Sashe 57
Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️=6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣
"Wlh Baffana bani bace! Wlh ban yi yunkurin kasheka ba!" gya ɗa kai Baffa ya yi yana shafa kan Azima ya ce
"Na sani Azima" riƙe Baffa tayi gam tana kan ci gaba kuka, nan al'umman yankin kwana suka hau hamdala ana taya juna murna, wa inda sukayi wauta da farko ta hanyar dukan Aziza suka hau ba wa Baffa hakuri yace shi kam ya wuce a wajansa, nan aka zauna ana ci gaba da jajinta lamarin, lokaci zuwa lokaci Azima tana ɗaga ido ta kalli Almazeen wanda yake lullubi idonsa a lumshe bai san hayaniyar da ake yi ba.
Maga isar da sako ne ya shigo da sallama yace Sarakunan Yankuna da Muƙarrabansu sun fara isowa da wani lokaci za a fara fafatawa?" Baffa ya ce
"A shirye nake, amma a bar fafatawar sai anyi sallar la'asar da yamma kenan, a ƙara shiryawa mutanen yankuna wajan zama mai kyau da abun motsa baki dan kar su gajiya, sannan a dama musu nono mai kyau a tabbatar an basu isasshe ba ƙasasshe ba" Maga Isar da saƙo ya amsa da to, sannan Baffa yace
"Mu tafin ku dan a kara shiri" dukkansu suka fice aka bar Nawaz da Azima da Aziza, Azima idonta na kan Almazeen wanda lokaci daya taji zuciyarta ta harba da shi, a yanzu yana cikin wannan halin ne sabida ita, wani kuka Azima ta kara sakawa tana rufe fuskarta da sauri Aziza tasa hannu ta riƙo hannunta tana fadin
"Haba Azima miye haka? Godiya zakiyi wa Allah dasu Mom da Hamma Mazeen" cikin kuka har tana sheshsheƙa ta dago idonta wanda yanzu ya koma daidai amma dik da haka basu da baƙin ido ta kalli Aziza tana girgiza kai ta daga hannuwanta hawaye na zuba ta ce
"Aziza! Ni! Wai ni da kaina na ke son kashe mahaifin da ya haifeni! Wai ni da kaina na rayuwa bana bautar wanda ya halicceni! Wai ni da kaina mutane suka shiga masifa da tashin hankali! wai ni da kaina na maida yar uwata ta biyuna macijiya! Wai ni da kaina....!" kuka yaci karfinta da sauri Aziza ta rungumeta tana bubbuga bayanta itama tana kuka
"Taya zan manta da wannan abun a rayuwata! Kenan mu haka kaddararmu take!" ɗago fuskarta Aziza tayi tace
"Karki yi sab'o, ki godewa Allah, sannan duk abunda kika lissafa ai bake kikayi ba Banju ne ya yi, dan haka ki bar fadin haka Sis" cikin kukan tausayi da Azima ta kasa tsayarwa tace
"Amma da jikin wa!? Da fuskar wa?"
"Koma da miye ne komai zan zama tahiri, ki ta nanata kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yafi wannan sambatun da kikeyi dan bana so,kina ji na ko?" Azima ta gya ɗa kai hawaye na kan sauka tana kallon Almazeen wanda Nawaz ke riƙe da hannunsa yana ji kamar yasa kuka dan tausayinsa, zuwa can da suka gama kukan Nawaz ya kalli Aziza ya ce
"Tashi mu tafi watakila yanzu kam ana can filin yaki, zo muje karo na farko a rayiwata naga yadda ake faɗa tsakanin mutum da aljan" tashi Aziza tayi ta kalli Azima tace
"Ki kula da kanki da kuma Hamma Mazeen uhum?" Azima ta gya ɗa kai, Nawaz da Aziza suka fita, suna fita Azima ta miƙe a hankali ta karasa jikin gadon ta kwanta a kusa da Almazeen har yanzu jikinsa da zafi sosai, tana kwantawa ta kama hannunsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta ɗora hannunsa a fuskarta ta lumshe ido.
⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️
Hakika su Mom sun sha mamakin ganin mutane him a wannan alkarya, mutanen yankuna sun zo daga yankuna daban-daban, jama'a an cika ana kallo, Aziza na zaune kusa da mom, Nawaz yana gefen hannun hagunta, ya ce
"Mom wlh naso ace sultana tana nan da ta ga abunda take kalla a zahiri a tv" mom tayi murmushi.
A hankali Baffa ya fito yana riƙe da zureren takwabinsa wanda ya kashe Banju da shi a karon farko amma wannan karon bai yi amfani da zaren sakar dana ba, dan ko ya koma jejin lore ba ba shi za ayi ba,amma duk da haka yau sai ya kashe Banju da yardan Allah.
Kunce Banju Baffa ya yi, Banju yana ganin takwabin hannun Baffa ya ce
"Magaji! ka ajiye takwabin nan ba da shi zamu gwabza ba" murmushi Baffa ya yi ya kalli Nawaz ya miƙa masa takwabin, zuwa Nawaz ya yi ya karba yana riƙewa sai da yaji damtsen hannunsa ya girgiza, kara sarawa Baffa Nawaz ya yi sannan ya koma ya zauna.
