← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 61

Sashe 15

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      "Ka rufe mana baki Magaji!!Ya isheka haka!!" Jauro ya katse Baffa, Jauro shine mai magani na yankin kwana
"A kan me zamu bi abunda zaka gindaya!? Kana da halin da zaka taimakemu amma kayi hakan ne? Duk wani yaƙin da zai kunno kai kasa a ranka har da sa hannnunka a ciki! Da ace ka taimaki yankinka har za a yi aike a wani yanki mai suna yankin ja'i ne! Dan haka babu abunda zaka gayawa mutanen yankin nan! Sai ka bar mu mutu! Idan an kashe Garkuwa da yan faɗa biyu sai mu ma mu jira mu ga mai zai yi ajalinmu,Macizai ne ko kuma jama'ar ja'i!"

      "Haba Jauro miye haka ne kake yi! Bai kamata ka faɗawa Magaji wannan maganar ba! Kwata-kwata ma yanzu ba lokacin musayar yawu bane!" cewar Arɗo, Jauro ya ce
"A kan me ba zan faɗa masa ba! Karya nayi ne! Na ce karya nayi ne!!?" sarki Chubaɗo ya ce
"A gaskiya ban san me zance a wannan lamari ba, amma zan iya bin maganar Jauro! Magana ta domin Allah wannan yanki ya kafu tun kakanni, wanda ya taimaka ya kara tsayawa ma wannan yanki kai ne Magaji! Tun ban san da cewa zan zo na zama sarkin fulanin kwana ba, ni dai roƙonka zanyi da girman Allah ka taimakemu Magaji! Muji da masifa ma daya ta ishemu ba sai an ɗaɗo mana da na yaƙi ba" Sarki Chubaɗo ya faɗa yana haɗa hannunsa alaman roƙo,Baffa ya jinjina kai tare da faɗin
"Naji! Kuma na yarda! Abunda aka binne shekaru ashirin shine zanje haƙosa yau! Shin zaku iya fama da masifu biyar!? E ko a'a? A da masifa daya ce, sannan ku ka kuma janyo mana wata da hannunku, yanzu kuma kun bada dama aje a kara haƙo wata shin zaku iya tayani tareta? Nayi imani a yanzu yankin kwana babu mai iya tayani yaƙi da aljanu babu shi!"

       " *AZIZA!* Baffa ya ji an raɗa masa a kunne, da sauri ya dago yana waige amma bai ga kowa ba, "Aziza kuma?" Baffa ya tambayi kansa a zuciyarsa yana shirin faɗawa kogin tunani ya tsinkayo muryan Arɗo da Baffa Mandi suna fadin
"Gaskiya ba zamu yarda a haƙo ba,ta bakinka Magaji babu wanda zan iya wannan yaƙin kawai a bar maganar mu sake neman taimako ku kuma ka faɗa mana hanyar da zamu bi" Sarki Chubaɗo ya ce
"E hakane magaji, ka gaya mana wace hanya ce zamu bi?"

     "Inaaaaa! Sam-sam  ba zai yu ace Magaji bane zai bamu mafita sam ban lamunta ba! Ni fa wlh ina zargin Magaji, duk yadda aka yi yaransa ne *MACIZAI!*" Jauro ya faɗa yana huci, saurin dagowa Baffa ya yi yana kallon Jauro, dama ya jima da sanin jauro baya sonsa yana baƙin ciki da shi, ya jima yana masa ƙulli amma kawai bai san yadda zai yi da Baffa bane, shuru Baffa ya yi yana kallon Jauro, yayinda Arɗo ya katse Jauro da fadin
"Wai lafiyarka kuwa Jauro? Ko dai akwai wata a kasa ne tsakaninka da Magaji?"

"Miye haɗi na da shi?" Jauro ya faɗa yana yiwa Baffa kallon ƙasƙanci,
"Kawai dai gaskiya abunda na sani ne,meyasa ya ƙi aurar dasu yara duk sun gandare a yanki babu mai rab'arsu, shekarunsu goma sha biyar oh Allah ni Jauro, yara na tafiya jiki na lankwasa ace mutane ne! Taya hakan zata kasance!? Kullum fuskarsu a rufe sabida babu ido mai kyau, sannan duk taron da za ayi na magani basu zuwa, dan Allah a cikinku nan ku gaya min suwaye suka yarda da yaran Magaji mutane ne?" nan wa inda Jauro ya haɗa baki dasu suka amsa da basu yarda da Azima da Aziza ba, sannan Jauro ya matso kusa da Baffa wanda ya koma tamƙar wanda aka dasa bishiya ya ce
"Zan fara sakawa yaranka ido fiye da yadda na saka musu a baya, idan har na gano cewa su ɗin ba mutane bane na maka alkawari da hannuna zan kashesu a gabanka!!" rass!rass!rasss! Gaban Baffa ya bada yana kallon Jauro, shi kuwa Jauro yana gama faɗi ya juya zai bar wajan ya tsinkayi muryar Baffa na faɗin
"Allah ya baka sa'a,ni nan zan baka takwabin da zaka kashe yarana a gabana!" ko uhum Jauro bai ce ba ya bar wajan, Baffa Mandi ya ce
"Wai miye haka ne kam?" murmushin takaici Baffa ya yi ya ce
"Ba komai! Ni na jawowa kaina ai!" shi ma ya juya zai bar wajan sai gasu Garkuwa a muraran! Da sauri aka tarbesu kowa yana furta kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Da sauri aka sauko dasu daga dokin yayinda Garkuwa ana sauko da shi yana sumewa, ba shiri aka ce a kai sa wajan Jauro ya duba sa.

