← Book details Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 61

Sashe 52

Aziza da Azima Macizai Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ayya sannu da zuwa ɗiyata" Mom ta fada tana kurawa Azima ido ganin wani sirhitaccen kamanni da takeyi da Aziza, duƙawa har kasa Azima tayi ta ce
"Ina kwana mom? Mun sameku lafiya?" hakan da tayi ba karamin dadi Almazeen yaji ba, Mom ji tayi muryan ma irin na Aziza amma sai dai Aziza ta fita sanyin murya sosai,
"Alhamdulillah! Ga shi kin zo su Sultana sun tafi gidan lalle da gyaran jiki, amma zo na nuna miki dakin sultana sai ki zauna ki jira su, ko kina so a kaiki gidan lallen kema a miki?"
"A'a ban taba yi ba ma a rayuwata, zan jira su ɗin kawai" mom tayi murmushi ta kama hannun Azima caraf idonta ya sauka akan zoben hannun Azima iri daya sak da na Aziza,kuma Aziza tace sadda aka haifesu kakansu Arɗo shi ya ba wa Hajjarsu ta saka mu shi a hannu, daurewa Mom tayi ta ce ya sunanki?
"AZIMA!"
"Ma sha Allah Azima suna mai dadi, Azima wa?"
"AZIMA BANJU!!" ba iyakar Mom ba harta Nawaz wanda yake kokonta sai da ya waigo a firgice, da kyar Mom ta iya riƙe kanta tana murmushin yaƙe ta rungumo Azima ta kaita dakin sultana sannan ta koma daki ta samu Almazeen na tambayar Nawaz meke damunsa, Mom Na shigowa Nawaz ya mike yana fadin
"Wlh ita ce mom, yar uwar Aziza ce, Allah Alhamdulillahi³!" Mom da Nawaz suke faɗi, Al'mazeen da kansa ya shiga duhu yace
"Dan Allah Mom ku min bayani ku fiddani a duhu, dama Aziza tana da yar uwa ne?" mom tace
"Dole zamu maka bayani amma kafin nan a ina kasan Azima ina ka sameta?" bai boye musu ba aiki takeyi agidansa a cam ma ya sameta dan tun bayanan su Maman Hanan suka gaya masa an dauke sabuwar mai aiki, har izuwa sadda ya dawo da shakuwar da ta shiga tsakaninsu.

"ALLAH KENAN MAI YIN YADDA YA SO, HAKURINKA BAYA FADI KASA BANZA! ALLAH YA TAKAITA MANA WAHALA" cewar Mom tana jinjina kai, zama sukayi nan Mom ta hau warwarewa Al'mazeen komai bata kara ba bata rage ba, Al'mazeen ya zare ido yace
"Kenan mom *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE? SANNAN YAN BIYU NE?* mom ta gya ɗa kai,
"Kenan Azima ba Azima bace Banju ne?" mom ta ƙara jinjina kai
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" mom ta kara da cewa
"Wannan shine dalilin da yasa auren Nawaz da Aziza ya tashi babu shiri dan yin jahadi ya taimaki Aziza" jinjina kai Al'mazeen yayi ya ce
"Idan har Aminina zaiyi wannan aikin ladan ba tare da ya faɗa soyayya ba ina ga ni da na fara son Azima? Sannan ta taimakeni da badin sanadinta ba da yanzu b'arayi sun kasheni!" nan ya bai wa mom labari mom ta hau salati tana sanar da ubangiji, sannan ya kara da cewa
"Ta taimakeni! Ta ceci rayuwata yayinda ta saka nata a hatsari! mom ina son Azima! Ina so kuma jibi nima a ɗaura min aure da ita amma karta sani, kamar yadda Banju shaiɗanin aljani ne zai iya kashemu idan har yasan da hakan, sannan ya kamata a gayawa Aziza kar ta dawo gidan nan dan karsu haɗu da Azima har sai bayan an daura aure" Mom tace
"Hakan ma wata shawara ce mai kyau,idan yaso aka daura auren da washe gari ranar sai mu shirya tafiya yola,ko kuma da an daura kawai mu wuce tinda Aziza tace cikin daci suke, sai ku shirya mota mai ƙarƙo da zai iya kaimu zamu tafi da Malam Yunusa da ƙanin mahaifinku da kuma Hajiya Lawiza ko kuma Hajiya luba"
"E hakan ma yayi mom" cewar nawaz, na suka gama tsara abunda zasuyi.

