yai cikin takaici Fati tace wai dan Allah Abu meye hakan me na tare miki da bakya son gani na cikin farin ciki"?. A gadarance Abu tace ban sani ba bani da lokacin ki kai kuma muje ". Kamar rakumi haka Sa'adu yabi Abu zuwa dandali kamar yadda ta bukata 'kawayen Abu na yiwa Fati dariya da habaici suka bar gurin". Wasu zafafan hawaye ne suke zuba a idanuwan Fati gashi gobe ne gasar nuna samari yanzu ita ya zatai da rayuwar ta cikin takaici ta juya zata shiga gida". Al'ameen dake kallon ta yace " madam ji mana ". A firgice Fati ta kalli inda yake tana goge hawayen fuskarta" Jitai yace mene sunan ki"?. Muryarta na rawa sakamakon kukan da take tace suna na Fatima". "Ok yayi jeki" kawai yace yana mayar da hankalin sa kan waya wucewa tai ta shiga gida. Cikin shishshigi da cusa kai Saude ta shiga dakin da mami suke tana cewa Aisha a karo muku abincin ne". "A'a ya isa haka mun gode". "To shikenan bari na kawo miki wata kyakkyawar fura ko zaki sha". Fita tai tana daukowa ta kawo mata sannan ta musu saida safe ta fice tsaki mami taja tana rakata da harara tace ko ina ruwanta dani mayya bazan sha ba aikin banza kawai". 'Yar dariya Afeeyah tai tana gyara kwanciyar ta yayin da mami take ta maganganu da fada ita kada kadai. "kawai an kawo mutum wannan mugun kauyen an ajiye duk zafi babu wata ni'ima ko jin dadi ba a.c haba wallahi bazai yiwu ba dole gobe na samu alhaji idan shi bazai koma gida nikam na gaji zan tafi". Shiru kawai Afeeyah tai tana sauraron mami da mamakin furucin ta amma batai magana ba saboda gudun abinda mamin zata ce mata saidai bata jin dadin yadda take kushe 'kauyen mahaifin nata domin itama tana son garin ". Washe gari Al'ameen bai tashi bacci da wuri ba har rana tai saida Sadiq ya tashe shi yana mikewa ya rike kansa tare da cewa. "Subahanallahi wannan karar haka kamar zata fasa min kunne kuma daga ina me suke". Sadiq dake shirin fita yace bazan jira kaba domin an fara wai wani biki suke na nuna samari" yana fadin haka ya fice. Shiru Al'ameen yai kamar kuma an tsikare shi ya mike cikin gaggawa yai wanka ya shirya yana fita yaga Salamatu ta fito daga daki. Bayan sun gaisa yace ina Zarah". Cikin mamaki tace wace haka"?. Tunawa yai sai kuma yace oh Fati nake nufi tana nan". "A'a wallahi bata nan ta dade da fita ban sani ba ko tana gurin bikin wasan samarin can nasu da suke". "Ok" yace yana fita daga gidan harya kusa zuwa yaji kid'an na hawa kansa domin makad'a ne da yawa da maroka na gari da gari suke taruwa su zo". Juyawa yai ya fasa zuwa hango wasu gajerun bishiya masu ni'imtacciyar inuwa yasa ya nufi gurin dan yadan huta". Yana karasawa yaji ana shashshekar kuka cikin mamaki ya soma dube dube can ya hango me kukan zaune ta kifa kanta". Har zai rabu da ita sai kuma ya tuna duk wanda ya sharewa wani hawayen sa Allah zai share masa shima". Tunani ya farayi to me zaice mata zuwa wani lokaci da yaga bashi da mafita yai gyaran murya". Da sauri ta dago a razane wanda shi yana mamakin ganinta a gurin ita ma tana mamakin ganin sa". "Kukan me kike"?. Shine tambayar dayai mata kaita girgiza tana cewa" ina kuka ne saboda dazan aje abin fada zanyi abin kunya yau ranar fitar da gwani ne a dandali". "Kamar ya"? Me kuke yi idan kunje"?. Gyara zama tai tana cewa da farko idan kowa yaje me kira zai rika kiran suna mutum da budurwar shi su fita fili ya bata kyautar zobe da agwagi guda uku shikenan sai su fita wasu su shigo. To kowa ya sheda ya gani wace nada saurayi kuma baza a kada mata kalangun tayi kwantai ba idan kuma baka da saurayi kowa saiya sani ayi ta maka dariya". "Toke yanzu bakije ba kina nan idan aka kira sunan kifa kisa saurayin naki ya rude". "Ni bazan je ba". "Saboda me"?' "Idan naje ma babu amfani wazan nuna wanda yake sona yayata Abu tamin 'kwacen sa bani da kowa". "Zaki are ni"?. Cikin rashin fahimta tace aron me". Basarwa