← Book details Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunawa da maganar da Meemah ta faɗa mata tayi, da sauri ta ce. “ Dan Allah ka taimaka muna buƙatar kudin ne, tun da na gama maka aiki ka barni na tafi bani da lafiya ne.” Ta faɗa cikin sanyin murya da yanayin rashin jin dadi a tattare da ita.

Wani shu’umin murmushi ya saki wanda idan baka lura ba, ba za ka taɓa tunanin ya yi ba.

Janyo wani ƙaramin takarda ya yi ba tare da ya dube ta ba, ya yi rubutu yana ɗagowa ya dube ta tare da cewa. “ Uhm.”

Ba tabi ta kansa ba, dan yau kawai magana take saboda ba za ta iya wani faɗa ba tsabar ciwon dake damun ta, takowa ta yi zuwa gabansa ta sa hannu ta karba takardan.

Buɗewa ta yi tana kallon, da mamaki akan fuskarta ta dube sa da sauri tana cewa. “ 100k ?.” Sai ta kuma duba takardan ta sake dagowa ta dube shi tare da cewa. “ Me zanyi da shi?.”

“ Kiyi sadaka da shi idan kin ga dama.” Ya faɗa yana danna laptop din gaban shi.

Haɗe rai ta yi tana murguda masa baki, kana ta kuma cewa. “ Thanks.”

“ Da ki ka gama muyguda min baki kenan?.”

Shuru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Cigaba da magana ya yi ba tare daya gan ta ba. “ Office din accounter za kije ya baki kudin, and buy medicine for ur health, and before u go make sure u bring some tea for me.”

Gyaɗa masa kai ta yi ta juya zata fita. “ Ga kitchen fa Madam.” Ya nuna mata wani ƙaramin ƙofa da idan baka lura ba zaka ce wani toilet ne.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta juya ta nufa kitchen din, babu wani kayan tarkace a ciki daga gas sai tukunya da kayan shayi da kwalin indomie.

Sauri-sauri ta yi ta haɗa masa tea din duk da irin hajijiyar da yake k’ok’arin dibar ta, tana gamawa ta fito hannunta rike da tray ta ajiye masa a kan table, kana ta jiyo zata masa magana suka haɗa ido.

Murmushi ya sakar mata yana cewa. “ You can go.” Ya faɗa yana nuna mata hanyar fita.

Chan ƙasa-ƙasa ta ce. “ Thanks.” Tare da juyawa ta fice daga office din tana rufe ƙofa.

Da harara PA ta rakata tana jan dogon tsaki, ba shiri Meerah ta juyo tana zuba mata lulu eyes din ta wanda hakan yasa PA yin shuru tana cigaba da aikin ta.

Ƙwafa ta yi tana juyawa ta fice, duk da bata jin dadin jikinta taso ace PA ta kuma tanka mata dan sai taga mai tsaya mata a garin nan.

Tana tafiya tana harare harare ba tare da ta ankara ba ta bangaje mutum, saurin dafa goshin ta ta yi tana ɗagowa ta kalle shi.

“ Kina tafiya bakya lura da hanya.” Taji sauƙar muryansa a kunnen ta.

“ Ai ba laifi na bane, kai ma kana tafiya baka ganin hanya ne ai.” Ta mayar masa da amsa tana wucewa ta gefe.

Sakin baki ya yi yana kallon ta har ta bacewa ganin sa, Jijjiga kai kawai ya yi ya nufa office nashi; yana buɗewa ya ganta zaune tana daddanna laptop, da mamaki ya juya yana kallon hanyar da Meerah ta bi kafin ya juyo yana kallon Meemah.

Dago ido tayi da zummar kallon waye ne, karaf suka had’a ido, miƙewa tayi tsaye tana cewa. “ Welcome Sir.”

“ To idan ke kina nan ita kuma wancan wacece?.” Ya faɗa a ƙaƙare.

