← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 61

Sashe 59

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*PAID.*
🅿️=7️⃣1️⃣↪️7️⃣2️⃣🔚🔚🔚🔚 ALHAMDULILLAH!.

Suna isa da gudu tayi cikin gidan tana fadin
"Oyoyo Mom! Oyoyo Anty Aziza!" mom dake zaune a parlour ta ce
"Sai dai ni Amma Aziza kam tana garinsu" turus sultana ta tsaya tace
"Bangane tana garinsu ba mom? Sakinta Yaya yayi?"
"Taya zai saketa? Ba yanzu zasu dawo bane sai sun kwana biyu,mahaifinsu ne ya roƙi alfarma a barsu" cikin rashin jin dadi Sultana ta zauna tace
"Wayyo wlh banji dadi ba mom, to ba komai Allah ya dawo dasu lafiya, inasu Yaya Nawaz da Yaya Almazeen?"
"Muna isowa basu zauna ba asibiti suka wuce"
"Ayya Allah Sarki! Ohh wayyo Mom na bar Khalil a waje ashe" Mom tace
"Shi dai yaso zaman waje ai khalil ba baƙo bane"
"Wlh kuwa mom kyaleta iyayi take ji da shi waya na tsayayi" cewar khalil da yake shigowa ya duƙa ya gaishe da mom ta amsa tana dariya,sultana tace
"Oh wato ma haka zaka ce ko? Ba komai ai"
"To dan Allah mom ki ji ni da 'ya fa, to me nace?" mom tace
"Ahh kai kam baka ce komai ba" khalil yayi dariya yana fadin
"Inasu Nawaz?"
"Sunje asibiti,ai muna isowa basu zauna ba"
"Ayya Allah Sarki, to bari na wuce mom"
"Ah to ita Sultanan fa?"
"Zan dawo na dauketa da daddare" khalil ya fada yana ficewa, sultana ta miƙe a dogon kujera tana fadin
"Ohh mom korata kikeyi?"
"To nan gidanki ne? Me zaki zauna ki min"
"To yau ma a nan zan kwana"
"ashe da rabon zaki kwana a wajan gate" mom ta fada tana hawa sama, sultana dakin Aziza ta shiga tana tuno abubuwa da dama har bacci ya kwasheta, kamar yadda Khalil ya faɗa bayan isha'i yazo ya dauki sultana, su Nawaz basu dawo ba sai wajan goma, sai da sukayi wanka kafin suka shiga wajan mom a lokacin tana waya a kawo mata 'yar aiki wacce zata dinga tayata aiki da zama dan ita daya ne, sai da ta gama wayarta ta fuskancesu ta ce
"Sannunku da dawowa fatan komai lafiya?" Almazeen ne yace
"E mom komai lafiya alhamdulillah! Amma muna kewan matayenmu,bamu san halin da suke ciki ba ,su ma basu san wanda muke ciki ba" mom tayi murmushi tace
"Haba dai ai wata biyu kamar kwana biyu ne a wajan ubangiji" sai a sannan Nawaz ya yi magana fuskarsa a haɗe
"Mom wata biyu kuma? Ba wata daya naji kince ba? Baffa ma fa wata daya naji yace" mom tace
"E wata daya ne nice nace suyi wata biyu" tashi Nawaz yayi zai fice mom tace
"Akwai abinci a dinning"
"Bana jin yunwa" yana gama fadi ya fita, Almazeen shi ma tashi yayi mom tace
"Kana nan ne tukunna?"
"A'a mom zan tafi gobe naje na duba asibitina nima, ba zan dawo nan kusa ba sai an kwana biyu idan zamuje kwaso matanmu" mom tace
"Ya kamata a haɗa musu lefe ayi shagalin biki, ya kasance kafin su dawo an tanada musu komai, da kuma gida wajan zama, shin a gidanka na kano Azima zata zauna? Kasan fa yanzu ba kamar da bane, Aziman yanzu ba jin dadin zama zatayi dasu Hajiya Lawiza da yaransu ba, Azima kuma matarka ce amanace a hannunka a san abun yi gaskiya" komawa Almazeen yayi ya zauna yace
"Mom ko da a kano na zauna da Azima wlh su Maman Hanan zasuje su takura mata, inaga gidan dake kasan unguwan nan zanje na taya naji, tunda babu abunda nake yi a kanon idan kuma ta asibitina ne ni zan iya zuwa ina kwana biyu ina dawowa" mom tace
"Hanya zai aureka kenan, to ba matsala Allah ya zaba mana abunda yafi alkairi, ka ga shi abokin naka ba shi da matsala a nan zasu zauna dani" Almzeen yace
"Ai hakan yafi mom shiyasa nima zan dawo cikin masu sona kawai" mom tayi murmushi, sun jima suna tattaunawa har wajan sha biyu kafin ya yiwa mom sai da safe ya tafi, a kwance ya samu Nawaz ya ɗora hannu a fuskarsa alaman tunani, zama shima ya yi, Nawaz yace
"An rabaka da matarka amma me ka zauna mom ke gaya maka? Ai wlh na fahimci mom idam na ci gaba da zama zata iya cewa su yi wata shidda ma" da sauri Almazeen yace
"Kamar kuwa ka sani cewa tayi sai sunyi shekara" wani zabura Nawaz ya yi yace
"She mene?"
"Shekara" Almazeen ya fada yana dariya, tsaki Nawaz ya yi, sai da mazeen ya gama dariyarsa kafin ya basa labarin yadda sukayi da Mom, Allah yasa mu dace, Nawaz ya faɗi tare da shigewa daki ya kwanta, amma kamar jiya ya kasa bacci dan kuwa sun bar wa juna abin tuni.

