← Book details Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 26

Sashe 26

Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wajen 10 pm yana zaune yayi kiba yayi haske yayi kyau,ta shigo ta zauna kusa dashi,baiko nuna yaga mutum ba harta gama zaman tayi bacci agun bai kulata ba ya haye gado abinsa ya kashe wuta yayi addua yaka Dove ya rufe kansa.

Wajen 2am ta farka taji haushin ganinta agun sosai jki bbu ƙwari ta bisa gadon,tahsige jikinsa tafara shafasa cikin bacci yaji yadda ake masa wani wasa ya farka,“ya haka baki da hankali ne zaki dinga shafa mutum hka? Yana ture ta.

Da kuka ta fashe tana faÉ—in, "so kake sha'awa ta kashe ni?nifa wlh yau sai kabani hakkina kusan wata tara knan ina fama da sha'awa da azumi wlh bazan yarda ba nagaji.

Murmushi yayi yace,“au sai yau kika san dama akwai hakki tsakanin mata da miji ni kika wahalar dani iya wayannan shekarun kiji me naji banida tym ɗin ki yanzu Nabila,kin gaji kin kasa a tray knan nikuma ban ɗauka ba matsa kibani guri gobe fitan sassafe zanyi,yana faɗin hka ya tureta yaja bargonsa.

Kuka taciga ba da rera wa mai cin zuciya tana masa magiya,takusa one hour tana roƙon sa kafin ya miƙe yace mata,"har idan kina so na kusan ceki sai kinmin alkwarin zaki dinga mun biyyya kuma aduk sanda nake so bazaki hanani ba kuma zamu yi zama irin na kowace mace da namiji,kuma bbu raini baki koyi da abokiyar zamanki ne hka kika tana mun?sosai yayi mata faɗa tare da wa'azi mai shiga jiki,daga nan kuma zance ya canza saide ta ciwu tun tanajin na marmari har ta dawo neman temako shikam sanda yasa mu nutsuwa yarabu da ita.

Washe gari da asuba ya wuce side din Nanah ya duba ya jikinta,nan na hangeta da cikinta baifi 5months ba duk da bata da lfy bai hana sa wasa da ita kafin ya fice inda sabo yanzu tasa ba da halin Jamal na jaraba.

4years latter Salkhan ne zaune,da jariri a hanunsa bakinnan yaƙi ruhuwa sai kallon sa yakeyi,da murmushi ya kalleta yace,“thank you Fariha nagode ma Allah daya bani ke a matsayin mata i love you beyond expectations,nan nakai idona kan wacce yakira da matar sa Masha Allah,abinda nace knan ita ba fara bace kuma ba baka bace,tanada dogon hanci da idonta dan dai² sai bakin ta ɗan karami ko makiyin ta ya kalleta yasan Masha Allah tanada kyau bbu laifi,Ammih ne suka shigo ita da Noor wow! wayyo Allah kaman nasace ta gashin ta akame a tsakiyan kanta,cikin riga da wanda tayi tsayi kuma tana da kiba tayi kyau sosai, yarinya sak turawa bazama kace uwarta ba baturiya bace ba,ga gudu tazo ta na faɗin,"Daddy want to carry the baby, murmushi Salkhan yayi yanajin son ta aransa da ɗayan hanunsa yasa ya daga ta zuwa cinyan sa ya ɗaura mata babyn,sai kallonsa take can kuma ta fashe da dariya tamasa kiss a abaki tana faɗin,"i love the baby dukan su dariya sukayi,ya miƙa ma Ammih babyn ya rungume Noor yana mata peck a goshi.

Gidan Nanah ya je ziyara nan naganta zaune da tshon ciko ga wata kyakyawar baby daba tafi 3,yrs ba aganta sak Jamal Masha Allah yarinyar ta haɗu shikan sa Jamal ji yake da yarinyar,har yaran Nabila cewa sukeyi yanzu suna da sister dan itama namiji ta ƙara haifa Nanah tayi kiba tayi kyau sosai cikin yasake sata haske,rikici yarinyar danaji takira da ilham take mata kwade tayi tana faɗin wlh kin dameni da rikici dai² da shigowan Jamal ransa aɓace ya ɗauke ta bbu um bbu um um suka haura sama itama tabi bayan su.

