← Book details Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan da nan idanunta suka cika da ƙwalla, kamar wacce akace ki fara kuka kawai ta fashe mata da kuka tana faɗawa jikinta.

“ Subhanallah ni dama nasan wani abu ne ya faru, kiyi hakuri love komai zai wuce, me ya faru.” Tana maganar tana bubbuga bayanta alamar rarrashi.

“ Meemah me ya sa kaddarar mu take zuwa a haka? Mun aikata zunubi ne bamu sani ba, da nasan haka kaddara zata zo da ban darsu cikin duni…” Saurin rufe mata baki ta yi tana girgiza mata kai.

“ Koman da ya faru rubutaccen kaddara ne, kar kiyi saɓo Meerah.”

Numfashi ta sauƙe tana cewa. “ Idan na faɗa miki komai kar ki ga laifi na dan Allah, hakan zai ƙara saka zuciyata cikin ƙunci.”

Murmushi ta mata tana cewa. “ A guna bakya laifi kuma ba za ki taɓa yi ba har abada, ki faɗamin komai idan na shawara ne zan baki idan kuma na kuka ne sai mu taru muyi tare, kin ji so faɗamin me ya faru da aka ce kin ɓata?.”

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallon ta ta fara magana. “ Kin san Alyan?.”

“ Waye Alyan kuma?.”

“ Wanda muke aiki a company shi, wanda yazo ranar har na masa rashin kunya shi da Yaya Mansoor.”

“ Ohhh eh na gane shi.”

“ To tun ranar da na rubar masa da coffee a jiki ya ƙullace ni…. Nan ta bata labarin komai da komai tana kuka ta ɗaura da cewa. “ Da nasan haka zai faru Wallahi Allah da banje neman aiki a company ba.”

Ita ma Meeman kuka take tana cewa. “ Ni banga laifinki ba Love, kuma ai komai da ya faru Allah shi kaɗai yasan me ya boye a tsakanin ku.”

Tana kuka ta ce. “ Tamkar karuwa fa ya ɗauke ni, ya mayar dani tamkar abinci.”

Jawo ta jikinta ta yi tana rarrashin ta, ta ɗaura da cewa. “ Da ciwo abun amma idan za ki iya komai mai sauƙi ne, ki cigaba da rayuwarki kamar komai bai faru ba, amma aiki kam a company ki bari ko ince mu bari, tun da har ya baki Atm din shi kin ga sai ki biya kudin Makaranta na part three sai ki cigaba da yi.”

Da sauri ta ɗago kai tana kallon ta. “ Wai na cigaba da yi ke kuma fa?.”

“ Nima ai Allah zai kawo.”

“ Yanda zanyi haka za kiyi.”

Murmushi Meemah ta mata tana cewa. “ Yanzu ya soyayyar Yaya Mansoor din a gurin ki?.”

Da mamaki ta ce. “ Wani Mansoor din?.”

“ Wanda kika sani.”

“ A’a babu soyayya kuma ni a rayuwata ai, an rushe min komai, abun da nake taƙama da shi an ƙarbe ta ƙarfin tsiya, ni yanzu maza ma kallon daya nake musu da ni…”

“ Kar ki sake faɗan irin wadan nan kalaman, idan bakya son Mansoor ai akwai Jameel.” Ta ƙarashe tana dariya.

Murmushi kawai Meerah ta mata tana cewa. “ Kin ga har an fito daga magariba bamu yi sallah ba.”

“ Ai na mai da kina off ne, dan nasan tare muke yi.”

“ Aa bana yi nikam kila ya chanza ya koma ƙarshen wata, bari na tashi nayi sallah.”

“ To bari naje gurin Yasmeen ko ta gama.” Da haka Meemah ta fice ita kuma ta shiga toilet dan ɗauro alwala, ta dan daɗe a toilet din tana tsaye duk tunanin duniya ya ishe ta, ga maganar Mama da ta mata wai ta mishi biyayya sai kace ubanta ko mijinta, ta gefe guda kuma har cikin ranta tana kewarsa amma idan ta tuna da cewa ita karuwarsa ce kamar yanda yake faɗa sai taji ba dadi.

Ganin tunanin babu abunda zai haifar mata ne yasa ta yi alwala tana fitowa, sallah ta gabatar tana addu’a sosai a ciki.

**************
INDIA / DALHI
**************

kwance yake akan makeken gadon shi suna video call da Ammy, duk damuwa ya bayyana akan fuskarsa, Ammy ce ta lura da hakan tana cewa. “ Babana ko akwai matsala ne.”

Shuru yayi ba tare da yace komai ba, sake tambayar sa ta yi yayi saurin firgita yana cewa. “ Meeyah!!!.”

Da mamaki Ammy ta ce. “ Wace ce ita Babana? Ƴar wace ce haka da ta rikita ka kake tunanin ta?.”

Shafa sumar kansa yayi yana cewa. “ Ammy sai da safe bacci nake ji, bye love you.” Da haka ya rufe laptop din.

Gyara kwanciyar shi yayi yana faɗawa duniyar tunani, ya dade a haka kafin ya tashi ya shiga yayi alwala ya dawo yana sallan nafila, sai kusan ƙarfe uku kafin bacci ya ɗauke shi, yana kwanciya ba da daɗewa ba aka kira sallan asuba.

Idanunsa duk bacci ya farka yayi alwala ya wuce masallacin dake ƙofar gidan shi, sai da alfijir ya fito kafin ya fito daga masallacin, kansa a ƙasa ya nufa ƙofar gidansa.

