Sashe 16
Dan Millionaire Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abin cutar da ita zaiyi zata ci please Al'ameen dan Allah ka fada min gaskiya kodai kaine ka zuba mata"?. "Haba Sadiq akan me zan bata guba taci dan kawai bana sonta kka yarda itace tasa abarta da kanta". Sadiq yace taya kenan wanne tabbaci kake dashi ko ka ganta lokacin data zuba din"?. "Kwarai ina tsaye a kofar falo ta zuba data juyo ta ganni kasan me tace min"?. Kai Sadiq ya girgiza. Al'ameen yaci gaba "wai sai tace ga abinci ta gama shirya min dama danni ta shiga kitchen da kanta ta dafa shI saboda ni". "dana tambayeta me ta saka a cikin abincin sai tace babu da tana da gaskiya da nace taci sai taci amma jikinta yana rawa taso guduwa". "Ni kuma na riketa na dura mata spoon biyar kaga nine take shirin kashewa dan haka bazan mata uziri ba"'. Kai Sadiq ya jinjina lallai tayi kuskure amma kasan mami baza ta yarda ba "?. "Na sani". Sadiq yace to kaje ka dubata kafin ka wuce". Mikewa Al'ameen yai yanaa kallon Sadiq yace "Bana bukatar ganinta Sadiq ni dama gurinka nazo muyi sallama dan haka na tafi". Mikewa shima Sadiq din yai yana cewa to Fatin kuma fa bakace batajin dadi ba"?. "Eh Afeeyah tana gurinta". "Ok muje na maka rakiya Allah ya kiyaye saika dawo". "Amin Sadiq dan Allah lokaci zuwa lokaci ka rika zuwa kana duba Zarah". "Ok ba damuwa daddyn baby za'ai yadda kace" fita sukai ya masa rakiya sannan ya dawo". Mami data koma gida haka takai karar Al'ameen gurin daddy domin ita batasan ma baya gari ba. "Yanzu alhaji tsakani da allah abinda Al'ameen yake ya kyauta kenan ka duba yarinyar Zainab ba ta da lafiya kullum ina asibitin amma bai taba lekowa ya duba jikin taba". Wani kallo Alhaji Mustapha ya mata domin yasan komai tun ranar da abun ya faru Al'ameen ya kirashi ya sanar dashi. Ganin irin kallon da yake mata kuma bai tanka zancenta ba taji gaba. "Gaskiya alhaji kanada abin mamaki nace maka ga abinda ya aikata amma saikai burus dani, kana min wannan kallon kamar zaka dake ni saboda na tabo dan lelenka kodan bakason a fadi laifinsa tunda lu'u lu'un zuciyar kane"?.. "Aisha to me kikeso nace meye nawa a ciki kece silar gurbacewar komai kuma laifin kine tunda ke kika 'kulla komai ni babu ruwana a cikin wannan al'amarin". "Abinda zaka ce kenan alhaji a tunani na zakai masa fada ka nuna fushinka ai Zainab dince ta dace dashi shiyasa na dage ya aureta domin auren 'kwarya tabi 'kwarya na musu". Kai daddy ya jinjina yace" to dakyau ai kinyi musu ga sakamako nan na biyo baya kiyi addu'a abin ya tsaya iya haka". Mikewa yai zaibar gurin da gudu mami tasha gabansa tana huci tace" wallahi alhaji nagaji bazan yarda ba domin yanzu kam na gane kaine ke shiga tsakaninsu ka hana su zaman lafiya duk wata kitimurmura da fitina kaine kake shiryata". Cikin tsananun mamaki daddy ke kallon tsaurin idon mami dake fada masa duk abinda yazo bakinta". Ganin tana shirin sake magana ya daka mata tsawa wanda a firgice ta matsa daga gabansa domin iya tsahon rayuwarta dashi bai taba mata tsawa ba saiyau". Cikin bacin rai ya nunata da yatsa yana cewa" babu shakka Aisha