2years later Nanah ce zaune driver na janta iham nagaba Nanah na riƙe da Hussain,Hassan nacikin baby seat tana gefe kuma mai tayata reno ce,cema driver tayi yayi parking tana so tasaya Olive Oil yanzu zata zo da Hussain tafita Masha Allah yaro ne tiƙe² bazama kace Nanah ce ta haife su ba,da sallama ta shiga saide bbu kowa ganin bbu kowane yasata fitowa wani shagon chaji dake gefe tanufa tayi sallama,ɗago kan da zaiyi ya ansata ne yasata saurin juyawa zata bargun har tana tuntube,da sauri yafita yasha gabanta,“Nanah Dan Allah kitsaya alfarman ki zanne ma ganin yadda yake magiya sata tsayawa kafin hankalin jama'a ya dawo kansu,hakuri yashiga bata harda ƙwalla "wlh Nanah wannan karan na tuba kinga yadda Allah ya mayar dani ko ankoreni a gun aiki nasaki matata,wanda yayi mata cikin kuma ya Aura yanzu hka suna Abuja,mahaifiya ta takoreni kingani yanzu bani komai wlh wannan dan chajin dashi nake ci nake sha dan Allah kiyafe mun yaƙare mgnar yana share hawaye.

Taji tau sayinsa sosai,"nayafe maka wlh Duniya da hira Allah ya yafemu gaba ɗaya bbu komai kuskure ne munyi saide muroki Allah ya yafe mana Kawai,harta fara tafiya yace mata.

"Nanah ta juyi" wannan me gadin gidan naku ba mutumin kirki bane ku koresa, murmushi tayi tace masa, "ai ya daɗe da barin gidan na gode ta shige mota jiki bbu ƙwari suka kama hanya zuwa gidan Ammih.

Suna isah ilham tafice da gudu tana ihun kiran Ammih,Noor najin muryan ilham tafito da gudu tasan mamanta tazo dai² da fitowan Salkhan ya ƙara so yaƙarɓa Hussain yana faɗin, "Dan Allah mekike ba yaran nan dan Allah jiyara Masha Allah kaman buhun gishiri dariya tayi,dai² da fitowan Noor da gudu itama ta ƙarasa ta ɗagata ta rungume ta sanda tayi ajiyan zuciya,afili tace i miss you swhrt tana mata peck a both side of her chicks sake rungumeta tayi yana faɗin,"i don't think zan sake haifar yarinyar danake sonta irin Noor tana riƙe da ita suka shiga ciki nan ta tarar da matar Salkhan Ammih ta ɗakko ta dan ba yar Kano bace ba,ranar a gidan suka wuni sai dare suka tafi taso tafiya da Noor amma tana tsoro hka tana share ƙwallanta suka bar gidan takasa sabo da rashin Noor.

Life goes on,Jamal ya sake samun matsayi dan yakusa retire wani dan ƙarraren gida yake gida musu,yanzu kam Alhamdulillah Nabila taɗan yi sanyi har akan gaisa koda dai basa shiga harkar juna sosai,yarane suka sasu dole yanzu suna zaman lfy,kuma da warning da Jamal yayi mata,dan dukan su yara ne Nabila dai tafi Nanah kadanne.

2years later, visa yazo ya zube mata agabanta yace su shirya dukan su zasu saudi harda Noor,hka Nabila ma duka da iyalen ta murna gun su harya baci,yace daga Saudi zasu wuce Qatar da sauran ƙasa she kaman biyar.

Cikin Kano international Airport knan, Alh Jamal knan da iyalen sa duka duk sunyi shiga ta alfarma sunyi kyau,amma kallo ɗaya zaka musu duk kasan ubansu ɗaya ne saide babban cin kyau da zaka ƴaƴan Nanah sunfi kyau,Noor kam kallo ɗaya zaka mata kasan ba jinin su bace ba dan kamanta duk inda sukayi sai ankalle su sbd yadda sukayi gwanin ban sha'awa sanda sukayi pice kafin suka hau jirgi,su Nabila ansa sakko sosai yanzu har ɗan hira suke taɓa wa,nan take cewa Nanah ranta nasan Noor Nanah taji daɗi sosai dan taso ɗago hka gun pics musamman tasa aka dinga yi masu itada Noor hka jirgin su ya tashi nikuma da bani da visa na dawo cikin Kano.

Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen Novel ɗina mai suna AUREN ƘIYAYYA nagode sosai mabiyana Allah yabar mu tare😍😘

*Masu jiran ARUWAN SAMA KADDARA TASAME NI,KUMA KUSA IDO INSHA ALLAH YANZU ZAN KARASA LABARIN NAGODE SOSAI MASOYA NA INA* *ALFAHARI DAKU* 😘❤‍🔥😍🥰

*Daga alƙalamin* ✍🏽📝

*Nanahkhadii💅🏽* 🛍️

*08069224458*
Chapter 26 · 0% Book details