← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 61

Sashe 58

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda aka tanada haka kuwa ta kasance wajan karfe goma na safe aka fara bikin naɗa Baffa sarautar kwana, inda manyan yankuna da ƙananun yankuna duk sun zo, anyi walima Baffa ya samu alkairi ba ma iyakar shi daya ba harda jama'ar yankinsa, yankin kwana Allah ya ɗagata sama.

Wajan irinsu biyu haka aka kammala taro lafiya, an yanka su shanaye dasu kaji da zabbi an sha kindirmo, kai taro dai tayi saidai muce Allah ya taya Baffa Magaji Bawa Arɗo riƙo.

Da yamma Azima da Aziza suna zaune a bukkarsu, hajja kuma suna bukkarta dasu mom, bayan Aziza ta gama koyawa Azima karatu ta kalleta ta ce
"Aziza dama ina son na tambayeki" gyara zama Aziza tayi tace
"To inajin yar uwata" maganganun da Al'mazeen ya gaya mata a kunne ne take son Aziza ta fassara mata, dan ta kwashe maganganun tsaf a cikin kanta, dan haka ta gayawa Aziza tace ta fassara mata, dariya Aziza ta hau yi har tana riƙe ciki ta ce
"Inyee! Kin faɗa soyayya ne?" haɗa rai Azima tayi tace ban son wulakanci idan ba zaki gaya min ba sai naje na tambayi mijinki Hamma Nawaz ko naje na tambayi mom"
"Allah ya baki hakuri maida wuƙar" nan ta fassara mata abunda kalmomin ke nufi, wani murmushi Azima tayi tana rufe fuskarta da tafin hannunta, Aziza zatayi magana sukaji sallamarsu Nawaz sai da gabanta ya faɗi, su dai basu fito ba sunajin maganarsu dai a tsakar gida, Almazeen ne ya ce
"Mom ya kamata mu koma gida, dan muje mu dubasu mu ga lafiyarsu, barin ma mu da muke da asibiti" mom ta ce
"Nima na fara wannan tunani zuwa anjima zamuyi magana da Baban su Azizan" wani zaro ido Azima da Aziza sukayi bama su kadai ba harda Hajja, dan tasan za a kwashesu a tafi dasu ne tunda yara da mazajensu, kuka ta fara haɗiyewa, Almazeen ya kuma cewa
"Mom ina yaran naki suke? Ya kamata dai yau su zo su kai mu yawo mu ga gari" mom ta ce
"Hakane, Azima! Aziza!" a sanyaye suka amsa da na'am, barin ma Aziza damuwarta yafi bayyana ƙarara a fuskarta, a tare suka fito suka duƙa, mom tace
"Ku dauko mayafi kuzo ku kai mazajenku yawon ganin gari" amsawa suka yi da to suka dau mayafin dama dogon abaya ce iri daya a jikinsu, mayafinsa suka dauka suka rufa kansu da shi, a kofar gida suka samu Almazeen da Nawaz sannan suka hau tafiya babu mai cewa qala, duk inda suka wuce sai an bisu da kallon burgewa ganin yadda suke tafiya tamkar wasu taurari masu haska sararin samaniya.