yau kin sake tabbatar min da baki da tunani kuma kinsamu gushewar hankali kamar ki ace har yar bakida hankali kinyi asara bari kiji bazan dau wannan shashancin naki ba ina mai baki shawara ki gyara bar ganin mun dau shekaru tare ga zuri'a hakan bazai hana idan kinyi ba daidai ba nadau mataki a kanki". Mami datai tsalle ta koma gefe guda tun sanda ya mata tsawa jin abinda yake cewa yasa ta dafe kirji tana kallon wani irin bacin rai a fuskarsa wanda bata taba gani ba tace. "Wayyo Allah ni Aisha wannan wacce irin kaddara ce ta sameni alhaji da muna zaune lafiya tun daga lokacin da Al'ameen yazo da bidi'ar sa ya nuna yana son auren baturiyar nan alhaji ka fara juya min baya". "Amma banyi dace ba haihuwar Al'ameen batai min rana ba nayi asarar haihuw...'..... Katse ta daddy yai jin tana neman dorawa Al'ameen alkaba'i yace "Aisha idan kika karasa yau saina baki mamaki dan zanyi abinda bakya zato". Kuka mami keyi na bakin ciki da kuma rudewar abinda daddyn yace tana zama tace" na shiga uku na lalace". Jinjina mata kai dady yai alamar batai karya ba ta fadi gaskiya yace" zadai ki shiga ukun ki lalace din kamar yadda kika fada idan har baki gyara halin kiba" bar mata pal on yai ya shiga part dinsa. Page 33 to 34. Sati uku da faruwar haka aka sallamo Zainab daga asibiti mami taci gaba da kula da ita a gida har ta karasa warwarewa". Suna zaune a falo mami ta tasa gaba da tambaya" wai Zainab meke damunki ne kwanan baya Sadiq yaki fada min komai yace tunda kin warke shikenan"?. Kuka Zainab keyi tana kallon mami tace" mami Allah neyai ba gawata zakije ki tarar ba da sauran kwana na a gaba". "Eh meya faru"?. Cigaba Zainab tai "mami wannan shegiyar yarinyar yar kauyen nan wai ta shigo birni ta waye itace ta zuba min guba a abinci naci bansani ba". Zaro ido mami tai "guba ta baki wato kashe ki take sonyi ta zauna ita kadai a gidan ko aiko bata isa ba koda uwar ta take yawo tashi muje yau saita gane kuren ta". Mikewa Zainab tai tana dauko mayafi suka fita ko driver daya zo mami tace bata bukata da kanta tai tukin zuwa gidan. Suna shiga ganin bata palor yasa mami shiga part dinta dama tana wuya da ita akan dawowa gidan da Afeeyah tai gashi alhaji yace bazata koma ba sai Al'ameen ya dawo. Afeeyah bata nan ta tafi makaranta ita kadaice tana gado a kwance sakamakon kanta dake mata ciwo. Mami ta banka kofar da karfi ta shiga ganinta kwance tana bacci yasa ta yaye bargon tana sakar mata wani zazzafan duka tace. "Tashi matsiyaciya kin samu guri wato kura ta mutu ko"? To baki isa ba gata ta dawo". A firgice Fati ta farka cikin magagin bacci ganin wacce ke tsaye a kanta yasa ta wartsake a zabure tace. "Mami kece"? Sannu da zuwa". Cikin tsawa mami tace sannu da zuwan ubanki munafika annamimiya mai hana zaman lafiya yau sai naci uwarki a gidan nan". Mamaki ne ya kama Fati muryarta na rawa tace" mami meya faru wani abu na miki"?. 