An gama yiwa Aziza lalle tana zaune,ita kuwa Sultana ana wanke mata nata, gajiya da zaman Aziza tayi ta ɗan jinginu tana lumshe ido, tana lumshe ido wa zata gani? Azima ta hanga wani ajiyar zuciya ta sauke da jan numfashi ta buɗe ido tace
" *AZIMAA!?"* sultana tace
"Azima kuma? Ina kika ganta?"
"Wlh na ganta Anty Sulty ina rintse ido na ganta,ina zuwa bari na sake dubawa" rintse ido tayi ta shafo tafin hannunta nan ta hangi Azima kwance a gadon sultana, a hankali ta buɗe ido tace
"Azima a gida kuma a dakinki a gadonki?" sultana zatayi magana wayarta ya yi kara, tana dubawa ta ga mom saurin dauka tayi tasa a kunne tayi sallama mom tace saurareni da kyau Sultana" nan mom tayiwa sultana bayanin komai sannan tace
Idan sun gama su biya gidan kawarta Hajiya Biba su ajiye Aziza sannan su su dawo, yanzu sultana ki yiwa Aziza bayanin komai yadda na miki, mom na gama fadi ta ajiye waya,sultana ido bude ta kai bakinta saitin kunnen Aziza tayi mata bayani dalla-dalla,itama Azizan ido a waje ta kalli Sultana, sultana ta jinjina mata kai.

Basu gama ba sai gaf magriba dan haka ko da suka tashi suka biya suka ajiye Aziza a gidan Hajiya Biba su kuma suka wuce gida.

Ko da suka isa Sultana bata nunawa Azima komai ba tayi maraba da ita ta hau janta a jiki.

Nan sanarwan aure ya koma na mutum uku.

Da washe gari walima Mom ta ba wa Azima haɗaddiyar dogon riga wanda yasha stone, a jiya ne ma da dare tasa aka nemo mata kasancewar ba ayi shiri da ita ba, bata tayi ta saka Azima ta karba ta mata godiya, kasancewar a gidan za ayi walimar a tare kusa da juna Mom ta zaunar da sultana da Azima,itama Aziza ana can anayin nata a gidan kawar mom, sadda aka fara wa'azi dodon kunnenta kamar zai tarwatse ji take har fatarta ƙuna yakeyi dan da karfi Malama Rasheedat Hassan Usman ke fadin Allah yace Annabi Yace.

Duk wanda yazo ya tambaya wannan itace amaryan Nawaz din sai mom tace a'a ta Al'mazeen ce, lokacin dasu Maman Hanan suka iso kamar su mutu da bakin ciki dan tun a jiya labari ya iskesu nan suka dinga tsinewa Almazeen da Azima, har suna cewa dama ya sane ya ƙi fada musu zaiyi aure.

Anyi walima lafiya aka watse lafiya.

Da washe gari karfe sha ɗaya za a daura aure kasancewar su Nawaz zasu kama hanyar yola ne da an daura aure.

Tun wayewar gari Azima ta kasa zama ta kasa tsayuwa ta rasa dalili, a gidan Hajiya Biba kuwa itama Aziza ta matsu suyi ido huɗu da Azima.

Ma sha Allah sha ɗaya nayi dai-dai aka shaida daurin auren Khalil Alhaji Yaro da Amaryarsa Sultana Alhaji Sardauna, sai kuma na NAWAZ ALHAJI SARDAUNA DA AMARYARSA AZIZA MAGAJI BAWA, SANNAN AKA DAURA NA AL'MAZEEN ALHAJI SAHABI DA AMARYARSA AZIMA MAGAJI BAWA! ana daura aure Azima na zaune a daki da su Sultana da kawayen sultana nan ta riƙe kirjinta ta hau tari, ana gama daura aure Nawaz da Al'mazeen da wasu abokai sukayi gidan Hajiya Biba dan dauko Aziza, da lullubi aka fito da ita kanta na juyawa kasancewar mahaɗi daya suke da Azima wacce take mayuwacin hali a gida su Sultana sun rufo a kanta.

Da kyar Aziza ke fizgar numfashi ta gaida su Al'mazeen suka amsa ,hankalin Nawaz na kanta yana lura da halin da take ciki.

Suna isowa gida guɗa ya hau tashi ana ga angwaye ga angwaye, Mom tace su hauro sama, Aziza ta taka step jiri ya kwasheta zata fadi da sauri Nawaz ya tallabota nan jama'a aka sa ihu ana musu tafi, shi dai matarsa kawai ya kama suka hau sama, hannun kofar Aziza ta murɗa fuskarta a murtuke, tana tura kofar a lokacin Azima na duƙe sultana na bubbuga bayanta.

"AZIMA!" Aziza ta kira sunanta murya a daskare, wani wawan dagowa Azima tayi caraf idonta ya sauka cikin na Aziza wacce Nawaz ke rike da kafaɗunta.

🍃🍃🍃🍃

MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
  11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*WA INDA BASU BIYA BA SUN BIBIYI PAGES BA, CMLPT DCMNT #300 NE, NOR #100.*

*PAID.*
🅿️=6️⃣7️⃣↪️6️⃣8️⃣
Chapter 52 · 0% Book details