Sashe 48
Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Fansa kuma!? To kiyi hakuri yau aiki ne ya min yawa a office,nima wuni nayi ina tunaninki kuma babu ta yadda zanyi magana dake shiyasa na siya miki waya da zan dawo, zancan kuma nuna damuwa a kaina ba mamaki ni ɗin na musamman ne!" gaban Azima ne ya faɗi amma da shike tana zumudin waya yasa bata bada hankalinta a kan fadin da ya yi cewa shi ɗin na musamman bane.
Wayar ya nuna mata amma yace ba zai bata ba har sai ya mata chajinsa, jakar hannunsa ta karba, ya yi gaba tana binsa a baya idonta kyam a kansa,gani take kamar akwai wani mugun haske dake fita ta ƙeyarsa tare da wani farin mutum na mata kwala
"MAGAJI BAWA!" ta faɗa tana shirin kaiwa keyar Al'mazeen duka, juyowar da yayi ne yasa tayi saurin maida hannunta, ya ce
"Mene? Waye kuma Magaji Bawa?" haɗe rai Azima tayi ta ce.
"Tsohon abokin gabana ne"
"Abokin gaba kuma?" Al'mazeen ya faɗa cike da mamaki.
"Karka fiye tambaya" ta fada tana wucewa gabansa ta rigasa hawa, duk abunda sukeyi a kan idonsu Sumy:Sady:Maman Hanan:Maman Beenah:Hanan: Sumy tace
"Muje kasa ku ga yadda zan tsara wasan nayi cilli da shegiya wajen gate a daren nan" suka sauko a tare, suna saukowa, Sumy ta ware murya tana kwalawa Azima kira sai kace gidan ke ci da wuta, a lokacin Azima na tsaye a kan Al'mazeen dake jona mata wayarta a chaji, jin kira kuma Al'mazeen ya gane murya ya ce
"Sumayya? Sun zo ne? To meyasa take kiran Azima haka?" Azima wacce zuciyarta ya tunbatsa jin yadda ake kiran sunanta abun ya bata haushi, a tare suka sauko da Al'mazeen,ya kalli Sumy ya ce
"Sumy, Sady, yaushe ku ka zo? Sannan meya faru kike kiran Azima haka?"
"E mana,mun zo dazu, da muka zo na ba wa Azima kayana ta haura min da shi sama, na zo da sarƙata ta gwal amma yanzu na duba ban gani ba, da na shiga dakin kuma na ga Azima a jikin kayana ta bude min akwati har nake tambayarta me take yi sai ce min tayi babu komai nayi hakuri, ka dai ni ba saninta nayi ba banda yau" Maman Beenah ta ce
"Anjima ana yi mana dauki ɗaɗdai, amma dai bamu taba zarginta ba, kasancewar mun yarda da ita"
"Haka ne kam, nima na nemi sarkata wanda ka siya min ɗin nan ban gani ba" cewar Hanan.
Al'mazeen a rayiwarsa ya tsani mai halin b'era dan haka ya ɗago ido yana kallon Azima wacce jikinta ke rawa idonta sun ƙanƙace sun kara rinewa, harta hannunta ya fara sab'ulewa yana zama blue, cikin wani irin murya Al'mazeen ya ce
"Azima da gaske ne? Kin dauka mata sarƙa?"
Wani ihu da gurnani Azima tayi tasa hannu ɗaya ta damƙi wuyar Sumy, nan Sumy ta hau jijjiga kai jin an shaƙe mata magudanar numfashi, cikin daga murya Azima ta ce
"Faɗi gaskiya ko yanzu ki jiki a kabari! Kikace na sace miki sarƙa! Nayi miki kama da b'arauniya! Da ku ka sakani daukar kayanku na dauka!?" duk maganar da Azima take yi tana rike da makogoron Sumy wacce ke mutsil-mutsil idonta har ya fara zazzagowa, su Maman Hanan sai dambe sukeyi da hannun Azima a kan ta saki wuyar Sumy amma sun kasa koda motsi ne da hannun Azima, harta Al'mazeen ya kasa b'anb'are Azima daga cikin Sumy, cikin in-ina da shaƙewa gami da fitar hayyaci Sumy murya irinta wa inda suka sha azaba ko suke sha ta ce
"Wallahiii.....karya......na.....ke...yi...."
🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*JUMMA'@T MUBARAK*🕋
*PAID.*
🅿️=6️⃣1️⃣↪️6️⃣2️⃣
Sakin wuyarta Azima tayi tana huci,tana sakinta Sumy ta zube kasa a sume, cikin tashin hankali suka ɗagota,Beenah wacce saukowarta kenan daga sama dan dama bata nan akayi wannan show din, Mamanta tace
"Beenah! Hanzarta dauko ruwa a fridge" ganin Sumy a baje yasa beenah kwasa da gudu taje kitchen ta dauko ruwa aka yayyafawa Sumy, da karfi ta fizgi numfashi, ganin ta saki ajiyar zuciya yasa Al'mazeen ya fizgi Azima ya wanka mata mari, wani gurnani Azima tayi tasa hannu zata shaƙi wuyar Al'mazeen da hannu biyu amma tamkar an daskarar mata da hannu ne ta kasa, cike da mugun zuciya da mugun jin haushin kanta ta yi hanyar waje, ganin haka yasa Al'mazeen dafe kai yana ambatar sunanta amma kamar ba da ita yake yi ba.
