← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 61

Sashe 54

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bukka kuwa Almazeen zama ya yi ya kurawa Azima ido yana kallonta, shi bai ma san ta ina zai fara ba, ya kwashi kusan mintuna talatin yana kallonta daga bisani ya tashi ya ɗauro alwala ya yi sallah raka'a biyu, ya ciro wayarsa ya yi karatun alkur'ani mai girma ya daga hannunsa sama yana adduoi sannan ya shafa ya miƙe a hankali ya fara rage kayan jikinsa, wani magani da Baffa ya basa yace ya shafa a jikinsa idan zai taba Azima, maganin ya shafa a hannunsa da dukkkan jikinsa, yana tabata sai da ta girgiza,kwantar da ita yayi, Banju dake jikinta yana kallon abunda ke faruwa ɗauresa kawai Baffa yayi, wani gurnani ya fara nan ya hau buge-buge, Almazeen da iyakacin karfinsa ya fizgi kayan dake jikin Azima, nan dambe ya kacame duk da banju yana daure amma ba shi ya hanasa kokarin yunkurin kashe Almazeen ba shima Almazeen yaci albarkacin daure Banju da Baffa yayi amma duk da haka yanaji a jikinsa, duk kalman da yazo bakin almazeen indai na salati ne yin shi yake yi
,Banju bai gama sarewa ba sai da ya ga Almazeen ya yiwa Azima kaff da kayan jikinta, yunkurin komawa maciji Banju yayi amma kafin ya fara hakan tuni Almazeen ya karanto adduar saduwa ya fara kokarin shiga jikin Azima, wani sarawa kansa yayi tare da wani wawan jiri dake shirin watsa shi waje daurewa yayi ya riƙe kokaran gadon karan gam jikinsa na kyarma, nan Azima ta fara canzawa tana zama wata halitta daban mai matukar ban tsoro da firgitarwa, kokarin zare jikinsa yayi dan dama bai shigeta sosai ba, tunowa da maganar Baffa na cewa kar ya kuskura ya kyale Azima har sai ta yi attisha sau uku dan duk hanyar da Banju zai bi dan ya ga ya hana Almazeen kusantar Azima zaiyi, daga karshe kuma zai kashesa ya kuma guduwa, tunowa da haka yasa Almazeen ya dage da iyakacin karfinsa sakamakon b'ari da jikinsa ke yi ya shige Azima gabadaya, wani ihuu Azima ta saka da karfi wanda sai da ya karaɗe gefe da kewayen inda suke, ta shaƙo wuyan Almazeen wanda shi kadai yasan abunda yakeji kamar ana zare ransa haka yakeji tsananin azaba dan harta fatarsa ji yakeyi kamar ana soya masa shi, sake damƙar kafaɗun Almazeen Azima tayi ta dage ta saki wani attishawa mai karfin gaske dan kuwa an karya makarin Banju tunda Almazeen ya afka cikinta, tana yin attishawa na ɗaya tayi na biyu, na ukun ne nan wani guɗa ya hau tashi, tana attishawar Banju wanda ya yi tsalle ya fice ta baki da hancin Azima, ƙauuuuu! Azima taji yayinda ta wani firgita tana jan wani numfashi da iskar duniya,da nauyin kai ta hau ware ido da kyar jin idon kamar an liƙe mata su, tana ji tamkar yau ne uwarta ta haifeta, tana gama buɗe ido mutum ta hanga a saman kanta, Almazeen wanda yake gaff da sumewa yana ganin ta bude ido a hankali ya sauke bakinsa saitin kunnenta cikin mayuwacin hali da kyar ya furta
"Alhamdulillah! Wlcm back my dear wife, am so happy, u are back! i promise that i wouldn't let any harm attack u, i will sacrifice my life to u, cox I luv u, am really luv u, i fell in luv with u Azima! pls don't leave me alone" Almazeen na faɗi ya hau kokarin zare jikinsa daga na Azima, a lokacin Azima taji wani mugun raɗaɗi ta kasanta hakan ne yasa taja wani numfashin mai cike da azaba, a tare suka suma.