@@@@@@@

      A ranar yankin kwana babu wanda ya rintsa, Aziza kuwa ta yi neman Azima ta rasa hakika Aziza idan tace akwai natsuwa da sauran hankali a tare da ita ta yi karya.

       Da washe gari Aziza na idar da sallar asuba ta fice, jejin kwana ta nufa, tana zuwa ta kirawo Inno Fandi, Inno Fandi na zuwa Aziza tasa kuka, girgiza kai Inno Fandi ta yi ta ce
"Aziza ba kuka bane mafita, abu mai mahimmanci shine a yanzu ki maido da natsuwarki, rashin natsuwarki shi ya hanaki ganin Azima, zaki iya ganinta amma sai kin samu natsuwa, sannan zaki iya zuwa dan ki gayawa Baffanku gaskiyar su waye ku, dan ba zaku ci gaba da boyewa ba Azima na kashe mutane,idan ba haka ba a duban da nayi kowa na yankin nan ya kusan mutuwa! Abunda Magaji baya so dole karshe shi zai aikata, wato haƙo baiwarsa da ya binne shekaru ashirin, sannan duk yaƙin da zata kama da wuta kece garkuwar mahaifinki Aziza,ki koma gida Magaji ya ba ki asalin tahirin rayuwarsa na abunda ya faru shekara ashirin amma har sai kin gaya masa gaskiyar su waye ku!" Inno Fandi na gama faɗi ta b'ace, Aziza kuka takeyi kamar ranta zai fita,taya zata fara faɗawa Iyayenta su ba mutane bane Macizai ne? Taya!? Ya Hajja da Baffa zasuji? Idan suka gano cewa duk kisan da akayin nan Azima ta yi su?" kuka sosai ta yi ta godewa Allah fuskarta ya yi jajur idonta ya ƙara komawa fari sol, tashi tayi tana ajiyar zuciya tare da tattaro natsuwarta  kamar yadda Inno Fandi ta gaya mata sai ta samu natsuwa kafin ta iya sanin ina Azima in ba haka ba yau ma kisan da zatayi sai Allah ne yasan adadi, a hankali ta rintse ido tana karanto adduar samun natsuwa ta hanyar tasbihi ga Ubangijin talikai, sai da taji zuciyarta ya samu natsuwa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta rintse ido nan ta ganota kwance a jejin hayi, da sauri ta buɗe idon tana me daukar hanyar jejin hayi ba tare da bata lokaci ba gwanda taje suyi na yau.

      @@@@

Maga Isar da Sakon yankin kwana ne yake karantawa fada sakon yankin ja'i kamar haka
" _DAMA MUNYI MAMAKI ACE KUNA DA MUTUM A YANKINKU KAMAR MAGAJI BAWA AMMA ACE KUN ZO YANKINMU NEMAN TAIMAKO DA INNU MACIJI! HAKIKA MUMA MUN ZAMA SHASHASHU DA MUKA YARDA DA KUDIRINKU! BAYAN MUN SAN DA CEWA KU ƊIN ABOKAN GABANMU NE NA TUN TULI-TULI! A KODAYAUSHE KU YANKIN KWANA KUNA SO KU DINGA NUNAWA KUN FI SAURAN YANKUNA! TO MUNA SO KU SANI KU KARA SANI, LOKACI YA YI DA ZAMU MAIDA YANKIN KWANA BABBAR MAƘABARTA! DAN KUWA MUNYI SAƘO YANKIN JIMO MUN ZUGASU NA JARMAN MACIZAI DA KU KA KASHE! TUN KAFIN KUYI AIKE YANKIN TUDU MUN RIGAKU DAN BA ZAMU YARDA DA KASHE MANA INNU MACIJI DA KU KA YI BA, MUN GAYAWA YANKIN TUDU KUN KASHE MANA INNU MACIJI SANNAN BA MAMAKI KU MUSU AIKE A BAKU IRO MAGANIN MACIZAI TO MUN TOSHE WANNAN HANYAR DAN MUN TONOWA SARKIN TUDU TSOHON RAUNIN DA YANKINKU SUKAYI MASA TA HANYAR KASHE MASA GUDAN JININSA, DAN HAKA KU FARA SHIRYAWA TARBAN YAƘI NA YANKUNA GUDA UKU, YANKIN JA'I: YANKIN JIMO: YANKIN TUDU: SAKO DAGA YANKIN FULANIN JA'I._"

     Maga Isar da sako yana gama karantawa aka hau kallon-kallo, Mai Unguwa Ori ya ce
"Yaƙi da yanki uku a kan yankin daya?"

"Kuma lokaci daya?" cewar Sarki Chubaɗo,Arɗo ya ce
"Mu dai mun san bamu aikata komai ba, mu sa a ranmu wannan wata jarabawa ce daga Allah, kuma yana sane damu, shi zai kawo mana dauki, kar mu ce zamu yi wani shirin yaƙi, mu zubawa sarautar Allah ido" kowa ya amsa da haka ne sannan kowa ya watse cike da alhini.

       🐍🐍🐍🐍🐍

Azima na kwance a kan bishiya rabinta mutum rabinta macijiya, jelarta na lilo a ta saman rashen bishiya fuskarta a haɗe har gefe da gefe ya yi jaa! Idonta kuwa ya kara rikiɗewa ya rine ya koma blue sosai harta fari babu, Aziza tana zuwa jejin hayi jelar Azima ta fara hangowa, saurin karasowa ta yi ta ce
"Azimaa!?" jin muryar Aziza yasa Azima sulalowa tare da komawa mutum, a fusace tayo kan Aziza tana isowa gabanta kafin ta yi mata magana Aziza ta yi saurin dafe goshin Azima nan take taji abu ya shige mata kai sai da ta girgiza.
Chapter 15 · 0% Book details