Gate ta nufa da niyyar barin gidan, dan ta ga Alkadarinta yana gaff da karyewa, kamata ya yi ace ta kashe sumy dan ita duk wanda ya tabata hukuncinsa kisa ne! haka ma Hamma Mazeen da ya mareta, amma ta kasa aiwatar da komai,to me hakan ke nufi? ai gwara ta bar gidan kafin abunda take rayuwa da shi shekara shabiyar zuwa sha shidda a rabata da shi.
Al'mazeen ne ya biyota yana kiranta amma kamar ba da ita yakeyi ba dan ta zuciya, karamin kofar gate tasa kafa tayi kwallo da shi,ga mamakin mai gadi sai ganin kofa ya yi a kasa da sauri ya tashi ya matsa ya bata waje, tana sa kafarta a waje da niyyar fita kamar wanda wutar lantarki ta kama haka taji a jikinta, ji tayi kamar an ja kafarta akayi sama da ita sannan aka wurgota cikin gidan, sai da ta yi sama tukunna ta faɗa kan wani dutse kanta ya bugu, zare ido Al'mazeen ya yi yana fadin
"Azimaaaa!" da sauri ya yi kanta yasa hannu ya dagota, harta baƙin tabarau dinta sai da ya fadi, a lokacin da Al'mazeen ya matso gareta ta rufe ido jin yadda wani mashahurin jiri dake kwasarta dan kanta ya buge sosai, cikin tashin hankali Al'mazeen ke fadin
"Subhanallahi! Azima! Azima! Azima! Dan Allah kiyi hakuri ba da nufi bane,meya sameki?" jinta shuru ba motsi yasa ya dauketa cak ya koma da ita ciki, yana shiga har yanzu ana tsaye a kan sumy wacce bata gama farfaɗowa ta dawo hayyacinta ba.
Ganinsa sukayi ya shigo da Azima a hannun sai kace baby yana shirin sa kai ya haura sama,cikin masifa Maman Hanan ta ce
"Kai Al'mazeen! Wannan wani irin rashin hankali ne! Ya zaka dauko yar aiki haka a hannunka sai kace matarka!? A gabanka fa ta shaƙe Sumayya tana shirin kasheta amma baka dakatar da ita ba, zata bar gidan ka je ka dawo da ita, ga Sumayya nan dake bukatar taimako amma baka kalleta ba ka wani dauko wannan ƙidahumar jejin matarka ce ko aurenta zakayi! bayan kasan kuma su Sumayya da Sadiyya sune matan da zaka aura ko? ko dai akwai wani abu a tsakaninka da wannan daukar kaddaran ne?" (wai Azima ce daukar kaddara) rai a haɗe Al'mazeen ya juyo ya ce
"To auranta zanyi! Ta fiye min su Sumayya da Sadiyya sau dubu! Ina sumayyan ce ta jagaleta? Ita ma Azima ta suma,ku kai sumayyar sama bari na duba Azima tukunna,zan zo na duba Sumayyan daga baya" yana gama fadi ya hau sama ya bar su shanye da baki.
A gadonsa ya kwantar da ita yana dubata, gefen kanta ya gani ya ɗan fashe, hannu yasa da niyyar yi mata treatment ji ya yi ta riƙe hannunsa, kallonta ya yi ya ga har yanzu idonta a rintse yake, a hankali ta miƙe ba tare da ta kallesa ba tasa kai zata fita yayi saurin shan gabanta,
"Azima yi hakuri! Ki fahimceni ba da nufi na mareki ba, laifinki ne inata miki magana ki saketa amma kin ƙi ki
saurareni, taya zaki shaƙeta haka idan ta mutu me kike tunani zai faru? Ba ke kaɗai ba harta ni sai an kulleni dan anyi kisan kai a gidana! da kin kasheta sunanki fa zai koma criminal ne, kuma ba zan so hakan ta faru ba amma kiyi hakuri kinji? karki yi fushi" ya faɗa yana haɗe hannuwansa alamun roƙo,Azima kuwa juya kanta tayi gefe har yanzu taki yarda ta buɗe, yana gama magiyarsa ta rab'a ta gefensa ta fice, riƙe kai Al'mazeen ya yi yana jan ajiyar zuciya,box dinsa ya dauka ya fito yayi side din su Hanan, ya nufi dakin baki wanda su Sumayya suke zama idan suka zo, da sallama ya shiga har zuwa yanzu suna tsaye a kan Sumy, rai a haɗe fuskarsa ba annuri ya shiga, allurai ya yiwa Sumy sannan ya ɗora mata ruwa, nan da nan bacci ya kwasheta, kwashe box dinsa ya yi zai fita Maman Beenah ta ce
"Al'mazeen? Amma ina fatan batun auren yarinyar nan kawai ka faɗa ne ba da gaske kakeyi ba?"
Cak Al'mazeen ya tsaya ya juyo ya ce
"Da gaske nakeyi! Zan aureta! taya zan auri Sumayya? daga zuwanta yau ta bi Azima da sharri! Laifi biyu wanda na tsana a rayuwata! tayiwa Azima ƙarya da ƙazafin abunda bata yi ba,ƙazafin ma kuma na sata!" yana gama fadi ya fice, aka barsu da zare idanu.
Part dinsa ya koma, yana tajin babu dadi na ganin Azima tayi fushi, shirin bacci ya yi ya kwanta dan yana tashi sallar dare.
@@@@@