← Book details Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hakanko akayi washe gari tana tashi sallan asuba bata koma ba tasa wannan kaya tacire tasa wancan ta cire saboda sunyi da Rabin ranta zasu haɗu da kyar tabar wata riga da skirt na atampa datashs embroidery tayi kyau sosai makeup tayi sosai tayi kyau kamar yar tsana ita kanta tasan tayi kyau 7:30 tafita koda ta isah dai² za'a fara lectures tunda tashigo kallonta yakeyi da mamaki kyan data sakeyi haka yafara koyar dasu saide time to time ita yake kallo suna haɗa ido take sake masa murmushi haka sukayi 2,hours kafin suka fita bakin sch ta tsaya tana kiransa dai² da fitowan sa tare sukayima juna smiling motanta suka shiga taja motan suka fita sun ɗanyi tafiya kafin tayi parking gefen titi hira sukeyi sosai ita dashi suna dariya duk wata damuwarta tanema ta rasa jinta take kaman ba itaba tsabar farin ciki Maina dogon mutum ne shiba fari ba kuma ba ba baƙi ba yana da ɗan jiki yana kyan da duk ƴa mace zata soshi hakan yasa mata kebinsa sosai.......sun jima sosai suna hira kafin ta maida shi sch taja motanta zuwa gida da yunwa sosai tashigo da kyar tayi wanka ko mai bata shafa ba jin yadda cikinta ke kuka yasata fita daga ita sai towel din ta iya guiwa kusan tsirara ma take dan ɗabi artace ɗaura towel ɗin da idan ta tsuguna tsab komai nata zai bayyana..... indomie ta dafa da kwai ta juye a plate sama zata hau sukayi karo gefe takoma ta bashi hanya daya wuce saide har ya wuce tana ƙoƙarin hawa taji kaman daga sama yana faɗin....."you illiterate baki iya gaida mutane bane yi tayi kaman bata jiba ta wuce ɗakinta cikin ɓacin rai yabi bayanta.......

*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝

*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*08069224458*
[8/28, 1:07 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥

*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋

*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽

*Auren kiyayya*

🅿️6️⃣🔁7️⃣

*This book is dedicated to my dearies my* *Dost and my behty can't heart you less you guys mean* *a lots to me* 💝💖

*Bismillahir rahmanin* *Raheem*

Alh Muhammad Kabeer cikakken sunansa kenan cikakken bafula tanin Adamawa ne saide duk zuriar su yan boko ne duk da wasu na kasuwanci amma sun fi ƙarfi a boko shidai bai tsayama boko ba yayi shi dai dai misali zuwa diploma yabama kasuwanci ƙarfi kaman wasa yake sarar abinci a ƙauyen su ya kaishi kano cikin ikon Allah ya dafa masa abu ya bun ƙasa anan ya haɗu da matar sa ko ince uwar gidansa cikakkiyar banufiya ce me suna Hadiza Abdul Kareem mata ce saliha mara son damuwa ya yaba da hankalinta sosai hakan yasa yabada himma ya aureta suna zaune a kano cikin ikon Allah ko bbu yabo bbu fallasa Allah ya haɗa arziƙin su dai² misali nan tafara haihuwar yaya mata har rai huɗu bbu na miji hakan yakawo cece kuce cikin dangi na bbu mai gadonsa ko tema konsa idan girma yazo suka takura suka basa yar uwarsa tayi baƙin ciki a lokacin yaranta sune Fatima,Aisha,Zainab tana goyon Hauwa cikin ikon Allah kuma sai amaryar tata me suna surayyah sam bata da damuwa suka haɗa kai haka rayuwa taciga ba itama surayyah yaya mata biyu ta zubo itakuma Hadiza haihuwa cak ta tsaya nan shima ya sake rarumo auren wata mai sayar da abinci a kasuwar su still gida ɗaya ya haɗe su bbu laifi suna zaman lfy haka dai surayyah sanda tayi ƴaƴa mata huɗu itama....ɓangaren zinatu mai abinci ma yaƴan ta mata biyu ta zubo nanfa cece kuce yasake yawa akan shi duk sai yaji duniyar bata masa da daɗi ana cikin haka ya sake kwaso bazawara ya cike huɗun nanfa gida yasoma samun damuwa Hadiza lokacin tanada cikin wata biyar bbu wanda yasani ɓoye shi takeyi saboda gudun kar ace ganin kishiyoyi na haihuwa ita bazata hkra ba ranar data cika wata tara da sati ɗaya ta haifi ɗanta namiji kyakyawa kaman ubansa murna gun dangi har ba'a mgna nan fa ƙiyayya ya soma tashi cikin yaro yaci sunansa Abdul Jabbar son duniya Alh Muhammad ya ɗaura masa cikin ikon Allah ana yaye shi takuma yin ciki wannan kam bai ɓuya ba sbd laulayi tayi sosai har an cire rai da ita kafin cikin ikon Allah kuma cikin na ƙwari tasamu sauƙi haka takuma sulluɓo dan ta namiji shima sak ubansa wanda yaci suna Ahmad murna nan ma gun mahaifin su ba'a mgna kuma cikin ikon Allah daga nan ta rufe haihuwa cikin matan ma bbu wanda yasake haihuwar namiji dukansu daga me yara shida sai mai biyar sai bazawara mai biyu haka rayuwa taciga ba duk yaransa yasa su makaranta asirin dai² a rufe......life goes on duk yaran bbu wanda baiyi University ba daga mazan har matan wasu suna kanyi suke aure wasu kuma sai sun gama cikin ikon Allah gida yasha gyara gun yara kuma kansu a haɗe...... Abdul Jabbar da Ahmad sun kammala karatun su suma Abdul Jabbar yafara aiki a government kuma yana kasuwanci mahaifin sa cikin ikon Allah tuni ya tashi haka Ahmad business ɗin dutse yakeyi yayinda shima ya haɗa da aikin government cikin ƙanƙanin lokaci suka kai iyayen su duka hajji suka siye gida jen maƙota suka haɗe dana su suka gyarama iyayensu.......