Bayan sun kewaya dasu, Azima ta kalli Aziza tace
"Ukhty muje rafin jimulo" a sanyaye Aziza ta amsa da to, dan tun lokacin da taji anyi maganar tafiya jikinta yayi sanyi dan idan tace tana son komawa tayi babban karya, suna isa rafin wani iska mai dadi da yake kaɗawa ga ruwa farin sol abun burgewa ga ganyaye kore shar kwance a wajan,
"Wowww!" Nawaz da Almazeen suka furta, Azima tana satar kallon Almazeen, hannunta ya kama suka zagaya ta gefen rafin dan yana da bukatar suyi luv, dik da mugun kunyarsa takeji, suna barin wajan Nawaz ya maida idonsa kan Aziza wacce duk ta taburce kamar ma kuka take son yi, dan ita har yanzu bata taba ji Nawaz yace yana sonta ba, dan haka itama ba zata buɗe zuciyarta ba balle ta cutu, hannunta ya kama tayi saurin daga ido ta kallesa, janta yayi ya haɗata da bishiya murya a can kasa ya ce
"What's the matter?" girgiza kai tayi sai kuma hawaye suka biyo baya, hannu yasa ya goge mata yace
"Ba ki so ki koma ne ko?" shuru tayi, wani murmushi yaƙen takaici ya yi yana sakinta ya juya baya ya ce
"Na faɗi daidai shiyasa kika ƙi cewa komai?, karki damu duk yadda kike so kiyi, bcox u are free now" ya faɗa kamar a ɗan zafafe, rungumesa ta baya Aziza tayi tasa kukanta mai sauti, rintse ido ya yi ya ce
"Kamar dai na taba gaya miki bana son kuka ko? To sakeni!" sake riƙesa tayi, hannunta yaja suka isa bakin ruwan ya zauna ya zira kafafunsa a ciki, itama zaman tayi kusa da shi ta kamo hannunsa ta kifa kanta a kafadarsa, bata san lokacin da ta furta masa cewa
"Hamma Nawaz, ka taba ji kana sona? Ko kawai tausayina kakeji?" ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya fuskanceta yace
"Idan har zaki iya karanta abunda yake cikin idona, sannan ki auna bugun zuciyata" ya fada yana ɗora hannunta a saiti zuciyarsa dake bugawa da sauri
"Zaki iya ba wa kanki amsa, idan hakan bai samu ba, ki bari idan muka koma kd zaki tabbatar" daga haka bai sake cewa da ita komai ba banda rungumeta da yayi.

💞💞💞💞

Almazeen suna zagayawa baya da Azima ya rungumeta sosai a jikinsa, rufe fuskarta tayi da kirjinsa tana murmushi tanajin wani bakon yanayi a tare da ita, sakinta Mazeen ya yi ya rungumeta ta baya ya ce
"Na gama haukacewa na susuce a kan son...." shuru yayi ganin tana ta wani aikin rufe fuska, bakinsa yasa a saitin kunnenta yace
"Wai ni wannan kunyar na miye ne? tinda na farka ake guduna, ko dan sabida daren...." bai karasa ba ta jiyo ta sauri ta rike bakinsa tana shigewa jikinsa, murmushi yayi yace to faɗamin
"Ana sona?" ɗago kai tayi tasa idonta a na shi ta ce
"Idan ban furta hakan ba na zama butulu! wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin tawa, miye ribata idan ban so shi ba, ance tukaicin so kauna, sabida haka ina kaunarka Hamma Mazeen" wani runguma Mazeen yayiwa Azima cike da so, kafin ya haɗe bakinsa da nata ya hau bata hot kiss, Azima tayi alkawari ba zata taba juyawa Mazeen baya ba kamar yadda shi ma bai juya mata ba a lokacin da take abun gudu a wajan mutane, shiyasa ko da yake romantic dinta bata yi yunkurin dakatar da shi ba, tsayuwa ce ta gagaresu suka zube kasa, murzanta yake yi cikin salo da shaukin kauna, Azima ganin hankalinsa ya fara gushewa ne ya sakata zare jikinta daga na shi,yayi saurin riƙota ta ce
"Don Allah Hamma, ka duba inda muke,kuma ma ai" sai kuma tayi shuru, saurin saita natsuwarsa Almazeen ya yi, amma gaskiya ba zasu kara sati a garin nan ba zasu koma dan ya samu yaji dadin bai ji ba a daren farko dan wuya kawai yaci.