yai tare da cewa muje na ga abinda kuke yi a bikin. Badon taso ba jikinta a sanyaye ta mike suka tafi dandalin shake yake sosai da mutane suna zuwa sai zance da yamud'id'i da munafirci ake ana ta kallon Al'ameen'. Me shela ne ke cewa anzo gidan. Muntari na alhaji attajirin yan kauyen nan me taimako muntari gwani me 'kwazo ina babbar 'yarsa Abu ta fito mana fili da nata gwanin". Fita Abu tai tana hura hanci yayin da Sa'adu ya fito ya tsaya a gefen ta yana cire zobe ya bata sannan ya bata agwagi guda biyar. Lallai su Saude za a sha dafgen nama Suna fita me hela ya sake rafka cikiya ina 'yar uwarta Fatima ta fito fili da nata gwanin itama". Jikin Fati tai yadau rawa cikin nadama da dana sanin inama bata zo gurin ba . Kaurewa akai da surutu kowa da abinda yake fada wasu na mata dariya wasu na tausaya mata". Ina Fatima ne ko mu buga miki gangar bandaro me kwantai" maroki ya fada yana le'ke -le'ken inda zai hangota". "Ehhhh kawai a kad'a mata mu cashe " guri ya kaure ehhh a buga ehhh a buga. Al'ameen da abin ya bashi dariya shiga cikin filin yai yana murmushi yaiwa me hela magana". "Heeee a saurara jama'a ina mewa Fatima dariya ? To ka rufe bakin ka ina maison jin jarumin Fatima? To bude kunnen ka dakyau ina mai nuna Fatima da yatsa ? To ka sauke hannunka ina me son ganin gwanin Fatima ya matso kusa ya bude idonsa yai kallo inji wannan zankadedan saurayin yace shine saurayin Fatima"' Me hela ya fada tsit guri yai kamar sun mutu kowa idonsa nakan Al'ameen wasu suce ba mutum bace aljani ne wasu suce daga ina ta samo wannan. Fitowa filin Fati tai tana mamaki kare tan da Al'ameen yai a haka idan ka kalleshi zakai tunanin zaiyi girman kai. Kudi masu yawa Al'ameen ya baiwa marokan da makadan wanda me hela da lasafika a susuce ganin kudin da baiyi zato ba yace. "A saurara Fatima me 'kashin arziki ce tafi karfin kaji koda na turai ne balle agwagi masu wuni a cikin kwata "Sannan ku kalli zoben daya bata na gwal ne babu wacce ta samu koda na azurfa dan haka dole yau a yabe ta itace ta cinye gasa a wannan shekarar musbahu ku bamu sauti". Kid'a da algaitu ne ke tashi kamar gidan sarki suna kuma yabon Fati da mata kirari suna kod'ata sun samu kudi sosai a gurin Al'ameen saida ya tabbatar daya wanke Fati tas daga jin kunya". Abuh na komawa gida taje ta fadawa Saude abinda ya faru tsaki Saude tai to saime inace ba saurayin nata bane idan ya tafi shikenan ta fito rana karki wani ma damu kanki". Da salon munafirci Saude taje ta karancewa mami komai harda abinda ba'ai ba saida tai 'kari. Mami kam bata juri zuga ba tuni ta cika tayi fam waya ta dauka tana danna masa kira yana dagawa tace duk inda kake kome kake kazo yanzu ina son ganin ka". Yana zuwa ta balbale shi da masifa Al'ameen kana hauka ne? Akan me zakaje ka 'barnatar da kudin ka saboda ka kare wata banzar yarinya". Tun kafin yai magana Afeeyah tace kai mami kamar ya banzar yarinya yar uwar sace fa kuma koba haka ba duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi". "Ke kuma rufe min baki bake nake tambaya ba dakai nake". "Gashinan ta fada miki mami duk wanda ya taimaki wanI Allah zai taimake shi"'. "Hummm shiyasa kaje ka zubar da ajinka a gurin yan kauye a gaban mutane sama da kirge wai yaushe ka lalace da shashanci haka ne". "Mami ki fahimta yarinyar nan sister nace fa yar uwa tace jinina ce da ita da Afeeyah duk daya ne". "A wajen ka sakarai ba wacce kuke uwa daya uba daya da wacce kuka hada kakanni saboda mutuwar zuciya kace daya suke". "Maamii gaskiya maganar sa koni Fatiman nan tana burge ni wallahi amma komai mami idan ba kece kika zabe shiba baiyi miki ba " Afeeyah ta fada da yanayin damuwa". "Ke dalla 'kyale ni yar iyawa gwana saina fadi abinda ke raina ". Mikewa Al'ameen yai yana cewa good night mami". Ya fita daga murya tai yadda zai jiyota
Chapter 8 · 0% Book details