Sashe 9
Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da kyar Aziza ta ɗaga Hajja ta shigar da ita bukkarta tana lallashinta amma ina Hajja ta kasa tsaida hawayenta, kasa juran kukan nata Aziza ta yi ta miƙe a hankali ta fita zuwa randar kasar dake tsakar gidansu ta ɗibo ruwa a kwarya ta bude bakinta ta zuba abu a ciki sannan ta koma ta ba wa Hajja, ƙin karba Hajja ta yi ta ci gaba da kuka, Aziza ta ce
"Dan Allah Hajja kiyi shuru ki daina kuka, kin ga gidan nan bamu da sauran ganyen magunguna balle na haɗa miki ki sha idan kanki ya fara ciwo, zan yiwa Azima magana ga ruwan nan ki sha zuciyarki ta yi sanyi" da kyar Hajja tasa hannu ta karbi ruwan ta sha, tana shan ruwa ko minti uku bata yi ba, ta zube a jikin Aziza, hawaye ne masu zafi sosai suka zubowa Aziza a fuskarta a fili ta ce
"Kiyi hakuri Hajja ki yafe min ba zan iya ci gaba da kallon kukanki ba, baccinki shine mafi alkhairi, tun a yau da ba ki san su waye mu ba kina irin wannan kukan ran da kika sani za ki hadiyi zuciya ne Hajja? Ina ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan iya rasaki ke da Baffana ba! Zan ci gaba da boyewa tare da dakatar da yar uwata, ko da kuwa zamu kashe juna" Aziza ta karasa maganarta tana sake rungume Hajja, ta sha kuka sosai kafin ta gyarawa Hajja kwanciya ta fita.
sallama ta yi a bukkan Baffa, da sauri Baffa ya share hawayensa ya ce
"Shigo Aziza" cikin natsuwa ta shigo,zama ta yi kusa da kafarsa ta ce
"Baffa kuka kake yi?" girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"A'a ba kuka nake yi ba Aziza" shuru Aziza ta ɗan yi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Baffa
ina so na san meke ƙunshe da wannan zaren da Azima ta saƙa"
"Me kuma kike so ki sani bayan wanda na gaya miki Aziza? Hatsarin da ke cikin wannan zaren ba zai faɗu a baki ba tsananin yawanta, da ace za a dauki kwaya ɗaya tak! A jefata a cikin rafin jimulo, ina mai tabbatar miki duk wanda ya sha ruwan wannan rafi zai mutu!" dam! dam! dam! gaban Aziza ya bada nan ta shiga saƙe-saƙe a ranta tare da tunane-tunane, shin wa Azima take son kashewa da wannan zaren? *"BAFFA"* wata zuciyar ta bata amsa da sauri ta miƙe tsaye a firgice tana zare ido tare girgiza kai gami da fadin
"A'a karya ne! Ba zai yu ba! Ba zan bari hakan ta faru ba!" ganin yadda ta ruɗe lokaci ɗaya ne yasa Baffa tashi da sassarfa ya kama hannunta ya zaunar da ita ya ce
"Aziza natsu mana! Tsaya...kina ji? Menene? Gaya mini? Miye ba za ki bari ya faru ba?" kuka Aziza ta fashe da shi mai tsanani tana kwanciya a jikin Baffa, sosai hankalin Baffa ya tashi yana tambayar Aziza meke faruwa!.
Cikin kuka Aziza ke faɗin
"Me yasa! Me yasa! Me yasa!" da kyar Baffa ya shawo kan Aziza ta yi shuru ta daina kuka, Baffa ya ce
"Aziza meke faruwa ki gaya min gaskiya karki boye min komai, ni mahaifinki ne" saita natsuwarta Aziza ta yi ta ce
"Baffa, haihuwarmu ta yi muku rana?"
"Subhanallahi! Wannan wace irin magana ce kike faɗi Aziza?"
"Baffa kukan da Hajja ta yi a kan Azima dazu bazan sake bari hakan ta faru ba, ba zan sake bari ba!" ajiyar zuciya Baffa ya sauke,ita kuwa Aziza ta yi hakane dan kawar da shakku a zuciyar Baffa, shuru na ɗan wani lokaci ne ya ratsa wajan kafin Aziza ta ce
"Amm Baffa? Taya za a lalata zaren saƙar danar da yake hannu Azima?"
"Wannan ba shi bane abunda nake tunani Aziza, yadda aka yi Azima ta samu zaren nake tunani"
"Amm amma Baffa ta ce inda ake samu ta samu! Ya matsayin hatsarin jejin lore yake?"
