← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 61

Sashe 16

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Ganin yadda Azima ta tsaya yasa Aziza faɗin
"Azima lokaci ya yi da zaki saduda! Ki dakata haka" murmushi Azima ta yi tana yiwa Aziza kallon baki da hankali
"Ni kike cewa na saduda? To naji zan saduda, amma bayan na kashe Baffa!" ta faɗa tana cije baki, Aziza ta ce
"Wai ke wace irin dabbace Azima?" murmushi Azima ta kuma yi ta ce
"MACIJIYA! ina kina tambaya ne wace irin dabba ce ni? To ni Macijiya ce kamar ke amma bambancin shine ni muguwa ce ke akasin haka! Har yanzu ban huce da abunda kika min ba, ki bar ganin kinsa jikina ya yi sanyi kin kafar min da dafina! Ba shi zai dakatar dani ba, na iya yau ne kawai, amma gobe zan haɗa da kisan da banyi yau ba!" Aziza ta jinjina kai ta ce
"Kin sha fadamin idan na isa na dakatar dake! Ni kuma na sha fada miki cewa bazan bar hakan ta faru ba, shine zan kara nanata miki, ba zan bar hakan ta faru ba! Dan haka muje gida, kafin Hajja ta titsiyemu da tambaya!" a hankali Azima ta juya tana dafe kirjinta dan abunda Aziza ta tura mata ya shigeta sosai, a hankali suka jera suna tafiya dan Azima na da bukatar ta kwanta dan jikinta da ya mutu, sabida abunda Aziza ta tura mata a hankali yake bin jikinta yana kashe mata shi, dan makarin dafi ta tura mata.

       Da haka suka iso kofar gida Aziza ce ta fara shigewa da sallama ta samu Baffa da Hajja suna zaune yana labarta mata wasikar yankin ja'i wanda kaff abunda Baffa ya faɗi a kunnen Azima, a tana rarrafawa da kyar amma wani dadi ne ya mamaye zuciyarta nan ta hau murmushi tare da fadin
"Yankuna uku zasu yaƙe yankin kwana? Wayyooo Dadi!bari na ɗan daga kafa dan ganin yadda za a shafe yankin kwana idan ya so na kashe Magaji Bawa daga baya!" ta faɗa gami da sallama ta shiga gidan, Hajja ta ce
"Azima ina kika je ne? Ni anya jiya na ganki kuwa? Yana ganki haka kamar wacce bata da lafiya?"

"Kin ganni mana Hajja! Ko dai wannan bala'in ne yasa kanku ke da Baffa ya kama da wuta!? Sannan da kika ganni haka ba wata matsala bace babba kaina ke ciwo, da nayi bacci na farka zan dawo dai-dai" Azima ta fada tana kallon Baffa, da ido Baffa yake bin Azima yayinda take yi masa wani irin kallo, Hajja ta ce
"Allah ya kyauta, jeki kwanta" Hajja ta shige bukka, Azima ta juya kenan zata shiga bukka idon Baffa na kanta dan ya kasa kauda ido a kanta, wuyarta taji ya mata ƙaiƙaiyi tasa hannu ta sosa, tana sosawa sai ga sab'ar maciji ya fadi carab a idon Baffa, wani wawan firgita Baffa ya yi,ya tashi jikinsa na rawa ya karasa ya dauki sab'ar yana kalla,saurin girgiza kai ya yi yana fadin
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! Me hakan ke nufi?" jikin Baffa ya yi mugun sanyi dan ya tsorata ba kadan ba, bukkarsa ya shige yana jeka ka dawo dauke da fatar a hannunsa, cikin rawar murya ya ce
"me ya kamata nayi? Dole na haɗa maganin ganowa idanuna, amma kafin na samu furen surfa sai naje jejin gangare, kuma kafin na dawo sai na samu kwana biyu sabida dogon tafiya ne ban ci ta zama ba, In sha Allahu zan tafi gobe" yana gami fadi ya fito ya shiga bukkar Hajja ya gaya mata gobe da safe zai tafi jejin gangare Hajja ta ce
"Me zaka je yi?"
"Akwai maganin da nake son haɗawa ne, kuma furen da ganyen dole sai naje jejin gangare"
"To Baffa yan biyu Allah ya kaimu lafiya" Baffa ya amsa da amin ya fice, bai zarce ko ina ba sai wajan Ardo bai boye masa komai ba kasancewarsa mahaifinsa ya gaya masa komai, sosai hankalin Arɗo ya tashi ya kallesa ya ce
"Magaji bana so ka gaya ma kowa wannan batun ka ji ko? Har sai ka tabbatar" Baffa ya gya ɗa kai cike da damuwa, nan suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin.