Ta bangarensu Azima da Aziza yadda mazajen nasu ke ji a kansu haka suma suke ji a kansu.

Da washe gari Almazeen na wanka dan zai tafi kano yau Nawaz na danna system, wayar Almazeen ne yayi kara yayi kara yana dubawa yaga Alisha
"Mayya!" Nawaz ya fadi a fusace yana ci gaba da aikinsa,jin kiran wayar takeyi babu fa shi yasa ya jawo wayar zai daga wata daraba ta faɗo masa, murmushi yayi tunowa da haukan kishin Alisha dan haka Nawaz ya daga kafin Alisha tayi magana yace
"Wai ke baki san yayi aure bane?"
"What!?"
"Yes daidaine abunda kikaji na fadi, yanzu baya yayinki! Idan kuma baki yarda ba zan gwada miki kiji dan ki tabbatar da abunda nake gaya miki sabida...." maganar Nawaz ne ya tsaya sakamakon fitowa da Almazeen yayi, Nawaz yace
"Allah ya taimaki Majnun na Azima! wai ni kam ina Alisha ne Almazeen?" mazeen ya riƙe kai yace
"Wlh nikam na ma mance da ita"
"Kar dai kace min bata san kayi aure ba?"
"Wlh bata sani ba,har shakkar gaya mata nake dan ban san yadda zata dau lamarin ba" Nawaz yace
"To ai ga shi sai ka gaya mata" ya fada yana mikawa Almazeen waya, wani zare ido Almazeen yayi Nawaz kuwa ko a jikinsa, ba yadda ya iya haka ya karbi wayar yana shirin yi mata bayani ta wankesa tass a kan cewa ya ci amanarta kuma babu ita babu shi, tana gama gaya masa ta ajiye wayarta.

"Me kenan kayi haka Nawaz?"
"Me kuwa nayi? Ita fa ta kira! Cika min kunne take,kuma ma ai taimakonka nayi" ya fada yana ci gaba da aikinsa, Allah ya kyauta Almazeen ya fadi Nawaz ya amsa da amin, yana gama shirinsa ya shiga ya yiwa mom sallama a lokacin an kawo mata wata mai aiki, Allah ya tsare ta masa ya amsa amin sannan ya shiga motarsa sai kano.

🍃🍃🍃🍃🍃🍃

Haka suka ci gaba da rayuwarsu amma hankalinsu yana kan matayensu wanda suma kullum acikin tunanin mazajensu suke, ga shi babu netwrk babu waya bare a ji muryan juna ko hankali zai kwanta, a daddafe akayi sati biyu, Almazeen yaji ina sam ya kasa hakuri ya tattaro yazo Kd yacewa mom zasu je dauko matayensu Mom tace aa suyi hakuri dai a cike sati biyun, da kyar sukayi sati uku hakurin Nawaz ya kare ya shirya tafiya ya cewa mom zaije kano, mom ta tambayesa lafiya kuwa yace mata lafiya lau kawai zaije bikin wani abokinsu ne dama kuma yana da tiyatan da zaiyi a can, Allah ya kiyaye hanya a dawo lafiya mom ta masa

Nawaz yana zuwa kano dama tare suka shirya tafiyarsu shida Mazeen nan suka dauki hanyar yola ba tare da sanin mom ba.

Sai da suka kwana da washe gari suka yanki jejin kwana, kasancewar Nawaz ya ƙware a driving musamman ta fannin gudu yasa wajan biyar suna cikin yankin kwana, tun shigowar motarsu yara suka hau bi, a lokacin kuma Azima da Aziza suna kwance a bukka Hajja tana gidan Arɗo, Azima ta tsokani Aziza, Aziza ta hau binta da gudu zata daketa kanta ko dankwali babu, a wannan gudun ne suka fito har waje daidai a kan idon Nawaz da Almazeen, ga shi sun wani kara bulbul dasu sun ciko, wani daci Nawaz ya hadiye yana wurgawa Aziza harara, ganin basu san da zuwan su bane yasa Nawaz danna horn da karfi a firgice suka juyo, ko wacce idonta a cikin na mijinta ya sauka, gaban Aziza ne ya buga ganin hararan da Nawaz ke binta da shi, ita kam shikenan ta shiga uku, ranar da zai tafi ba ayi rabuwar dadi ba, yau kuma ya dawo za a fara rigima,tukunna ma me ya kawosu? Ai ba yau bane ranar da ya kamata ace sunzo daukarsu, Azima ce tayi karfin halin murmushi duk da itama zata iya cewa ba yanzu bane ya kamata ace sun dawo daukarsu ba, Nawaz ne ya hangi wani ɗan fullo rataye da sandarsa a wuyarsa yana tahowa ga Aziza kai ba dankwali tsoro kuma yasa ta kasa gaba ta kasa baya, da sauri Nawaz ya fito a motar yazo ya ja hannun Aziza suka wuce gida, ganin Nawaz ya fita yasa Azima shiga motar da sauri tana yiwa Almazeen oyoyo.
Chapter 59 · 0% Book details