← Book details Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 21

Sashe 13

Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowa toilet ɗin yayi yana ganin ta kafin ya ƙarasa, jin kamar an tsaya a kan ta ne yasa ta buɗe idanunta tana ganin shi, murmushi ya sakar mata tana mai kau da kanta gefe.

“ Na taya ki?.” Ya mata maganar a tausashe.

“ Ce maka akayi ina buƙatar hakan ne?.”

Murmushi ya kuma yi yana tusa hannunsa cikin sumar kansa, kafin ya ce. “ Ki gama za muyi magana.”

“ Ashe kuwa bazan gama ba idan da kai zanyi magana.”

“ Ok ki dauwama kay ki fito.” Ya faɗa yana juyawa ya fice daga toilet din.

Tana jin ya fita ta tashi tayi wanka ta tsarkake jikinta, ruwa na zuba daga kanta ta fasa wani uban kara. “ Haaaaaaaaaa!!!.”

A take security’s dake waje kowa ya sai ta bindigarsa yana jiran yaji ta ina za’a fito.

Da gudu ya shigo toilet ɗin har yana ƙoƙarin faɗi, cak ya tsaya yana kallon ta cike da mamaki da al’ajabi, muryansa a dake ya ke cewa. “ Meeyah.”

Kallon shi kawai tayi tana jawo towel ta ɗaura tare da wucewa ta gefen shi ta fita.

Bin bayan ta da kallo yayi yana tunanin ko aljanu sun shafe ta ne, biyo ta ɗakin ya yi jikinsa duk kumfa da alama yana cikin wanka ya ɗauro towel ya fito da gudu.

Zama tayi a gaban dressing mirror tana shafa mai, ta cikin mudubin ya kuma cewa. “ Meeyah.” Nan ma mantar dashi tayi tana cigaba da shafa mai.

Kamar zai haukace ya ƙara cewa. “ Wai me ya same ki ne?.”

“ Ka mayar dani gidan mu shine ya same ni Alyan.” Tayi maganar a tsanake.

Da mamaki ya ke kallon ta, tun da suke ko kiran sunan shi bata taba yi ba, sai dai tace Sir ko Malam amma ta kira sunan shi gatsau bata taba ba, sai gashi yau ta kira babu ko inkiya a ciki.

Gyaɗa kai ya ke kamar sabon mahaukacin kadangare kafin ya juya ya fice daga ɗakin.

Fitan shi bai fi da mintuna goma ba wata mata ta shigo da kayaki a hannun ta, kallon matar Meerah ta yi tana jan tsaki dan ta gane ta farkon kawo ta itace tazo, kuma ta sanadiyar ta ne duk haka ya faru.

Fita tayi ta sake shigowa kafin ta ce. “ Hajiya ina wuni.”

Kallon sifili ta mata tana cewa. “ Idan ban wuni ba za ki ganni ne.”

Ba tare da matar ta ce komai ba ta juya ta fice.

Tashi tayi tana zazzage kayakin akan gado bayan ta cire bedsheet din, sosai kayakin suka tafi da imanin ta, duk wanda ta ɗauka sai ya burge ta, wani simple ta dauka tana sakawa sauran kuma ta buɗe wardrobe nashi ta mayar da kayan shi a wardrobe biyu, ita ma ta saka nata a wardrobe biyu duk da kuwa nata din ko daya bazai cinye ba.

*UNGUWAR DOSA*

Hankalin Meemah yanzu kam ya ɗan kwanta, ga wani shakuwar da ya shiga tsakanin su da Mansoor dan kusan kullum idan zai fita aiki tare suke tafiya, ya barta a office idan zai shiga theater, idan kuwa ganin patient zai yi tare suke tafiya, dayawa sun ɗauka matarsa ne.

Yau satin Meerah biyu da batawa, Meemah ce ta fito da sauri tana cewa. “ Mama sai mun dawo.”

Dariya Mama ta mata tana cewa. “ Ai Mansoor ne zai ishe ku kuwa ba yawo ba, Allah ya tsare.”

Gaba ta buɗe tana shiga tare da cewa. “ Yaya sorry na tsaya ɗauko takalmi ne.”

Kallon ta ya tsaya yi na wasu seconds kafin ya mayar da hankalin shi kan tuƙi, suna tafiya suna hira har suka isa Hospital din, parking yayi suka fito suna tafiya a jere.

Tun ranar da ya fice daga ɗakin bai ƙara zuwa ba, yau kusan sati kenan rabon da ta kalle shi ido da ido, haka zata wuni a ɗaki idan ta gaji ta fito parlon ta zauna, bata san yana da muhimmanci ba sai da ya kusan sati baya gidan, har hankalinta ya tashi gashi ba damar fita ƙofar parlon a ƙanƙame kuma kullum securitys suna aikin su.

Sai da yunwa ya kusan halaƙar da ita kafin tasan da kitchen a gidan, ko da ta shiga kitchen din akwai kayan abinci narke a store tun daga kan kayan shayi har zuwa kayan abinci, a fridge kuma su kayan miya ne da nama da kifi, dayan fridge ɗin kuma su juice ne kala-kala.

Haka zata tashi da safe tayi sallah tayi wanka ta ɗaura girki iya cikinta, ta gama ci ta koma tayi bacci, tayi jiki amma bana kwanciyar hankali ba, dan kusan kullum sai tayi tunanin yar uwarta da shi haka zata zauna taci kuka har ta ƙoshi.

