← Book details Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka nake son ji Allah ya miki albarka ya had'a ki da abinda zai zamo alkairi a rayuwarki". "Ameen umma nagode da addu'arki da kyakkyawan fatan ki gareni" Fati ta fada cikin jin dadi. Page 37 to 38 Bayan wata d'aya Mami na zaune a daki ta zuba uban tagumi naban tausayi ta rame tayi duhu saboda damuwa da rashin kwanciyar hankali. Sallama wata mace tai tana cire nikaf din fuskarta ta zauna kusa da mami tana kallon ta tace . "Haba Aisha kina rage yawan wannan tunanin da kike saikin dorawa kanki hawan jini garin wanke biyar a 'bata goma". Numfashi me zafi mami ta fitar tana kallon 'kawar ta tace "humm Halima hawan jini kuma na nawa zai hauni saidai nasha magani taya damuwa ta zata kare alhaji ya'ki karbar bada hakuri na". "Aisha kina ji ki kwantar da hankalinki Mustapha mutun ne me hakuri may be bango kika kaishi yadau zafi dake haka amma idan ya huce komai zai dawo daidai". Jiki a, sanyaye mami tace "yanzu ba wannan ba da kikaje ya kukai dashi kinga alamar ya fara saukowa daga fushin da yake dani"?. Kai Halima ta girgiza tace ""gaskiya ko fuskar da zamuyi maganar arziki ban samu ba karshe ma securities ne yasa suka fitar dani daga office din a wulakance kamar wacce naje maula". "Amma nashiga uku Halima indai alhaji bai hakuri ya mayar dani ba banajin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare dashi ba domin ina sonsa". Gyara zama Halima tai "a'a karki ce haka ki sa a ranki zai hakura ya mayar dake amma dan Allah ki rage yawan damuwar nan zan sake komawa gurinsa nan da kwana biyu". "Shikenan Halima na gode Allah ya saka miki da alkairi gaskiya ke 'kawa ta gari ce". Daddy kam iya bango mami ta kaishi yama rufe babinta a rayuwarshi ya manta da wanzuwarta balle yai tunanin dawo da ita gidansa aiyukan sa kawai yasa gaba. Wannan hakan dayai na nuna halin ko'in kula ba karamin tsorata mami yai ba ya firgita mata kwakwalwa ya ruda mata tunani ya juyar mata da hankalinta". Har ciwo ya kama ta an kaita asibiti Sadiq na kula da ita sosai haka Al'ameen da Afeeyah kullum suna gurinta domin duk lalacewar uwa uwace. Sunyi matukar damuwa da ciwonta daddy ya sani amma yayi banza ya nuna ko a jikinsa ita yanzu ba matarsa bace bata da wani nauyi akansa. Haka ta 'karaci jinyarta ta shafe satika harta warke baiko le'ka asibitin da sunan ya dubata ba tayi kukan nadama da dana sani harta gaji. Ganin halin da take ciki da yake mahaifinta mutum ne me hikima dattijon kirki me aiki da hankali da tunani ya kira daddy har gida. Dole daddy yazo saboda yana matukar girmama tsohon yana ganin darajarsa cikin dabara da basira baba Ibrahim ya tarbi daddy da magana me dad'i. Cikin fara'a dason gyara musu al'amarinsu ya soma tambayar daddy da kuma lafazi me kyau yake bashi hakuri da nuna bacin ransa akan halayyar mami. Sannan ya kira ta yai mugun sa'ba mata ya kuma ce lallai ta aikata babban zunubi ta bawa daddy hakuri. "Dama abinda take nema kenan wata silar daidaituwar su tazo dan haka da taga ta samu dama haka ta dage da kukanta sosai ta rika bashi hakuri da rantsuwar baza ta 'kara ba. Saboda kunyar baba Ibrahim daddy ya karbi