← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 61

Sashe 53

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Murtuƙe fuska Banju ya yi ya ce
"Magaji! ba dawowa nayi ba"
"Na sani Banju! ba dawowa kayi ba,jarumar 'yata ce ta dawo da kai"
"Kaii Magaji! Kunceni! Idan ba haka ba yankin kwana ta koma toka! Dan kasan wanene Banju! Bana da imani! Kasan karonmu da kai!" murmushi Baffa yayi yace
"Amma ni Magaji Bawa! ban gudu ba hakane Banju?" haɗe rai Banju yayi baffa ya ci gaba da fadin
"A yanzu ko Magajiyata Aziza tsaf zan iya sakata kasheka! amma halin da ka sakani yasa nake son kasheka da hannuna! ka fara ƙirga numfashinka daga yanzu zuwa gobe" dariya Banju ya yi yace
"Ashe kuwa idan zaka kasheni zaka haɗa da 'yarka, karka manta gangar jiki daya muke da ita" Baffa shima murmushi ya yi ya ce
"Duk makahon da kaji yace ayi wasan jifa yasan ya taka dutse bare mai ido kuma kai ma kasan bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane, a wannan tafiyar kaine makahon inaji ka manta da cewa yanzu haka Azima na da aure ko? mijinta shine zai fiddaka daga jikinta ni kuma na kawo karshenka ta yadda ba zaka kuma dawowa ba, kisan farko da na kasheka ban so ba, amma a yanzu ne zan kau da ka" wani ihu Banju ya yi yana son tsincewa, Baffa yace
"Aziza!" juyowa tayi ta kalli Baffa, Baffa ya mata alama da ido, ta gya ɗa masa kai sannan tayi gaban Banju tana shirin sake kafar da shi, da karfi ya furta mata "BAHULAAAAA!!" a kunne yana son tada Bahula dake jikin Aziza, wani ja da baya Aziza tayi ta dafe saitin zuciyarta da kanta, ganin haka yasa Baffa jan Aziza da sauri ya watsa mata wani farin hoda nan Aziza ta sulale zata faɗi Nawaz bai yi kasa a guiwa ba ya tare matarsa, da yatsa daya Baffa ya do ki goshin Banju, kamar anyi ruwa an dauke haka Banju ya tsaya cak, Mom cikin tashin hankali ta kama hannun Aziza wacce take kwance a jikin Nawaz ta ce
"Dan Allah Baban Aziza kayi wani abu, Aziza ta sha wuya wlh! Duk wani masifa kanta yake afkawa dan Allah tunda ga Azima a cire mata Banju ko Aziza ta huta, me yasa baka kashesa yanzu ba?" cikin kunya Baffa yace sabida har yanzu yana jikin Azima, idan na kashe Banju a yanzu Azima ma ta tafi!" nan Mom ta gane abunda Baffa ke nufi, ta kalli Hajja wacce ke tsaye a gefe tayi lullubi tana duƙe da kai, Mom ta ce
"Nawaz shiga da Aziza cikin gida, Maman Aziza? Dan Allah ki daina ɗaurewa kina wannan kunyar taki, ki saki jiki ki rungumi yarki, an wuce wannan zamanin kunyar, yarki ce fa? Karki cutar da kanki kina son jin dumin yarki amma ki ta rabewa, dan Allah bana son haka, ai gwara ki ja ta a jiki kafin na dauketa" rasssss!! gaban Hajja ya faɗi jin mom tace zata dauke Aziza, amma bata iya furta ko da uhum bane tabi bayan Nawaz da ya shige da Aziza, mom ta ce
"Baban Aziza zamu yi magana" Baffa ya ce
"To madalla bismillah" gefe suka koma suka kebe, mom ta ce
"A ba wa Almazeen matarsa yau suyi mu'amala ta aure dan a kawo karshen wannan masifan, karka ce zaka biyewa kunya, wajan ceton rai babu zan can kunya, a nema masa inda za a kai masa matarsa, a gobe ka kashe Banju,idan kuma hakan ba zai yu ba to a bamu su mu koma birni idan yaso komai ya daidaita a can Banjun ya fita sai a kashesa a can birni sai mu tafi tare da ku, amma ya ka ce?"girgiza kai Baffa ya yi cikin sauri ya ce
"Maganar a bar yankin nan a shiga gari akwai matsala, ba zan boye miki ba, Almazeenu zai fuskanci kalubale wajan kusantar Azima, Banju ya wuce duk tunaninki , kuma bayan ya kusanceta zaiyi ciwo, ba lallai bane ku a cikin gari kuna da maganguna irin tamu ta gargajiya, ga misali a kan Aziza haka tayi ta faman ciwo sai da ku ka zo kafin ta samu furen huriri ta warke, a nan aka fara yaƙin a nan kuma nake so a ƙarasata,bana so a kai muku masifa kuna zaman lafiya, burin Banju kenan ya sake barin yankin nan,ni kuwa ba zan bar haka ta faru ba ta yardan Allah, dazu bayan munyi sallar asuba maganar da Baffa Mandi da Arɗo suka min kenan a ba wa Almazeenu Azima yau, akwai wani gida da Arɗo yasa aka zagaye a can kusa da wajan gari, amma akwai tsirarakun fulani a wajan kawai dai gidan ne shi daya, yanzu haka zamu tafi da shi Almazeenu din, kafin nan zan ba shi wasu magunguna da rubutu su sha shi da Nawazu din, dan shi ma yana da bukatar haka tunda miji ne ga Aziza" Mom ta ce
"To ba damuwa hakan ma yayi Allah ya iya mana" Baffa ya amsa da amin, mom ta kira Nawaz da Almazeen tace musu su bi Baffa, Malam Yunusa kuma da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami suna tare dasu sarki chubado da mai unguwa ori sai hira sukeyi ana shan damemmen fura da nono, gwanin sha'awa.

