← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 61

Sashe 25

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*ASSALAMU ALAYKUM, SAKO ZUWA GAREKU MASU FITAR MINI DA BOOK DA MASU KARANTAWA BASU BIYA BA, DA WA INDA SUKE GANI SUKE KARA WATSATA A DUNIYA,DA FARI ZAN FARA DAKU MASU FITARWA DAN BABU MASU LAIFI SAMA DA KU! HAUSAWA SUKA CE SAI BANGO YA TSAYE KAƊANGARE K......! DAYAWANKU WASUNKU SUN JAHILCI WANNAN LAMARIN NA CEWA WAI KUDINSU SUKA CIRE SUKA BIYA YA ZAMA NASU MALLAKINSU, YAR UWA TA INA LITTAFI YA ZAMA NAKI? LITTAFI HAKKIN MALLAKAR MARUBUCIYA CE ITA DA TA ZAUNA TA TSARA LABARINTA SANNAN TA RUBUTA TA WALLAFASHI TA WATSA SHI HAR KIKA KARANTA SHI,KE KIN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI,KI KARANTA KI BAR WA MARUBUCIYA ABUNTA, KUNA FADIN YANZU MISALI KUJE KASUWA KU CIRE KUDI KU SIYI ABUN SAI ACE MUKU KARKUYI KYAUTA DA SHI KO KU BADA ARO? TO INASO KI SANI AKWAI BAMBANCI TSAKANIN ABU A ZAHIRI DA SOCIAL MEDIA, YANZU NE AKA SAMU CI GABA KINA DAGA KWANCE A DAKI BA SAI KIN SHA WAHALA BA KINJE KASUWA KIN SIYO LITTAFI BA, A DA KAM WA INDA SUKAYI KARANCE-KARANCE SUN SAN TSADAR LITTAFI DARI BAKWAI DARI TAKWAS KAI HAR DUBU DAYA, SANNAN MIYE RIBARKI FISABILILLAHI DAN KIN CIRE DARI! NAIRA DARI KIN BIYA KUDIN KARATUN LITTAFINA SANNAN KI DAUKA KI WATSAWA MUTANE SAMA DA DUBU DARI DA BASU BIYA BA? ANYA KUWA AKWAI ADALCI A LAMARIN? DUK TALAUCIN MUTUM MAGANA TA DOMIN ALLAH ZAI CE BAI DA NAIRA DARI DA ZAI BIYA YA KARANTA LITTAFINA NE? BAN TSAULAWA BA SABIDA NA SAN KUNA SON LITTAFIN SHIYASA BANSA TA YADDA BA ZAKU IYA BIYA BA, WLH WLH WLH AZIM DA ACE KUN SAN WAHALAR RUBUTU KO A SHAFI DAYA ZAKU DINGA BA WA MARUBUCIYA DARI BIYAR A DUK SAKIN PAGE WLH BAKU BIYATA BA, BALLE KUMA NI DA NA ZAUNA NA TSARA MUKU LABARI NA CE KU BADA NAIRA DARI KACAL! YAKE MAI FITAR MIN DA LITTAFI INASO KI SANI HAKKINA NE,KUMA DUK HAKKIN DA KA RAINA SHI KE GIRMA YA TSOLE MAKA IDO, IDAN HAR BA ZAKI DAINA TOZARTANI BA TA HANYAR WATSA MIN LITTAFI BA TO INASO KI SANI BA ZAN MIKI ALLAH YA ISA BA, AMMA SHURUN DA NAYI WLH SAI ALLAH YA SAKA MIN, MASU CEWA SAI SUN SATO KUMA SAI SUN KARANTA ALLAH YA BAKU SA'A, A AL'ADANCE SATA SUNANTA MA BABU DADI BARE A ADDINANCE HARAMUN NE! SANNAN WANNAN ALLAH YA ISAN DA KUKEJI MARUBUTA NA FADI BA KARAMAN KALMA BA CE WLH,KE IDAN KINA DA TUNANI KI ZAUNA KIYI NAZARI A KAN KALMAN ALLAH YA ISA! SANNAN NA DAWO KANKU MASU KARANTAWA HARDA TAMBAYAR CI GABA,IDAN HAR KINA KAUNAR ALLAH KINA GANIN GIRMAN DARAJAN ANNABI MUHAMMADU SALALLAHU ALAIHI WASALLAM! KI DAINA KARANTA MIN LITTAFI BAKI BIYA BA,KI NEMENI TA LAMBATA KI BIYA NA SAKAKI A PAID GRP DINA IDAN KUMA KIN SAN ZAKI BIYA NE DAN KI WATSA SHI DAN ALLAH BA SAI KINZO GARENI BA🙏🏻, HAKA KEMA MAI YADAWA DUNIYA INA ROƘONKI DA GIRMAN ALLAH DA DARAJAN IYAYENKI KI BARI! BAKI SIYA BA AMMA IDAN KIKA GANI JIKINKI NA RAWA KI TURAMA WASU KEMA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA, ALLAH YA BAKU IKON FAHIMTAR ABUNDA NA FAƊI, WA INDA BASU SON SU CI HAKKI SAI KU NEMI NAKU!*

*PAID.*
🅿️==3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣

Cikin gari ya nufa inda ya kaita asibiti mafi kusa, yana shiga ya ce a bata taimakon gaggawa,inda wasu nurses suka hau masa iskanci a kan ba zasu karbeta ba, hannu yasa a aljinun wandonsa ya ciro wallet dinsa ya bude ya ciro ID Card dinsa ya nuna musu, suna gani suka hade gefe suna sorry sir, ya ce
"Baku da tausayi ko kaɗan! haka ku ke yiwa jama'a da haka idan yazo da ƙaran kwana sai marar lafiya ya mutu amma kune sanadi! An san likitoci da tausayi dan haka ku gyara,ina mai wannan asibitin ina son magana da shi idan har yana kusa" jiki na rawa suka ce bari su nuna masa office din, har bakin kofar office ɗin suka kaisa, ya kallesu su biyu ya ce
"Ku fara duba yarinyar nan kar ta mutu ina zuwa bari nayi magana da shi zan zo nayi mata dressing da kaina"
"Ok sir" suka fadi shi kuwa ya shiga ciki da sallama.