'Dauketa da mari mami tai a fusace ta fincikota ta soma janta tana cewa "uban maye baki ba ni kike tambaya me kika min zaki gane kurenki yau saikin gwammace mutuwa da rayuwa". Tana zuwa palor da ita ta kifa ta tana kallon Zainab tace "me kike jira fara abinda ya kawo mu ki lakada mata dukan mutuwa". Kanta Zainab tai tana tirmishe ta da dukkan karfinta ta rufe ta da duka ta ko'ina mami na tsaye tana kallo. Dakyar Fati ta samu ta fisge da gudu ta fita daga palon yayin da suka rufa mata baya " Daidai me gadi ya budewa Al'ameen kofa ya shigo Zainab ta shake wuyan Fati'. Ko kashe motar baiyi ba ya fito Afeeyah ma dawowarta kenan taga abinda ke faruwa cikin sauri ta kira daddy da kukanta ta sanar dashi". Hankali tashe Al'ameen ya nufi inda suke yana zuwa wani gigitaccen mari ya sakarwa Zainab wanda azaba tasa da sauri ta saki wuyan Fati tana dafe kunci ta zunduma ihu. Cikin bacin rai yake kallon mami wacce ke aika masa da sakon harara yace". "Mami me kenan kika aikata haka kina kallo a gabanki wannan jakar yarinyar zatai kisa". Wani razanannan kallon 'kiyayya mami kebin Fati dashi tace" ga babbar jaka nan a gabanka mara tarbiyya ita da yake goyon bayanta kake datai nufin kasheta ta zuba mata guba cikin abinci ai baka kula ba". "Itance ta zubawa Zainab guba cikin abinci"?. "Eh ita din karya akai mata"?. Kallon Zainab yai cikin bacin rai yace" ke kuma kinyi sanadin aurenki na sake ki" sannan ya juya gurin mami datai mutuwar tsaye yace. "Kenan mami shine dalilin da yasa kika sakota a gaba tazo tadau fansa bayan bakisan komai game da hakan ba bata da lafiya yanzu da kikasa take dukanta idan ta kashe mata d'a a ciki fa"?.= " 'Da kuma kana nufin ciki ne da ita kome"? mami ta fada tana dafe kirji idonta kamar zasu fito waje Bai tanka ba sai hannu daya rikewa Fati zaibar gurin da ita kukan kura mami tai tana fisgo ta tace. "Wallahi karya ne baki isa ki haifa min jika ba yau saina 'barar da cikin nan". Duka ta sakar mata a ciki harda naushi wanda Fati ta saki 'kara tana faduwa kasa. Daidai shigowar daddy a rude Al'ameen ya durkusa yana dagota kuka Fati keyi sosai ta rike cikin ta. Al'ameen na ganin daddy ya mike da sauri ya rungume shi cikin kunar rai da radadin abinda mamin ta aikata yace. "Daddy mami ta kashe min d'ana ina son baby na amma ta raba ni dashi". Cikin nutsuwa daddy yace" Al'ameen ka saurar..... Shiru yai jin Al'ameen ya tafi luuuu zai fadi yasa yai saurin tare shi yana dago fuskarsa ganin suma yai ya cewa Afeeyah maza ta dauko masa ruwa. Da gudu Afeeyah ta shiga cikin gidan Kasa magana daddy yai tsabar tsananin fushi sai kallo me ma'anoni da yakewa mami wacce ke tsaye gefe duk ta rikice. Ruwan Afeeyah ta kawo masa ya shashshafa masa sannan ya kira Sadiq cewa ya turo motar asibiti guda daya. Harda Sadiq din aka zo ganin haka harda mami a gidan ga Zainab tana kuka yasan ba kalau ba. Sa Al'ameen sukai a mota Afeeyah kuma da Fati suka shiga motar daddy suna fita daga gidan aka bar iya mami da Zainab tsaye'. Dora hannu Zainab tai aka tana rusa kuka tace "na shiga uku shikenan mami Al'ameen ya sakeni wallahi ina sonsa". Tabe baki mami tai ke kada ki wani damu tunda kindau fansa ga kuma na kashe shege ko shegiyar yarinyar dake cikinta ai komai yayi duk wani mataki da zasu dauka aikin banza ne burina ya cika bazan ma koma gida