Banju dake tsaye yana
kallon Almazeen wanda yake son kashesa dan ya lashi takwabin sai ya kashe Almazeen, amma inaaa ya kasa kusantar almazeen balle ya kashesa kasancewar Almzeen mutum ne mai riƙo da ibada baya sanya.

💕💞💕💞

*NAWAZ DA AZIZA.*

Sadda aka raka Aziza tsayuwa tayi a bakin bukkar taki karasowa, Nawaz na zaune yana danna wayarsa da tun shigowarsu garin babu network ko ɗigo, ɗaga ido ya yi ya kalleta ya ga jikinta sai rawa yakeyi, da alama tsorata tayi, a hankali ya tashi yaje gabanta bata ma sani ba tayi zurfi a tunani, ji tayi an kama hannunta, a firgice ta dago idonta ya haɗe da na Nawaz, ganin duk ta taburce yasa Nawaz rausaya kai yace
"Ya haka? Jaruma a waje, matsoraciya a gabana?" ya faɗa yana matsota sosai, ja da baya tayi tana shirin ficewa yasa hannu ya jata ta shige jikinsa,
"Haba jaruma, karki bani kunya mana" mutsu-mutsu ta hau yi tana son kwace jikinta, yasa hannunsa duka biyu ya kewayeta ta kasa kwacewa ya ce
"Ko za a watsar dani ne?" nan ma bata masa magana ba, ya ce
"Idan baki min magana ba, zan cinye bakinki" mamaki ne ya kama Aziza, oh dama haka Nawaz yake? take tambayar kanta, bata gama yankewa ba sai da taji ya dauketa ya ajiyeta a saman gadon kara yana shirin kwanciya a kanta tayi saurin miƙewa zunbur tana fadin
"Sorry Hamma" murmushi ya yi a boye, ya ce
"To matso kusa dani, kin san Baffa yace na rikeki da kyau dan haka matso" ya faɗa yana ware mata hannu alaman ta shigo cikin jikinsa, ganin yadda ya sauya fuska ba alaman wasa yasa ta matso a hankali ta shige jikinsa ta kifa kanta a ƙirjinsa, yasa hannu ya rungumeta da kyau yana son fassara me zuciyarsa takeji game da Aziza.

A lokacin da Almazeen suka fara dambatuwa da Banju, a lokacin Aziza na kwance a jikin Nawaz, lokaci daya kamar an zabureta haka ta miƙe, cikin hanzari Nawaz ya fizgota ya maidata jikinsa ya matseta dan ya tuno da maganar Baffa da yake cewa idan Aziza ta subuce za a iya rasata shiyasa ya kara matseta sosai a jikinsa, ihu Aziza ta saka jin fatar jikinta na sabulewa, saurin ture Nawaz tayi ta koma gefe tana ƙanƙame jikinta, fuskarta ne ta ji yana b'anb'arewa, hannu biyu tasa tana tare fuskarta tare da ihu, ganin halin da take ciki yasa Nawaz saurin tashi zai zo gareta, nan yabga masifa, daga ƙugunta abunda ya yi sama ta zama macijiya fara sol sai kyalli take yi, sak irin wanda yake gani a mafarkinsa, hannu ta miƙa masa cikin azaba tana fadin
"Help me plss! ka taimakeni Hamma Nawaz!" ta faɗa siffar jikinta na ƙasa na haurawa zata zama macijiyar gabadaya, da saurin Nawaz ya rintse ido yaje ya rungumeta ƙaƙam! Yana rungumarta ta tsaya a haka, a lokacin da Banju zai fita a jikin Azima itama Aziza taci azaba dan nan suka hau gwada karfi da Nawaz, hakika shima ya jikata, dan kuwa sadda abun zai fita gani ya yi wani farin abu shi ba dutse ba shi ba tsuntsu ba ya fice ta goshin Aziza, yana fita numfashinta ya tsaya cak yayinda ta koma mutum, haka Nawaz ya zauna riƙe da ita a jikinsa, gab'ob'insa na masa ciwo sosai, har asuba.