“ Waye kuma Sir?.”

Nuna hanyar ƙofa ya yi yana cewa. “ Me kama dake na gani yanzu fa a waje.”

“ Bani bace ai, ina ga Meerah ka gani.”

“ Ku biyu ke nan?.”

“ Eh.”

Murmushi kawai ya yi yana zama a seat nashi, kafin ya dube ta yana cewa. “ Ke kuma baƙa ita fara, amma daga gani ta fiki iya mutumci da hankali.”

Bata ce komai ba sai murmushin da take yi kawai, cikin ranta kuwa cewa take. ‘ Bata tafka maka rashin mutunci bane, amma ina Meerah ina hankali ai ko haɗuwa basu tabayi ba.’ Katsai mata zancen zucin yayi ta hanyar yin maganar da ya kusa daskarar da ita tsaye.

“ Inaso zan aure ta.”

Zama tayi ba shiri akan seat dinta tana sakin baki ganin yanda yake juyi yana murmushi, kamar wacce bataji me yace ba ta ce. “ Sir me kace?.”

“ Aureeeen ta zanyi…”

“ Wa zaka auya?.” Suka tsinkayi muryansa a bakin ƙofa.

Bayan ta fita daga company bata tsaya ko ina ba sai gidan su Yasmeen wanda yanzu za’a iya kira da gidan su.

Da sallama a bakinta ta shigo, shuru kake ji alamun ba kowa, direct ɗakin Yasmeen ta wuce ta fara rage kayan jikinta.

Bayan ta cire kayan jikinta ne ta ɗaura zani, zama tayi a bakin gadon tana miƙa hannu ta ɗauki maganin da Mansoor ya kawo mata yau da safe, ruwan dake kan bedside ta ɗauka tana balla maganin tasha.

Yamutse fuska ta danyi tana tashi bayan ta ajiye maganin da ruwan, sanin cewa ba kowa a gidan yasa bata saka hijab ba ta fito daga ɗakin dan samowa kanta ruwan zafi.

Kitchen ta shiga tana duba kettle dan ta ɗaura ruwan zafi, fuskarta ɗauke da mamakin ganin kettle din a jone gashi kuma ya tafasa, girgiza kai kawai tayi tana zuwa ta kashe, kana ta ɗauki ruwan tana hamdala an hutar da ita.

Toilet din ɗakinsu ta shiga tana zuba ruwan zafin a bucket, ruwan zafin da zai yi wa mutane kusan uku shi Meerah ta juye zatayi wanka da shi.

“ Wai har yanzu babu wanda ya dawo a cikinsu?.” A cewar Mansoor yana wucewa kitchen.

Turus yaja ya tsaya yana kallon kitchen din da mamaki. “ An kutumar raina min wayo, yanzu waye ya juye ruwan da na kai kusan awa ina jira?.” Ya faɗa a kufule.

Fita yayi yana wucewa parlon dan dubawa ko Mama ne tayi amfani da ruwan, har ɗakinta sai da ya duba amma bai ga kowa ba hakan yasa ya fito ya tsaya a filin gidan yana surutu shi daya.

“ Ai ko aljani ne zaiji tausayi na ya barmun ruwan, gashi kuma yaran nan basa nan balle nace su suka ɗauka.” Duba agogon dake ɗaure a hannun sa yayi yana jan tsiririyar tsaki.

Shuru yayi yana kallon ƙofar ɗakin Yasmeen jin kamar ƙarar ruwa, da sauri ya nufi ɗakin yana aiyana irin rashin mutunci da zai yiwa wacce ta ɗauka masa ruwan.

Tsayawa yayi yana kallonta ɗaure da towel da wani ƙarami a kanta ta rufe, ko ba’a fada ba yasan daga wanka ta fito.

“ Keee!.” Ya fad’a a dan tsawace.

Ko tsoro babu ta juyo tana kallonsa fuskarta a tsuke.