Buguwa yayi da mutum hakan yasa ya ɗago kansa yana kallon ta, hade rai yayi yana ja baya.

“ Beb.” Wata ƙyaƙyawar budurwa ce ta faɗa tana masa murmushi.

Ta gefen ta yabi zai wuce, saurin rungume shi tayi ta baya cikin yaren turanci ta soma magana. “ Beb kasan yanda zuciyata yake min kuwa na rashin ka.”

Bantare ta yayi daga jikinsa yana magana a fusace cikin turanci shi ma. “ Keee!!! Ki yike kanki okay, banason hauka da gidadanci ba sonki nake ba ki fahimta!!!!.”

Da gudu ta nufa gidan dake facing din nashi tana kuka, tsaki yaja yana shiga gidansa, kallon security’s din yayi yana musu warning ⚠️ akan kar a bar kowa ya shigo, da haka ya nufa cikin parlon.

Ɗakinsa ya nufa yana ɗaukar wayansa ya duba agogo, 8:02am dot ya nuna kenan a nigeria 12:32pm, danna kan sunan da aka rubuta best choice yayi yana mannawa a kunne.

Da safe suna tashi Meemah ta kama girki, Yasmeen shara Meerah kuma wanke-wanke, kafin ƙarfe takwas duk sun gama kowa yayi wanka anzo cin abinci.

Ganin babu Mansoor ne yasa Meerah tashi tana cewa. “ Mama bari naje na kira Yaya.”

Murmushi kawai Mama ta mata tana gyaɗa kai, part din Mansoor ta shiga tana sallama, amsawa yayi yana fitowa daga ɗaki, murmushi ya mata yana cewa. “ Meemah gani ma fitowa ai.” Ganin Meerah ce yasa yayi shuru.

Kallon junan su suka tsaya yi na mintuna, a hankali ta janye idanunta daga nashi tana cewa. “ Dama abinci ne nazo kiranka.”

Shi ma dauke idanunsa yayi daga gare ta yana cewa. “ Muje to.” Da haka suka nufa parlon.

Abinci akaci kowa ya tashi Meemah ta tattare gurin, Mansoor ya nufa gurin aikinsa, Yasmeen ta shirya ita da Meemah suka nufa gidan kawarsu dake unguwar, ba yanda ba suyi da Meerah ta bisu ba amma tace sam babu inda zata je haka nan suka bar ta ba dan sun so ba.

Ɗaki ta shiga ta gyara ta hau kan gado ta kwanta, bacci ne ya ɗauke ta, guraren ƙarfe 12:32pm wayanta ya fara ringing, farkawa ta yi a dan razane tana ɗaukan wayan.

Ta cikin wayan taji ya sauƙe ajiyar zuciya yana cewa. “ Meeyah.”

Cikin magagin bacci ta ce. “ Na’am.”

Sauƙe wayan daga kunnen sa yayi yana duba sunan, ganin eh lambar ne yasa shi mannawa a kunne yana cewa. “ Bacci kike yi ne?.”

“ Uhm Baby.”

Da mamaki ya sake duba number kafin ya ce. “ Kina saka hijabin a gida?.”

“ Uhm uhm ni haka nake yawo.”

Murmushi yayi dan ya lura bacci ke sa take fallasa, hakan yasa ya fara cewa. “ Kin yi missing dina ne?.”

“ Eh sosai.” Ta faɗa cikin bacci.

“ To bani labari?.” Ya faɗa yana zama a bakin gado dan ya lura zaiji dadin hiran.

“ Ni ka dawo kawai.”

“ Kina kewa na ne?.”

“ Eh har da kwanciyan da muke yi....” Ware idanunta tayi da sauri, jin sautin murmushin sa yasa ta ce. “ Kaji me nace ne kake dariya.”

“ Aa babu abunda naji.” Kashe wayan ta yi tana tashi ta zauna a tsakiyar gadon, tagumi ta yi tana jin kunyar maganganun da tayi, kira ne ya sake shigowa wayanta, ganin shine yasa ta kashe wayan gaba daya tana jan tsuki.

Shafa sajen sa yayi yana murmushi kafin ya tashi ya watsa ruwa ya shirya cikin suit baki da fari, takalmi ya saka baki yana ɗaukar jakarsa ya fito, da sauri daya daga cikin driver dinsa ya ƙarba jakan yana nufan mota da shi, buɗe masa back site yayi yana shiga shi ma ya shiga yana tadawa, buɗe get akayi suka fita.

A haka su Meemah suka dawo suka same ta tayi tagumi, kallon junan su suka yi kafin Meemah ta isa gurin ta tana cewa. “ Love me kuma ya faru.”

Kallon ta ta yi tare da cewa. “ Nayi babban casting….

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

21 - 22 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝🤝

*GARGADI*

Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*

*BOOK ONE*

*P.21 & 22*

A haka su Meemah suka dawo suka same ta tayi tagumi, kallon junan su suka yi kafin Meemah ta isa gurin ta tana cewa. “ Love me kuma ya faru.”

Kallon ta ta yi tare da cewa. “ Nayi babban casting.”

“ Na me kenan?.” Cike da fargaba ta tambaye ta tana kallon cikin idanunta.

Ganin Yasmeen tana dakin ne yasa ta mata maganar ido, gyada kai tayi tana cewa. “ Allah ya kiyaye gaba.” Ta fada tana dariya.

*Bayan sati biyu*
Chapter 16 · 0% Book details