Ahmad ne ya kawo matar da zai aura baturiyar America mamah tayi baƙin ciki tace bazaiyi aure ba wansa baiyi ba akan hakan har jinya ya kwanta kaman bazaiyi ba hakane yasa baba ya yenke hukuncin yin auren amma da sharaɗin zata musulunta batayi musu ba dayake tana sonsa dan girman 9ja ce ta musulunta akayi auren saide tunda akayi auren sam mama taƙi sa ko abu yabata bata ƙarɓa bai kuma fasa ba duk hakuri da rarrashi na duniya an mata tace itakam bbu ita bbu shi shekaran su da aure ta haifi ɗanta namiji kaman bature nan mamah tace idan yasaka sunan wani azuriya bata yafe masa ba yayi baƙin cikin abun haka yanemi shawarar matar sa itakuma dama sunan Indians na burgeta kawai ta zaɓa masa suna salkhan nan fa yaro yaci sunansa salkhan Ahmad Muhammad....... rayuwata cigaba shekaran sa biyar da aure kafin Abdul Jabbar shima ya rarumo wata ba haushiyar kano mesuna Sofia mamah tayi murna sosai haka akayi auren saide ko shekara ba'ayi ba ya daina hidimar dayake da su daga sofia sai yan uwanta wannan abu yayima mama ciwo har magana tayi masa amma aban za tayi kuka harta godewa Allah a haka mahaifinsu ya rasu baiyi arba'in ba mama ta bishi hakan yasa wani gaba a tsakanin su suna ganin yayunsa maza su suka kashe iyayensu da bakin ciki koda aka raba gado shikenan kowa ya kama gaban sa banda matan da suke zumunci sosai abinsu.....life goes on Sofia ta haifi yarta mace wacce taci sunan mamah ake kiranta da nanah arziƙi yaci uban nada gunsu dukansu kuma matansu basu sake haihuwa ba gashi bawani jiyuwa suke sosai ba matan......rayuwa tanata tafiya yara sun girma ana ɗan zumunci duk masifar mata sunki yarda su rabu duka ana zumuncin dole...... salkhan yagama sec sch nan aka tura sa Dubai University lokacin nanah na sec s.s 1 yatafi sun dai san juna amma basa shiga harkar juna sam kowa sabgan sa.....a s.s1 ɗinta aka kawo musu wani corper mai suna Mainah kaman wasa suka fara soyayya shi kuma yaron sarkin wani ƙauye ne acan Gombe .....koda yagama service ɗinsa suna tare haka yasamu lecturing a Bayero University......lokacin tana ss2.....

Life goes on Alh Ahmad ne da Alh Abdul Jabbar zasu dubo salkhan nan mahaifiyarsa ta tubure sai taje bbu musu suka kama hanya aiko sai lbrin plane crash ɗinsu ne ya dawo Sofia ana kuka ana farin cikin tarin dukiya haka yasanya salkhan yadawo gida jin wannan gigiceccen labari tunda yadawo yaki komawa har rasuwar iyayen sa da kusan shekara da kyar ya koma Bayero University shima don ya ƙarasa...saide ba nan gizo ke saƙa ba nan Sofia ta dunga lallaɓasa tana bibbiyan sa da duk wata dukiya tasa da makirci tasa ya dawo gunta komai nasa kuma ya yarda da ita sosai ya sake da ita.....haka suka ci gaba da rayuwarsu shida nanah bbu me shiga harkar wani....saide wata ranar laraba da bazai manta da ita ba ya dawo daga sch da yunwa ya shigo gidan sama yasoma duwa ina zaiga Ammih tun daga stairs yake jin shewa dai² da ana kiran sunansa dana mahaifiyar sa wato rabi'atul badawiyya tafawa sukayi da ƙawarta me suna uwani tana faɗin ai wlh duk yanda zanyi na mallaki dukiyar yaronnan dashi kansa sai nayi aini bakin cikin rasuwar miji na kawai nake shima ba sosai ba tunda ga tarin dukiya ai Rabi tayi wahalar banza tunda yanzu ga ɗanta ga dukiyarsa duk sun zama mallakina sake fashewa sukayi da dariya...hawaye yakeyi ɗaya nabin ɗaya ya fita a gidan Basu ma san yajiba....Magar da yau bata san yaji ba knan kuma bai nuna mata komai ba haka ya lallaɓe rayuwarsa har yagama karatu ya kama aikin government da kuma harko kin mahaifin sa......

💦💦 *CIGABAN LABARI* 💦💦
Chapter 3 · 0% Book details