← Book details Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 21

Sashe 2

Ba Kai Nake So Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Meemah ta sa hannu tana rufe bakinta dan kar dariyar ya subuce, ta witsiyar ido ta ganta, kafin ta ce. “ Are you laughing at me Meemah.”

Girgiza kai ta yi, ƙwafa Meerah ta yi tana cewa. “ If i go make i d…” Da saurin Meemah ta rufe mata baki tana cewa. “ Please Meerah don’t say no, bamu da wani hanyar da zamu biya kudin hayan nan, ga school zamu shiga part two, kinsan dole za muyi registration, and babu wani kayan abincin da muke da shi bayan indomie daya rage guda biyar; babu wanda yake taimaka mana tunda Dad da Mom suka rasu, gidan mu na gadon ma su Uncle sun ƙwace. Kin ga dole mu yarda da duk gurin da ya ajiye mu.”

Ta ƙarashe maganar a raunane.

Sanyi jikinta ya yi, cikin wani irin yana yi ta dube ƴar uwarta ta tana cewa. “ Shi kenan, but ki sani bazan yi tolerate din ko wani wulaƙanci ba.”

Murmushi ta sakar mata tana cewa. “ Babu ma wanda zai miki wulaƙanci Love, and nima ai ya ɗauke ni aiki a company.”

Da sauri ta juyo tana kallon ta, alamun tana son karin bayani, murmushi ta yi tana ɗaga mata kai tare da cewa. “ A matsayin mai duba shiga da fita na office din accouter.”

Waro ido ta yi tana cewa. “ So ni ya rainawa hankali ke nan, ni ce cleaner ko.”

“ Love ki ɗauka ke ce me kamfanin bashi ba, kar ki kawo tunanin ke cleaner ce a company ok.”

Lumshe ido ta yi tana tashi tsaye tare da cewa. “ Bari na watsa ruwa na gaji, sannan ki dafa mana indomie din ko guda biyu ne, gobe kafin mu fita sai mu dafa uku.”

Gyaɗa mata kai kawai tai, da haka ta wuce toilet, Meemah kuma ta fice.

Yana ƙwance akan makeken gadonsa ya yi ruf da ciki, idanunsa a rufe kamar wanda ya ke bacci, ringing din wayansa ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa.

Hannu ya miƙa ya ɗauka tare da mannawa a kunne, ta cikin wayan ne ake cewa.

“ Sir munyi bincike sosai akan yaran, gidan da suke ciki ma na hayane, sannan su biyu kawai suke rayuwar su basu da kowa.”

Jijjiga kai ya yi yana cewa. “ A nemo me gidan da ya basu hayan ya kore su nan da kwana biyu.” Da haka ya kashe wayan ba tare da ya jira ya ji me wancan din zai ce ba.

Tashi ya yi yana zura jallabiya ya sauƙo ƙasa….

*COMMENTS AND SHARE FISABILILLAH🙏*

09027308227 chart only

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

2- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, sacrifice, heartbreak and destiny _

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

________________________________

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
____________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
___________________________________

*GARGADI*

Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*

*P.2*

Tashi ya yi yana zura jallabiya ya sauƙo ƙasa, wata ƙyaƙyawar mace ce zaune a kan haɗadɗan two seater, ta ɗaura ƙafa daya kan daya tana kallon labarai, fuskarta ɗauke da murmushi take ganin ɗan nata, kafin ta ce wani abu ya ɗurkusa yana cewa. “ Ammah ina wuni.”

Murmushin nata ta faɗaɗa tana cewa. “ Lafiya Babana, ya aikin?.”

“ Alhamdulillah.”

“ Ka shigo ɗazu ina maka magana baka kulani ba, kuma naga ranka a ɓace, hope everything is fine.”

Sosa keya ya yi dan yasan sarai ɗazu ya jita amma ya basar, saboda ɓacin ran daya dawo dashi daga office, cikin lallaba ya ke cewa. “ Kiyi hakuyi Ammah, dazun ne yai na a bace.”

Murmushi ta masa tana cewa. “ Ya wuce ai, kaci abinci kuwa?.”

Ƙarɓan remote din hannunta ya yi tare da chanja channel zuwa na ball, kafin ya ce. “ Ammah am okay bana jin yunwa.”

“ Kai ka sani kuma, tv din ɗakinka bai ishe ka bane zaka zo ka hanani kallo.”

Dariya ya yi yana cewa. “ Ammah ɗakin ne ba daɗin kallo, kuma yau ake buga World Cup shi ya sa.”

Taɓe baki ta yi tana tashi ta nufa ɗakin ta.

Ringing wayansa ya ke yi, hannu ya sa ya ɗauka yana mannawa a kunnensa, ta can bangaren ne ake cewa. “ Sir mun bashi million biyar din, sannan ya ce yau zai kore su daga gidan.”

Murmushin gefen baki ya yi yana buɗe baki cikin rashin son magana irin nashi ya ke cewa. “ Good, and make sure kay a kuskuya wani ya taimake su.”

“ Okay.”

Da haka ya katsai wayan yana murmushi.

“ Ya Alyan yau kai ne da wannan maganar.” Wata ƙyaƙyawar budurwa ta faɗa, kai daga gani basai an maka dogon bayani ba kasan ƙanwarsa ce, duba da irin kaman da suke sosai.

Zama ta yi kusa da shi tana cewa. “ Ma waye din ne kar a taimakawa Bro.”

Tamke fuska ya yi kamar ba shi bane ya ke murmushi yanzu, kafin ya dube ta a tsare yana cewa. “ Laɓe ki ke min?.”