daba hakuri domin badan darajar saba shida Aisha saidai idan zance ya tashi tace da ta aure shi. A ranar saboda zumudi mami taso binsa ta koma yace a'a sai satin sama zai turo driver yazo ya dauketa bataso hakan ba amma zuciyarta mamaye take da farin ciki. Satin nan jinsa take kamar shekara ko baccin kirki batayi saidai tunanin daddy da mafarki komawa gidansa. Lalle da kitso mekyau taje aka tsara mata tai fes da ita tasha sabon dandakeken dinki tayi kwalliya fada sosai baba Ibrahim ya sake mata sannan ta fito 'kawayenta biyu zasu rakata. Halima da hajiya Maryama sai tsiya suke mata a mota har suka je gidan zama sukai saida daddy ya shigo sannan suka tafi. Suna fita mami ta diro daga kan gado tana durkusawa a gaban daddy dake tsaye tare da rike kafafunsa hawaye na zuba a idonta ta soma magana. "Alhaji dan girman Allah ka yafe min abinda nai maka nasan kayi hakuri da halina ina rokon ka kada ka gajiya nayi kuskure amma yanzu zan gyara ka yafe ni". Daddy baiyi magana ba sai kallonta da yake ganin irin kallon da yake mata kuma bai tanka ba taci gaba domin tana son goge laifinta". "Alhaji ka bani dama a karo na karshe ni kuma nayi maka alkawari zan gyara abubuwan dana 'bata maka fushinka a kaina barazana ce ga rayuwata ka yarda dani wallahi ina sonka kuma ina son ahlin ka na tuba kayi hakuri dan Allah". Ta karasa maganar tana fashewa da kuka ganin har lokacin kallonta yake kila bai gamsu da abinda tace masa ba'. Allah sarki zuciyar musulunci d'agota daddy yai daga durkushen da take saboda kada kafafunta suyi ciwo yana mikar da ita tsaye ya goge mata hawayen Muryarsa a daidai yace "shikenan Aisha ya wuce Allah ya yafe mana baki daya". 39 to 40 Washe gari da safe suna zaune a palor Afeeyah ta fito da saurinta suna gaisawa tai hanyar fita. Mami data bita da kallon yaushe rabo tace "Wai Afeeyah baki ganni bane ina zuwa haka? maimakon ki zauna mu wuni". "Dan juyowa Afeeyah tai tana cewa "am mami kiyi hakuri saina dawo sauri nake domin mun fara jarrabawa". "Ok shikenan to saikin dawo Allah ya bada sa'a". "Amin Afeeyah tace tana fita. Al'ameen dake kusa da Sadiq cikin tsokana yace" ni kuwa daddy ya batun auntyn nawa naji shiru har yanzu"?. Cikin mamaki daddy yace "wacce irin aunty kuma kake nufi"?. Kamar gaske Al'ameen ya gyara zama yana cewa "daddy aunty na mana dama gurinta zakaje ran nan amma bakace nazo nai maka rakiya ba"'. Da sabon mamaki daddy ke kallonshi amma ganin yana kallon mami yasa ya fahimci tsokanar mamin yake. Dan murmushi daddy yai yana mazewa kamar gaske yace" ayya sorry sorry Aminullahi auntyn ka tana lafiya ko jiya da mukai waya da ita tace na gaishe mata da autan ta". Baki Sadiq ya bude yana kallonsu Al'ameen yaci gaba "daddy yaushe ne auren fatan an kusa domin nine zan mana anko mami wanne kallar atamfa ko less kike so"'. Mami dake kallon Al'ameen jin shine me maganar a kara mata kishiya dukda tasan laifin tane itace tai sake jitai hawaye zasu zubo mata da sauri ta mayar dasu tana mikewa tabar palaon. Daddy dahar lokacin yake murmushi yace "wato Al'ameen ashe kaima 'kafar baya ne ? gashi kasa maminka kishinta ya motsa zatai kuka". "To ai daddy dama