Amsawa wanda aka yiwa sallama ya yi, ya kalli wanda ya masa sallamar ya ce
"Bismillah ƙaraso ga waje zauna mana" ƙarasowa ya yi cike da jin kansa ya zauna,sannan ya miƙawa Dr din hannu suka gaisawa, Dr din ya ce
"Amma ban gane ka ba daga ina? sannan baka yi kama da marar lafiya ba" murmushi ya ɗan yi na gefen baki, sannan ya miƙa masa ID dinsa,yana dubawa ya kallesa ya ce
"Doctor?" ya yi murmushi yana gya ɗa kai, tashi ya yi da sauri yana fadin

"Allah dai yasa sa'a ce ta sameni har office zaka fara aiki a hospital dina" shi ma tashi ya yi tsayen ya ce
"A'a ko ɗaya wlh,ai ni ba a nan yola nake da zama ba,ina zama a kd ne akwai aikin da ya kawoni ne,tun jiya ma ya kamata ace na bar yola to ashe tsautsayi ne ya tsayar dani dan na buge wata yarinya ne da mota shine na kawota asibitin,inaso nayi treatment dinta sai mu wuce dan bana so na ƙara kwana a garin nan"
"Ya Subhanallah! tana ina yarinyar? muje sai ka dubata ai ba komai" ba tare da ya sake magana ba ya bi bayan Dr har izuwa dakin da aka kwantar da Aziza, suna shiga ya hau dubata ya ga bata mutu ba, kayan aiki yace a ba shi ya fadi abubuwan da za a ba sa aka kawo masa sannan ya hau dubata,ya mata su allurai ya sakawa kanta bandage ya mata komai sannan ya ɗora mata ruwa, ya duba agogon dake daure a hannunsa ya ga sha ɗaya, ya kalli Dr ya ce
"Tnk u so much Dr on my way" ya faɗi tare da kokarin daukar Aziza, Dr ya ce
"Haba Doctor ka bari mana ko zuwa gobe sai ka wuce idan ta farka,ga shi kace baka santa ba,duk yadda akayi inaji irin fulanin rugan nan ne, yanzu idan ka wuce da ita kd alhali ba yar kd ɗin ba ce fa?" shuru ya yi yana nazarin maganarsa kuma gaskiya ne tunda a nan ya sameta miye hujjarsa na tafiya da ita? Kawai ya barta idan ta farka taji sauki sai su sallameta ta koma inda ta fito, da wannan tunanin ya ce Dr ɗin ya ba shi acct number ya masa transfer'n kuɗi ya kula da ita idan ta warke sai su sallameta,haka kuwa aka yi bayan ya masa transfer ɗin nan ya fito da sauri ya shiga mota ya tayar yaja ya bar asibitin, har ya fara tafiya ya ɗan yi nisa sai yaji hankalinsa bai kwanta ya tafi ya barta ba,ko ba komai shi ya bugeta sannan bata farfaɗo ba ya tafi ya barta anya ya kyauta kuwa? Saurin juya kan motar ya yi ya koma asibitin, yana zuwa ya ce a ba shi ita kawai, Dr ya ce
"Haba Doctor baka yarda damu bane?"
"No ba haka bane ba wai ban yarda daku bane,kawai ban yarda da shawaran da zuciyata ta bani bane na in tafi in barta alhali ban san a wani condition zata farka ba that's why, amma yanzu zan tafi da ita,idan ta farka lafiya taji sauki zan sa a maidata gidansu" da haka yasa hannu ya dauketa tare da drip ɗin da ya ɗora mata, har yanzu tana bacci, ya gyara bayan motarsa ya kwantar da ita ya ajiye drip ɗin a gefenta yana duba agogo tare da auna tym din da ruwan zai ƙare" da sauri yaja motar yanayi yana duba tym.

🐍🐍🐍🐍

Horn ta yi a wani madaidaicin gate da sauri gateman ya zo ya buɗe yana zuba mata kirari, hannu ta daga masa sannan ta danna hancin motar cikin gidan,tana parking ta fito tana fitowa ita kam ma ta manta da ta saka mutum a bayan both cikin gida ta wuce tun kafin ta shiga take kwalawa Lantana kira, da gudu wata 'yar dattijuwar mata ta fito ta zube a gabanta ta ce "gani *Hajiya Zubaida*"

"Oh dan iskanci dama kinaji ina ta faman kwala miki kira amma ba zaki iya amsawa ba sai dai ki wani fito da mugun gudu sai kace ana gasan tsaren karnuka, ki fa kiyayeni kiyi hankali!, ina Hajiya?"
"Tana ciki"
"Hajiya! Hajiya! Hajiya!" ta hau kwalawa Hajiyan kira.
Chapter 25 · 0% Book details