Sashe 21
Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Ba tare da ta dago kai ba ta ce. “ Har kana da bakin da zaka ce min kukan ya isa bayan kai ne silan kukan, ko ka manta cikin shege ne fa a jikina.”
Tauna lebe yayi yana bude murfin motan ya fito, zagayowa yayi ya bude mata yana saka hannu ya kama ta, dago da kai tayi tana kallon shi, kafin ta fito.
Kallon compound din take tana sake kallon shi, hanyar da zai sadaka da parlon ya nufa yana rike da hannunta. “ Ina ne ka kawo ni?.”
Bai bata amsa ba ya tura kofan parlon, tana biye da shi a baya suka shigo tsakiyar parlon, kallon ko ina take da ido tana tunanin nan kuma ina ya kawo ta, takun takalmi taji hakan yasa ta daga kai da sauri tana kallon mai saukowar, da sauri ta sake buya a bayan shi.
Kallon shi Ammy take fuskarta dauke da mamaki da al-ajabi musamman da tasan baya kasar, bata tabbatar ba sai da ta bude baki ta ce. “ Babana!!.”
Sunkuyar da kansa yayi murya a kasa ya furta. “ Ammy.”
Jin haka ya tabbatar mata da shi ne, da sauri ta sauko daga upstairs din ta iso din yake tana cewa. “ Babana ya na ganka a nan?.”
Shuru yayi bai ce komai ba, sai ma sunkuyar da kai din da yake ta yi, idanunta ne suka sauka akan bakinsa wanda ya fashe da jini a wajen, da sauri tasa hannu tana dago da fuskarsa ta furta. “ Subhanallah me yake faruwa ne wai? Kayi wani laifi ne ko me?.”
Nan ma shuru ya yi zuciyarsa sai harba uku-uku yake.
“ Alyan me ya faru?.” Ta kuma tambayarsa.
Laylerh da fitowar ta kenan taji Ammy na tambayarsa, dama ta shirya ne zata je gidan su Yasmeen, ita ma cike da mamaki ta kira sunan shi. “ Yaya?.” Kafin ta karaso gurin.
Cike da damuwa Ammy ta kuma cewa. “ Alyan banason irin haka ka fito fili ka sanar dani halin da kake ciki.”
A hankali ya dago kai yana kallon Mahaifiyarsa din, kamar mai koyan magana ya fara cewa. “ Ammy… dama…. Akwai…” Shuru yayi yana kallon ta.
“ Alyan ka fadamin me yake faruwa zan taya ka yakin.”
Numfashi ya sauke yana matsawa gefe, da sauri Laylerh ta furta. “ Meerah!!!.”
Kallon ta Ammy take tana sake kallon Alyan din, alamun bayani take son ji.
Da sauri ya kama hannun Ammy yana cewa. “ Ammy kiyi hakuyi, banyi dan na bata miki yai bane, amma… amma nasan cewa ke din uwa ce kuma zaki fahimce ni.”
“ Bangane ba, wace ce ita?.” Cewar Ammy tana sake kallon Meerah wacce ta sunkuyar da kai hawaye na bin kumatun ta.
“ Ammy In-law dinki ce ita.”
Kallon mahaukaci ta bishi da shi tana cewa. “ A taya ta zama In-law dina? Banason shirmen banza fa wacece ita?.”
Kan shi ta sunkuyar ya fara magana. “ Ammy tana da ciki ne kuma nawa ne….” Saukar mari kake ji har sau biyu, da sauri Laylerh ta kama baki a tsorace, Meerah kuma ta durkushe a kasa hannunta na kan kumatun ta tana kuka..
*SAI MUN HADU A BOOK TWO IN SHA ALLAH, ZAI ZO ON 28th APRIL🙌*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
Alhamdulillah!!!!! na kammala book one🤗 ga masu buk’atar su cigaba da karanta littafin *BA KAI NAKE SO BA* Book two dari biyar ne ~N~ 500, amma zanyi discount ga mutane goma da zasu fara biya da farko, zasu iya biyan dari hudu ~N~ 400🫠🫠🫠, dan haka ku hanzarta kar wannan damar ya wuce ku🤗😘😘😘. Za’a iya biya via 9031176727 Fatima Isa Opay, idan mutum ya turo da kudin sai ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta WhatsApp number ta 09027308227 SAHIBAR JAJIRTATTU ko DR TEEMAH.
Kar ku bari wannan labarin ayi sa ba tare da ku ba❤️🌹🫠 Yan Nijer kuma su min magana.
*BOOK TWO zai fara zuwa ne 28th April In Sha Allah kar ku bari ayi baku🤗🤗🤗*