nasan haka zata faru kishin nata nake son gani dama manya ma suna kishi akan tsohon mijins............. Rufe baki yai yana kallon daddy yace "sorry daddy ina nufin soyayya tsohuwar zuma tafi". Kai daddy ya girgiza yana mikewa zai fita yace "Allah ya shirya min kai auta na nabiye maka kasa mata ta kuka". Daddy na fita Sadiq kamar ana tsikarin shi yace" kai daddy dama aure zaiyi ban sani ba a ina ya samu lady"?. Dariya ce ta kama Al'ameen yace "wato kaima kayi zaton da gaske ne ba wata lady dazai aura kawai shiri nane mami nake tsokana"'. Sadiq yace "koda naji nidai nayi mamaki yanzu dai muje kamin rakiya yau tunda kana hutu" mikewa yai suka fita'. Da dare lokacin da daddy ya dawo ganin Afeeyah a palor ya tambayeta. "Daughter ina maminki"?. Dagowa Afeeyah tai tana cewa "sannu da zuwa daddy mami tana part dinta batajin dadi zazzabi ke damunta". "Ok bari muga" wucewa yai zuwa part dinta kwance ya sameta lullube da bargo yaye mata rufin yai yana kunna hasken dakin yace " Aisha". Bude ido mami tai ganin dady tsaye yasa ta tashi zaune tana jingina bayanta da fuskar gadon. Cikin alamar tambaya daddy yace "baki da lafiya"?. Muryar mami na rawa cike da damuwa da tsananin kishi tace "alhaji da gaske ne abinda kunnuwa na sukaji dazu da safe aure zaka kara"?. Kallonta daddy keyi haba yasan zafin kishin mami a kansa tun kafin ya aureta". Mami da zuciyarta tai mata nauyi tace "alhaji kaban lokaci na gyara kuskure na idan kayo aure a wannan halin da muke ciki komai cakude min zaiyi dan Allah karka min kishiya". "Aisha wai waye ya fada miki aure zan karo Al'ameen tsokanarki kawai yake amma ni banida ra'ayin zama da mata biyu karki damu komai ya wuce". Sauke ajiyar zuciya mami tai tana cewa "amma sai naci 'kaniyar Al'ameen wato kakarsa ya mayar dani "A'a karki taba min auta na babu ruwanki dashi idan ba haka ba muhau sama mu fad'o". Dariya mami tai tana cewa "shikenan tunda abin son kaine". Dan shiru tai kamar mai tunani zuwa can tace "alhaji gobe zanje garin ku". Da mamaki sosai a fuskarsa yace" wai kina nufin kauye na"?. "Eh ina son na gyara mu'amala ta da kowa sannan yarinyar nan Fatima nadau hakkinta zan bata hakuri kuma na taho da ita ta dawo dakin mijinta ta haihu". "Dakyau Aisha kin kyauta kuma naji dadi na gode idan kinje da kwana biyu zamu biyo bayanki". Kai mami ta jinjina tace "ina son atamfofi da kayan abinci na tafi dasu". "Ok yayi zansa a kawo miki komai da kike bukata". Page 41 to 42. Washe gari haka mami tai sammako kamar kasar zata bari dan zumudi ba daddy ba hatta su Afeeyah mamaki ne ya kamasu. Lokaci da mami taje Fati ta fara nema amma bata gidan taje wuni gidan kakannin ta na uwa. Data dawo Salamatu ta sanar da ita mami na nemanta mamaki ne ya kamata amma tai burus bataje ba domin babu abinda zatai mata ko tace mata. Kwanan mami biyu tana bin Fati tazo zasui magana amma harsu daddy suka zo garin Fati bata yarda sun hadu ba". Gidan hajiya ma ta koma da zama gabadaya saboda bata son ganin mami. Da kuka mami ta fadawa daddy Fati ta'ki sauraronta kwantar mata da hankali yai ta hanyar cewa zata hakura saita huce. Su Sadiq na gidan hajiya sai
Chapter 18 · 0% Book details