💞💞💞💞💞

Sanyin asuba ne ya fara farkar da Almazeen wanda da kyar yake iya buɗe ido sabida nauyin da suka masa, ya jima a haka kafin da layi ya tashi ya janyo kayansa ya saka, ya rufawa Azima jikinta, ya koma ya kwanta a gefenta yana sauke huci mai zafi.

Baffa suna idar da sallar asuba Arɗo yace su je a duba yaran nan.

Mom aka kira dan da ita za aje Hajja ta ƙi fitowa ƙememe.

Suna zuwa gidan Hajja zata shiga da saurin Baffa ya dakatar da ita ya hanata shiga, yace tana shiga Banju zai iya kasheta dan shi yanzu duk wanda ya samu zai kashe ne" Baffa ne ya fara shiga cike da yarda da kansa sabida ya yi imani da Allah ya yi riƙo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam,duk wanda ya yi riƙo dasu baya da fargaba a kan kowa, yana shiga kuwa Banju dake neman hanyar guduwa a gidan tun daren jiya ya kasa sabida Baffa ya ɗaure ko ina da ina, suna ido huɗu Baffa ya daga takwabi, Banju yace
"Magaji a gwabza idan ba tsoro! karka kasheni sai mun gwabza!" Baffa ya yi murmushi yace idan ka so haka"
"Zan so! amma ka ajiye takwabi" Baffa ya ce
"Ba daga yanzu zamu fara ba, kafin nan ga wannan" Baffa na faɗi ya wurgawa Banju wani igiya nan ya daure Banju ya fito da shi, yana fitowa da shi ita kam mom bata iya daga ido ta kalli Banju ba, dan tace mugun ji da mugun gani Allah ya rabamu dasu, Baffa na cewa zata iya shiga da sauri ta wuce shi kuma ya wuce da Banju, mom na shiga ta samesu a yashe, Azima ta jijjiga sannan ta taba Almazeen wanda jikinsa ke rawa alaman ciwo jikinsa zafi raɗauu kamar wuta, na Azima ma akwai zafi amma na Almazeen ya fi nata, babu wani taimako da zata iya masa, amma zata iya taimakawa Azima, dan haka ta fito ta haɗa ƙirare ta tafasa ruwan zafi, kafin ruwan ya gama sai ga jikan Ardo Sanda ya kawo wasu magunguna yace Baffa yace idan su Hamma Almazeen da Azima zasuyi wanka a zuba musu shi a ruwan wankan suyi wanka da shi, wannan kuma su sha, sannan a ba wa Hamma Mazeen wannan,wannan kuma a ba wa Azima" mom ta karba tana masa sannunsa da aika.

Mom da kanta ta taimakawa Azima tanuna mata yadda zatayi wankan tsarki, sannan tayiwa mata wanka haka,ita dai Azima wani iri take jin kanta, riƙota mom tayi suka shiga bukkar har yanzu Almazeen ya kasa motsi koda da yatsarsa daya ne, taimakawa Almazeen mom tayo shima ya yi wanka ya yi sallah a zaune ya sha magungunan da Baffa ya bada a ba shi daga nan ya hau bacci,itama Azima maganin ta sha ta hau bacci, haka ma Aziza wanda aka aika aka ba wa Nawaz yasha ita ma ya bata ta sha duk suka buge suka hau bacci.

Can wajan dandalin yanki Baffa yaje ya daure Banju, ko kaɗan Banju baida kyawun halitta gani, ga girma katam da shi tamkar basamude ga baƙi fiye da misali, kai babu ta yadda za a sunfanta zubin halittan Banju.
Chapter 54 · 0% Book details