    🐍🍃🐍🍃🐍🍃

COMMENTS AN SHARE
BY MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*STILL FREE..*
🅿️==1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣

Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba, riƙe kai Aziza ta yi tare da furta "YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala'i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama'ar mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!" Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta iske wata budurwa kwance bakinta sai  jini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota, tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu tana furta "AZIIIMAAAAAAA!!!?" da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue.

      Duk inda Aziza take tunanin zata ga Azima amma da ta je sai dai ta iske gawa, hakiƙa fadin yadda  hankalin  Aziza ya tashi b'ata lokaci ne, ga shi ta rasa yadda zata yi, bata kara shiga ruɗu ba sai da ta yi gamo da gawar mutum takwas wanda Azima ta kashe, daga karshe Aziza ta koma tayi zaman yan bori.

         🍃🍃🍃🍃

*YANKIN JA'I.*

a lokacin da garkuwan fulanin yakin kwana suka isa yankin ja'i da gawar Innu Maciji hakika sun ga tashin hankali, sun ga masifa da bala'i a wajan jama'ar yankin ja'i, ko kaɗan sarkin fulanin yankin ja'i wato Jawo da kuma mai unguwa Sodangi da sauran duk wanda yake yankin ja'i basu tsaya sun saurari su Garkuwan fulanin kwana ba, suna isa da gawar fadar sarki Jawo nan yankin ya ɗauka daga tafiyar Innu Maciji yau yankin kwana sun kashesa, nan jama'ar yankin ja'i suka janyo wuƙaƙe da adduna da sanda kokara,suka yi kan su garkuwan fulanin kwana tare da fadin su ma ba za a barsu a raye ba, Galadima da Liman suka ce yadda suka tunzura gwanda kawai su gudu, garkuwan fulanin kwana ya ce bai kamata su gudu ba tare da sun musu bayanin abunda ya faru ba" Galadiman fulanin kwana ya ce
"Baka da hankali ne garkuwa? Ka ga yadda suka haukace suna ihu ka ce mu tsaya musu bayani taya zasu sauraremu? Ka zo kawai mu gudu dan ceton ranmu daga baya idan suka yi sanyi sai mu dawo! Amma kaga yanzu suna abu kamar wa inda mahaukacin zaki ya cije su" Garkuwa ya ce
"A gaskiya ba zamu tafi ba tare da munyi musu bayani ba,tunda duk abunda ya faru mu muka ja wa kanmu! Da ace mun bi shawaran Magaji da ba haka ba"
"Amma dai garkuwa kasan rashin hakuri irin na yankin ja'i da haukarsu ko? Ka zo mu gudu idan ba haka ba zasu iya kashe m...." maganar da Liman bai karasa ba kenan yaji saukar dutse a goshinsa,nan ya riƙe goshin yana faɗin "Ya Rabbi!" kafin su Garkuwa su dago nan suka ji ihu, inda gaba daya ahalin yankin ja'i mata da mazansu kowa ka gani da makami nan suka yo rututu suna shirin kai wa su Garkuwa farmaki,nan suka hau musu ruwan manyan duwatsu kafin su isosu,ganin haka yasa Galadiman fulanin kwana da Limamin fulanin kwana suka kwasa a guje dan tseratar da ransu, sauran mutum biyar na fada mutum uku su ma suka arce da gudu aka bar Garkuwan fulanin kwana da mutum biyu na fada su uku kenan, kafin Garkuwan fulani ya yi kokarin faɗin wani abu tuni, an rufesu da duka da sanda, yayinda ƙanin Innu Maciji yasa adda ya sare daya daga cikin ɗan fada a wuya yana sare san nan ko minti daya bai yi ba yace ga garinku, ganin haka yasa garkuwan fulanin kwana yace shi da dayan ɗan fada su gudu, da kyar suka kwace suka hau dokinsu ba shiri suka sab'i hanya jikinsu jina-jina da jini, dan garkuwa ma kam an saresa a hannu.
Chapter 16 · 0% Book details