“ Waya baki izinin ɗaukar min ruwa?.”

Nan ma shuru ta masa tana kallon shi da manyan idanunta.

“ Wai ba magana nake miki ba yarinyar nan, kin wani zubamin na mujiya?.”

Taɓe baki tayi tana juyawa ta zauna a bakin gado.

A fusace ya ƙaraso gurin ta yana cafko hannunta. “ Idan baki sake sakamin wani ruwan ba ki chanja min suna.”

“ Dama ai ban ma san sunanka din ba.” Tayi maganar tana k’ok’arin fusge hannunta daga ruƙon da ya mata.

“ Ohh haba? Dalla Malama tashi ki sake ɗauramin wani ruwan.” Ya kuma faɗa a fusace yana tada ita da ƙarfi.

Harara ta balla masa tana cewa. “ Sai ka barni na saka kaya ai kafin kace na ɗaura maka ruwan.”

“ Da bakisan baki da kaya ba kika ɗaukamin ruwa? Kuma wani jikin za ki sakawa kayan? Ke wuce muje ki sake ɗauramin wani.”

“ Nifah ban iya ba.”

“ Za ki koya muje.”

Turo baki gaba tayi tana wucewa yana binta a baya har zuwa kitchen din.

“ A ina kika ajiye kettle din?.”

“ Yana ɗaki.”

“ Oya je ki ɗauko.” Ya fad’a yana matsa mata dan ta wuce.

Murmushi ta sakar masa tana k’ok’arin wucewa.

“ Wait bari naje na ɗauko.” Da haka ya wuce.

Bata fuska tayi tana magana ita daya. “ Daka bari naje na dauko ai, dani da kettle din duk ba zamu fito ba dan key zan sawa ɗakin.”

“ Shiyasa nace zan ɗauko ai.”

Taji muryansa yana miƙa mata kettle din, hararan shi tayi tana karɓa, ruwa ta zuba tana jonawa.

Kana ta juya ta fita tare da yin magana ƙasa-ƙasa. “ Matar ka ta boni ga bakin hali ga mugunta.”

Da sauri ya juyo yana cewa. “ Kika ce me?.”

Ɗaki ta shige tana saka key.

Ƙwafa yayi yana fita ya koma ɗakinsa.

Dariya Jameel ya yi yana cewa. “ Ita zan aura, ita kadai zan aura, itace wacce na tsaya jira tsawon shekaru.”

Duban Meemah Alyan ya yi yana cewa. “ Dama bayi da lafiya ne ko ciwon shi ne ya tashi?.”

Da sauri Jameel ya iso gurin shi yana kama hannun shi, yana cewa. “ Ga ta da kyau, kwarjini, manyan idanu, ga body, ga shagwaɓa, kai in fact ta hadu Alyan.”

Kallon rashin fahimta ya masa yana cewa. “ Waye wai?.“

“ Annurin zuciyata mana, kai Bobo idan ban auri yarinyar nan ba zan iya mutuwa har lahira.” Ya fad’a yana dafa saitin zuciyarsa tare da sakin murmushi.

Kallon Meemah Alyan ya yi yana son ƙarin bayani.

“ Sir wai akan Mee…” Dakatar da ita Jameel ya yi yana cewa. “ Me na zaƙewa Anutyn mu.”

“ Anuty kuma?.” Tayi maganar tana nuna kanta.

Cigaba da magana Jameel ya yi yana cewa. “ Bobo wacce ta fito daga office ɗinka yanzu fa.”

“ Wai wa kake faɗa ne?.” Alyan ya yi maganar yana dan boye fargaban shi.

“ Ohh wai ya kake so na faɗa maka ne?.”

“ Sunan ta zaka faɗa min.” A cewar Alyan.

“ Meerah…

09027308227 chart Only

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

5- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, sacrifice, heartbreak and destiny_

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

________________________________

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
Chapter 4 · 0% Book details