Banju ya kalli Baffa ya ce
"Ba kai ka yarda da kanka ba?to inaso ne mu gwabza da karfin-karfi,ni aljani ne faɗa da aljani kuma ba dadi" jan kafa baya Baffa ya yi ya ware hannunsa ya ce
"Bar ganin ka ƙereni a tsayi da girman jiki! a haka na daureka na kasheka a farko, ni mutum ne amma ba irin wanda kake tunani ba na san kasan da haka" Baffa na fadi ya hau tada guguwa, ganin haka yasa Banju wani juyi ya koma wani shirgegen Maciji🐉 blue mai matukar kauri da girma, wayyo karka so ka ga yadda wasu daga cikin masu kallo aka watse daga ciki kuwa har da mom, dan tace wlh wannan kallo ba da ita ba.
Kokarin sara Banju ya hau kai wa Baffa Baffa na b'acewa a cikin iska, yayinda masu kallo aka kara ja baya ana darewa ana basu fili dan yau abun babba ne, an gwabza sosai tsakanin Baffa da Banju, da ya ga tabbas ba fa zai samu galaba a kan Baffa ba nan ya yanki wajan jama'a yana shirin ya kai musu sara dan kuwa ya tabbatar da Magaji zai kashesa! to dan haka a cikin wa innan dibbannin alumman gwara ya shafe ko da rabi ne, nan ya yi kansu gadan-gadan ganin haka yasa Nawaz fizgar hannun Aziza suka sa gudu tare da mutane, ganin yadda Banju ya yi kan alumma yasa Baffa haɗa hayaki ya kwashe mutanen ya zubar dasu gefe, jelarsa Banju yasa zai kwashi wasu kafin ya kwashe Baffa ya kuma kwashesu, ganin haka yasa ya buɗe bakinsa zaiyi musu b'arin ambaliyar wuta cikin hanzari Baffa yayi wani tsalle ya tashi sama, dan kuwa idan Banju yayi b'arin wutar nan za a mutu dayawa, kafin Banju yayi tuni Baffa ya haye saman kansa tare da zaro wani wuƙa ya dab'awa Banju a tsakiyar kai, cak Banju ya tsaya, a hankali ya fara sulalewa yana zama mutum har ya zama mutum gabadaya, yana gama zama mutum Baffa na zaune a saman wuyarsa da karamin wukar da ya dab'a masa, tsalle Baffa ya yi ya sauka daga wuyar Banju ya dirƙo akan kafafunsa ya juya baya ya maida hannunwansa ya rungume a bayansa.
Da kyar Banju ya ce
"Wuƙar Dafi!" Banju na faɗi wukar ta narke a cikin kan Banju ta b'ace bat, dan kuwa ba wuƙa bace kamar sauran wuƙaƙe, Baffa ne ya haɗa da hannunsa dan zuwan wannan rana, sharabbbb!! Banju ya zube a kasa, nan take ya kama da wuta har sai da yaci ya ƙone ƙurmuss!! Hamdala da Wani ihu da guɗa da al'umma suka saka suna fadin
"Magaji! Magaji! Magaji!" suna daga hannu, wani hawaye ne ya tsiraro daga idon Baffa, da gudu Aziza ta tashi ta zo ta rungume mahaifinta tasa kuka, shima Baffa tamkar an cire masa wuƙa a maƙoro haka yakeji, Nawaz ne ya taso ya zo shima Baffa ha rungumesa, sannan ya karbi wuƙar ya damƙawa Aziza a hannunta yace a mallamaka mata dan tare sukayi yaƙin, nan aka kara sa ihu ana kabbara kafin kace me an daga baffa sama ana ambatar sunansa, sarki chubaɗo mai unguwan yankin kwana ori da kowa na yanki kwana murna sukeyi harda hawayen farinciki, sauran yankuna kuwa ji sukeyi ina ma ace Magaji a yankinsu yake, ko ba komai zasu samu karramawa da girmamawa da daukaka daga sauran manyan yankuna, haka aka dinga miƙawa Baffa hannu ana jinjinawa jarumtarsa.
Da kyar suka saffe sukayi sallar magriba, wasu yankuna wa inda basu da nisa sai sun koma yankinsu wasu gobe zasu koma.
Ranar yankin kwana wasai, duk majalisa kuwa hiran Magaji Bawa ake yi da yaransa Azima da Aziza, Jauro kuwa dan kunya da tsangwaman da ake masa yasa ya kasa fitowa.
Washe gari bayan manyan yankuna sun karrama Baffa nan suka gaya masa ai a yankuna yanzu babban yanki shine yankin kwana, bayan an gama komai suka yi masu sallama, godiya sosai jama'ar kwana sukayi ma wa inda suka samu damar halartan wannan gayyata ta fafatawa.
Bayan kwana uku da faruwar hakan komai ya zama daidai alhamdulillah Ma sha Allah.
Yanzu Baffa ya maida hankalinsa a wajan yiwa Almazeen magani, sai da Almazeen ya shafe sati curr kafin ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa, a wannan lokacin su mom sunyi sabo da mutanen kauyen kwana fiye da tunanin mai tunani.
Washe garin ranar da al'mazeen ya farka nan sarki chubaɗo ya tara su yace yana da magana, bayan kowa ya haɗu nan yake shaida bukatarsa na son sauƙa a kan kujerar mulkin yankin kwana, sannan ya bayyana Baffa a matsayin wanda zai mulke yankin kwana, girgiza kai Baffa ya hau yi kafin yace a'a tuni alumma sukace sunji sun gani, babu yadda Baffa ya iya dan kuwa bai so ba amma kowa ya nuna yana son Baffa ya mulke yankin kwana, haka sarki chubaɗo yasa aka rubuta sakon gayyata inda yankuna suka ce zasu zo, dan za ayi bikin da ba a taba yi ba na al'adun fulani.