Saurin girgiza kai ta yi tana cewa. “ Nazo wucewa kitchen ne naji kana waya.”

“ And sai aka ce ki tsaya kina sauyayan abunda nake faɗa?.” Nan ma ya yi maganar fuska babu annuri.

Tashi tsaye ta yi tana turo baki tare da cewa. “ Daga tambaya sai a fara min masifa.” Tana maganar tana nufan kitchen.

Tsawa ya daka mata ta hanyar cewa. “ Laylah!!!.”

Da sauri ta juyo tana rufe bakinta, kafin ya yi wani magana tuni ta gudu ɗakin Ammah, ƙwafa ya yi yana tashi ya haura sama ran sa fesss.

Suna zaune a ƙasan bishiya suna dan taɓa hira, amma duk rabi da ƙwatan hiran Meemah ce ke yin ta, ita dai Meerah sai dai ta bita da uhm.

Sallama aka musu daga waje, duban juna suka yi Meemah na cewa. “ Waye kuma da mangarib nan?.”

“ Ki zauna bari naje na duba.” A cewar Meerah tana tashi tsaye, veil din dake kanta ta warware ta yafa tare da saka takalmi ta nufa ƙofa.

Fitowa wajen ta yi tana gaishe da dattijon.

Fuskan mutumin babu alamun tausayi ya ce. “ Ina ƴar uwar taki.”

Dan ɗaga gira Meerah ta yi tare da kama ƙwanƙwaso tana cewa. “ Wani abun zaka mata.”

“ Ƴar nan karki min rashin kunya, ko baki gane ni bane.” A cewar mutumin yana ɗaga murya.

Kallon up and down ta masa tana cewa. “ Ba Malam Zubairu bane mai gida.”

“ Ashe kin gane ni.”

“ Sosai kuwa, yau kuma da wani rashin mutuncin ka dawo.” Ta yi maganar tana duban gardawan dake gefen shi tsaye su huɗu.

Jin shuru har yanzu Meerah bata shigo ba ya sa Meemah tashi ta saka hijab sannan ta fito. Ganin mai gidan hayan da suke ciki ne ya sa Meemah cewa. “ Baba lafiya dai ko.”

“ Zuwa nayi ku fita min daga gida na.”

A kiɗime Meemah ke cewa.” Baba me muka yi kuma? Ka rufa mana asiri dan Allah.”

“ Idan ba za ku fita salin alin ba, zan saka gardawan nan su fitar da ku ta ƙarfin tsiya.”

Ɗurkusawa ƙasa Meemah ta yi tana cewa. “ Ka rufa mana asiri dan Allah, ina zamu je da yamman nan idan ka kore mu.”

“ Wannan kuma ku kuka jiyo, kai dalla shiga ku ciro duk kayan dake gidan.” A cewar Zubairu yana nuna gardawan da suke tsaye.

Bangaje Meemah suka yi suka nufa cikin gidan, murmushi Meerah ta yi tana cewa. “ Me na kuka kuma Sis.”

“ Meerah koran mu fa akayi daga gidan, ina zamu je ki ke tunani.” Cikin kuka Meemah ke faɗan hakan.

Goge mata hawayen fuskarta ta yi tana cewa. “ Kar ki damu, ko kin manta Allah ne gatan mu.”

“ Amma Meerah ai…” Saurin rufe mata baki ta yi tana girgiza mata kai.

Matsawa gefe suka yi, aka fara wurgo musu da kayan su waje, duk mutanen da zasu wuce sai sun bada hakurin akan a bar su zuwa gobe, amma Malam Zubairu ya rufe ido ya ce ba’a gidan shi zasu kwana ba.

Sai da aka gama cire kayan su tas a gidan, aka dasa ƙwaɗo a ƙofar, kowa ya watse gurin ya rage su biyu, ga shi lokacin ana kiran sallan isha.

Ganin yanda Meerah ke rawan sanyi ne ya sa Meemah tashi da wuri ta ɗauko bargon su, rufe mata jikinta ta yi tana cewa. “ Ina ki ka saka inhelan ki.”

Cije labba ta yi tana cewa. “ Yana handbag dina.”

Ɗauko mata ta yi tana saka mata a baki, a hankali ta ja tana ɗaura kanta a kafaɗar Meemah.

Sun dade a zaune a gurin kafin Meerah ta tashi tana cewa. “ Kin ga dare yana yi, kizo mu nemi inda zamu kwanta zuwa gobe, kinsan akwai barayi da ƴan shaye-shaye.”

“ To Meerah ina zamu je?.”

Murmushi ta yi tana kama ta, kana ta ce. “ Muje school mu ƙwana, mu ɗiɓe kayan sawan mu da wani abun buƙatar mu muje, kinga dama katifar ba namu bane shi ya sa bai fito mana da shi ba, iya kayan mu kawai ya watso mana.” Sai kuma ta dafe kanta tana cewa. “ Wallahi na gaji da surutun nan.”

“ Sorry.” A cewar Meemah, kafin suka shiga tattare kayakin su, mai adaidaita sahu suka tara, suka zuba kayakin su a ciki kafin suka hau.

Ƙwatance Meemah ta masa inda zai kai su, wato unguwar Dosa, a ƙofar wani gida suka tsaya, ta ciro dari uku ta basa, ya ciro musu kayakin su kafin yaja machine nasa ya bar gurin.

Kallon juna suka yi kafin Meemah ta ce. “ Mu ajiye kayan mu sai mu wuce hostel mu ƙwana.”
Chapter 2 · 0% Book details