"Aziza faɗin hatsarin jejin lore ba zai yu ba, dan yafi karfin ki fasalta shi da komai, taya har Azima zata shiga wannan ƙasurgumin jejin ta fito tana yar adam? Wannan shine tambayar da nake yiwa zuciyata amma na kasa samun amsa, ban san meke shirin faruwa da mahaifana ba"
"Baffa ka rabu da maganar Azima, kasan wani lokaci ba hankali gareta ba, yawwa kuma Baffa na mance ne ban gaya maka ba, Azima kamar tana da aljanu! Dan cikin dare sai na dinga ji kamar tana ta buge-buge da sambatu ita dayanta, Baffa na tabbata su ne suke saka ta rashin kunya,kuma ba mamaki karya take yi ba ita taje jejin lore ba, sai dai idan aljanun ne suka je suka kawo mata, ka yarda dani Baffa gaskiya nake gaya maka" Aziza ta karasa maganarta tana riƙo hannun Baffa, jinjina kai Baffa ya yi ya ce
"Kenan wani irin aljanu Azima ke da shi? Wanda har zasu iya kawo mata zaren saƙar dana? Me zata yi da shi? Kuma har tasan yadda ake saƙata?" zare ido Aziza ta yi ta hau rawar murya tare da in'ina
"Amm....eh.....umm....ohh...Baff....Baffa ....kar...ka...da..mu...da...Azima...ni nan zanji da ita, zan mata hayaƙin aljanu zata warke da yardan Allah na san ka yarda dani ko Baffa?" murmushi Baffa ya yi yana jin kaunar Aziza a cikin ransa, hakika ba zai ce baya son Azima ba tunda ita ma ƴarsa ce, amma aka ce mai kyautata maka shi ne wanda yake rayuwa a cikin zuciyarka,
"Na Yarda da ke Aziza, Allah ya miki albarka" murmushi Aziza ta yi ta miƙe tsaya tare da fadin "Amin Baffana" fita ta zo yi a bukkan har ta duƙa sai kuma ta ɗago tare da juyowa ta ce
"Amm Baffa? Baka faɗa mini abunda zai iya lalata zaren saƙar dana ba?"
"Aziza sanin wannan ba sauki garesa ba, har sai an koma jejin lore, jejin da mutane ba su shiga"
"To amma Baffa kai a garin yaya ka shiga ka fito?"
"Tsoron tarihi ne Aziza, kun dai sannin a matsayin mahaifinku! Amma har kwanan gobe baku da tarihin mahaifinku, na sha miki alƙawari zan baki tahirin jarumtar mahaifinki! Abunda yasa bana son faɗi yanzu sabida jarumtar bata jawo min komai ba sai babban kuskure"
Da sauri Aziza ta dawo ta zauna ta ce
"Baffa kamar ya? Dan Allah ka gaya min"
"A'a Aziza dama kin tashi kin tafi ne da ya fi miki alkairi, dan ba zaki ji komai ba a yanzu" ganin yadda Baffa ya yi maganar yasa Aziza miƙewa a hankali ta fice, tana fita ta koma bukkansu tana tsaye tana ta saƙa da warwara, a fili ta ce
"Kenan domin dakatar da Azima nima sai naje jejin lore? Idan kuwa hakane! *yau din nan zanje domin dakatar dake, amma kafin nan sai kin gaya min wanda kike hari da zaren sakar Azima!" Aziza ta faɗa tana harɗe hannuwanta.
🍃🍃🍃🍃🍃
Zaune suke a fadar sarki Chubaɗo, da sauri Maga Isar da saƙon kwana ya zo ya zube a gaban sarki ya ce
"Ranka ya daɗe! Sako ce daga yankin ja'i" da sauri wa inda suke zaune a wajan suka mai do da kallonsu kan Maga Isar da Sako, wazirin kwana ya ce
"Maga Isar da sako, buɗe ka karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuta" jiki na rawa Maga Isar da saƙo ya zo zai buɗe sakon sarki Chubaɗo ya dakatar da shi da cewa
"Dakata! Maga Isar da Saƙo, wannan saƙo ba na iyakar mu na nan kawai za a karanta ma wa ba, a'a yanzu maza kuyi aike a tara mutane,kuje ku sanar da Mai unguwa Ori, ku kira Arɗo tare da Baffa Mandi, da Magaji Bawa duk a hallara yanzu" Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya mike da sauri dan isar da saƙon sarki chubaɗo.
A cikin yan mintuna ƙalilan kowa ya hallara a fadar sarki Chubaɗo , kowa yana fargaban kar yankin ja'i ace sun rubuta ba zasu taimake su ba.
Bayan kowa ya bada hankalinsa sarki Chubaɗo ya ce
"Maga Isar da sako karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuto" Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya buɗe wasikar yankin ja'i ya fara karantowa kowa naji.
" _Wa'alaikumussalam, da fatan yankin kwana su na lafiya? Ya kuma fargaban iftila'in da ku ke ciki? Kashh! Ayya! Allah Sarki! Wasikarku ta iso garemu na neman taimako! Tunda har yankinku ya duƙawa tamu yankin,mun yarda zamu taimaka muku da Innu Maciji! Zai zo gobe, amma abun mamaki ace kuna da mutum a yankinku kamar Magaji Bawa har sai kunzo yankinmu neman taimako? Koma miye daukakarmu ce, tunda yankuna yanzu zasu shaida kun watsar da makamanku wa yankinmu, saƙo daga yankin ja'i, mun karb'i ƙudirinku!_"