Yau ma kamar kullum tana gama girki ta ajiye a daining, kitchen ta koma ta ɗauko juice na 5 alive ta fito, tana sanye da maroon din riga na shan iska, ta danyi jiki dan hips din nan ya cika Masha Allah, ta danyi haske ga wani kyau din data karayi na kwanciyar hankali, ba ko bra a jikinta dan kusan kullum haka take yawon ta bata sakawa, gashin kanta na yawo ta baya dan bata kama ba.

Zama tayi tana fara cin indomie da ta dafa wanda yasha busheshen kifi, tana ci tana shan juice ɗin ta har ta gama ta tattare ta je ta wanke ƙwanuƙan.

Kwanciya tayi akan three seater tana kunna tv, nigeria flim ta saka tana kallo, bacci ne ya ɗauke ta a gurin.

Sosai ya mayar da hankalin shi kan aikinsa, duk da kuwa yana muraɗin kallon ta amma hakan bai hana shi ɗaurewa ba ya cigana da aikinsa.

Yau ma ya shirya ya fito daga ɗaki hannun shi rike da traveling bag ya sauƙo ƙasa, Ammy ce ta fito da wani bow na tangara a hannunta tana murmushi tana cewa. “ Babana har ka fito.”

Ƙarɓan abun hannunta yayi yana cewa. “ Ammyna na fito.”

“ Dambun kaza na maka nasan kanaso, a hanya sai kana ci.”

Sumbatar kumatun ta yayi yana cewa. “ Ammy ina sonki sosai, Allah baymin ke.”

“ Amiin Babana, yaushe zaka dawo to?.”

“ Ammy idan na gama saita komai.”

“ Allah ya taimaka to.”

“ Ameen Love.”

Laylerh ce ta fito da waya a hannunta tana cewa. “ Masha Allah taƙurarre zai yi tafiya, Allah tsare hanya nima zan samu na fita yawo.”

Juyawa yayi yana kallon ta kafin ya ce. “ Zo ki bani wayan da na siya miki.”

“ Haba Bro daga maka wasa sai ka ɗauka da gaske ne, nifa ko a lahira cewa ake kowa ta kansa yake to ni ta kai nake Bro.” Ta faɗa tana marairaice fuska.

Murmushi kawai ya mata yana fara tafiya suna rakasa a baya, har gurin mota suka raka shi yana cewa. “ Layleyh ko zamu tafi taye ne?.”

“ A’a kaje kai daya banaso nikam, chabb mutuwa kenan.”

“ Ni ko?.”

“ A’a Bro ni.” Ta faɗa tana masa dariya.

Sallama ya musu yana shiga mota, amintaccen driver din sa ne ke jan sa wato Alex, ta mudubi ya dubi uban gidan nasa yana cewa. “ Sir ina zamu je.”

“ Unguwar Yimi.”

Cike da mamaki Alex ya ce. “ Sir ba tafiya zaka yi ba?.”

“ Shine tafiyan da zanyi ai, sanna idan ka koma kace ka kaini Airport.” Gyaɗa kai kawai Alex yayi yana murmushi, da haka suka isa Unguwar Rimi.

A bakin ƙofar parlon ya tsaya yana saka key ya buɗe parlon, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga, idanunsa ne suka sauƙa akan ta tana bacci a gujera.

Rufe ƙofar yayi yana ƙarasawa ya ajiye bow din da Ammy ta bashi, sunkuyawa yayi yana kallon fuskarta da ya cika yana sauke idanunsa akan lips din ta, haɗiye yawu yayi yana hura mata iska a fuska.

Bata fuska tayi tana cigaba da baccin ta, hannu yasa yana wasa da gashin kanta, a hankali ta soma buɗe ido tana jin kamshin turare da tasan mutum daya ne kawai ke shafawa.

Da sauri ta gama buɗewa tana sauƙe su akan shi, murza idon ta kuma yi tana sake buɗewa, murmushi yake mata ganin abunda take yi, kuka ta fashe da shi tana cewa. “ Nikam na shiga uku ya sake dawowa….

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

15 - 16 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝🤝

*GARGADI*

Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*

*P.15 & 16*

Da sauri ta gama buɗewa tana sauƙe su akan shi, murza idon ta kuma yi tana sake buɗewa, murmushi yake mata ganin abunda take yi, kuka ta fashe da shi tana cewa. “ Nikam na shiga uku ya sake dawowa.”

Da mamaki ya ce. “ Sai kace kin ga dodo ko aljani.”

“ Ai kai kafi dodo ma.”

“ Haka ake tayban mutum dama idan ya dawo, babu hug babu muyna babu komai sai baƙin magana.”

“ Ma kai zan yiwa hakan? Lallai kam.”

Taɓe baki yayi yana tashi ya zauna ta gefen ta, zuba mata sexy eyes din shi yayi yana kallon yanda tayi fresh, ga wani jikin da ta danyi kenan da baya nan tajin daɗi? Kenan yana takuya mata ne?.

Murmushi ya kuma yi yana cewa. “ Zan samu yuwa?.”

Haɗe rai ta yi tana turo baki gaba kafin ta tashi ta nufa kitchen, da ido yabi bayanta yana haɗiye yawu har ta dawo hannunta rike da tray da faro da cup, dire masa ta yi a gaban shi tana komawa dayan kujeran ta zauna.
Chapter 13 · 0% Book details