@@@@@

Gidan suka je, duk da gidan kara ne amma yadda aka shirya gidan ya burge Almazeen, tarko Baffa ya saka a ciki da waje ta yadda ko Banju ya fice a jikin Azima ba iya guduwa zaiyi ba.

Sannan Baffa ya ba wa su Almazeen da Nawaz wasu maganguna da rubutu yace su sha, ya basu na kariya da na sha da na wanka da na gogawa dana murzawa dana ɗorawa duka babu wanda bai basu ba, daga nan sukayi wani gida gaba kaɗan da na inda aka ba wa Almazeen, Baffa yace
"Nawazu, kai ma a nan zaka zauna ka riƙe Aziza, dan a lokacin da abun da ke jikinta zai fita zata iya shiga wani hali, zata iya fita hayyacinta, idan kuma ta subuce zamu iya rasata na har abada dan babu abunda Banju ba zai yi ba" Nawaz yace
"In sha Allah hakan ma ba zata faru ba Baffa, hakuri da gaskiya sune a sama, zamuyi nasara a kan Banju bi'izinillahi ta'ala!" Baffa ya yi murmushi na jin dadin samun sirkai kamarsu Nawaz da Almazeen, haka shi ma wannan gidan ma ya saka matakan tsaro.

Wunin ranar kuwa Baffa bai zauna ba shiri yayi sosai ya koma asalin Garkuwa Magaji Bawansa kyakkyawa fari dogon bafulatani mai dogon hanci da halin girma da cikar zati da haiba.

Da daddare mom ita ce tayiwa Azima da Aziza komai,ita da Maman Beenah suka raka Azima da Aziza, Almazeen wani irin kunya yakeji, hajja kuwa ta kasa fitowa a bukka tana zaune tana tasbihi ga Allah, tana roƙon mai duka da ya fidda mata yaranta lafiya, hakika ita kam ta ga jarabta.

Bayan an mikawa Almazeen Azima wacce take da ita da babu za a iya cewa duk daya, sannan aka wuce aka kai wa Nawaz Aziza duk da shi ba wani abu bane zai wakana a tsakaninsu.

Ko da su Mom suka koma itama ba kwanciya tayi ba, alwala tayi ta zauna ta fuskanci gabas, Maman Beenah kuwa gadon kara ta haye tayi kwanciyarta dan tace bacci takeji.

Baffa ma uban gayya bai ga ta zama ba balle ya rintsa dan kuwa a tsaye yake kyam.

💕💞💕💞💕

*AL-MAZEEEN DA BANJU AZIMA.*
Chapter 53 · 0% Book details