Tashi yayi ya kama hannunta ya ɗagata tsaye, yace
"Muje gida" riƙesa tayi tace
"Kayi fushi ne?" ɗan murmushi yayi ya girgiza mata kai alaman a'a, wajan su Nawaz suka dawo har yanzu suna zaune a bakin ruwa yana rungume da Aziza, Almazeen ya ce
"To romio and Juliet muje gida lokacin sallar magriba yayi" Nawaz yace
"Okay Laila da Majnun" dariya Almazeen yayi dan zuciyarsa fari sol.

Gida Suka tafi, bayan sallar isha'i mom ke gayawa su Nawaz yadda sukayi da Babansu Aziza kuma itama tayi na'am da maganarsa na cewa a dan barsu Azima da Aziza tukunna, su zasu tafi gobe, Almazeen da Nawaz kamar su kurma ihu, Nawaz da gajen hakuri yace
"Har na kwana nawa?" mom tace ungo nan naka🖐🏻
"Har na tsawon wata daya,ni kuma nace a barsu suyi wata biyu tunda alfarma suka nema,kuma ai gaskiya ne tinda sun jima basu ne, yanzu kuma zama na dindindin zasuyi daku"
"Haba dan Allah mom, yanzu dake za a yanke wannan shawaran?" cewar mazeen,mom tace bana son rashin kunya, maza ku tashi ku fara shiryawa, a zuciye Nawaz ya fice Almazeen ya bisa a baya.

Washe gari asubanci sukayi, kaff jama'ar kwana aka fito yi musu sallama, Almazeen ne kawai yayi sallama da Azima inda ya jima yana tsotsar bakinta, Nawaz kuwa ya ƙi kallon Aziza dan yace itama harda haɗin bakinta dama ba son komawa take yi ba.

Baffa ya haɗawa su Mom kaya sha tara ta arziki yayinda suke zubawa juna godiya cikin mutunci da mutuntawa, haka Baffa ya rungumi su Almazeen da Nawaz, sukayi musabaha da Malam Yunusa da Alhaji Karami, su Inna wuro ma sunyi wa mom da Maman beenah abun arziki, mom tace
"Dan Allah wata rana ku kawo mana ziyara, da sunyi wata daya kuma mazajensu zasu zo su daukesu"
"In sha Allah" mota suka shiga aka dinga ɗaga musu hannu, da gudu Nawaz ya figi motar Aziza ta fito itama da gudu tana daga masa hannu ya hangeta ta glass din mota amma sai ya kara gudun motar, cikin rashin jin dadi tin daga Azima har Azizan suka juya jiki a sanyaye, a ranar haka suka wuni zuciyarsu babu dadi amma suna zuba hira da wasa da dariya da Hajjarsu,yayinda Yawuro ta fara musu gyara tana tsumasu dan tana so ace kafin nan da wata dayan nan sun sama zam-zam dasu, idan mazajensu suka kusancesu basu ba kara tunanin wata mace.

@@@@

Sabida gudun da suke yi yasa biyar na yamma suka fice daga jeji suka b'illa titi, yau ma sai da suka kara kwana cikin garin yola kafin da washe gari suka kama hanyar kd, suna isa mom ta kira sultana tace mata sun dawo, wani ihu da murna Sultana tayi a waya mom ta bata labarin abunda ya faru, bata gama ji ba zumudi yasa ta katse wayar ta kalli Khalil dake danna waya tace
"Dear su mom sun dawo" da murna a fuskarsa yace
"Alhamdulillah"
"Dear tashi mu tafi ina son ganin Aziza"
"Oh Allah sultana ki bari su huta sai muje da daddare"
"O'o ni kawai ka tashi mu tafi yanzu sai ka dawo ka daukeni da daddaren" ta fada tana buga kafafunta a kasa" hararanta yayi yace "ai saiki dauko mayafinki" kiss ta sauke masa akumatu tana godiya da gudu ta hau sama dan dauka mayafinta ta sauko a mota ta samesa ya tada suka nufi gidansu.

🍃🍃🍃🍃

MOMYN AHLAN✍🏻
GARKUWAR MACIZAI🐍😂
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Chapter 58 · 0% Book details