← Book details Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 26

Sashe 12

Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Life goes on haka rayuwa taci gaba Nanah bata ko fita kullun tana gida ko abu takeso saide Ammih da kanta tafita ko ta aika driver ya sayo mata Noor kam masha Allah tayi kiba kumatun nan na yaran turawa kaman zai zubo gashin kan sul sul yaso ma fita brown dashi ko makiyinta ya kalleta sai yasake kallonta,saide tana damun Nanah da tsotso kaman me har takai Nanah na bata rabo da abinci agefenta,dan ma tym to tym idan ba Ammih agun saita bata ruwa tayita rarrashin ta harta hkra takoma baccin......

Wasa² fa bbu ɗuriyar Salkhan bbu ɗuriyar Mainah akwana atashi yau watan Noor 8 harda yan hakorinta guda biyu tayi kyau sosai idan kashi go gidan ma kaganta zaka zaci mamanta da babanta turawa ne dan bbu wani abu data ɗakko na bakkin fata, gashinta akwance har gashi ga blue eyes datake da ga hanci yarinyar ta haɗu masha Allah abinda nima Nanahkhadii nace knan,Nanah ce zaune ta idar da sallah Noor ta rarrafo zuwa gunta tana ɗaga mata hijab ko kallonta batayi ba taci gaba da adduanta,ganin uwar bata da niyan kulata yasata kuka tana sake jan hijab din, hanunta ta ɗaga ta mareta ta tureta gefe tana faɗin "shikenan ni dan na haihu nono na bazai huta ba nima bazan huta,kuka sosai Noor ta fashe dashi ta rarrafa tana so yafita amma ƙofan arufe,kwanciya tayi kasan gun taci gaba da kukanta dan bata kuka sam bazakce da yarinya agidan ba,ganin yadda take kuka kaman zata shiɗe yasata miƙewa jikinta asanyaye ta ƙarasa gun tasa hannu ta ɗauke ta, koda taga itace kanta ta kwantar ajikin ta tana kuka bayan ta take shafawa harta ƙarasa bakin gado,taciro ta miƙa mata saide sam taƙi karɓa kuka takeyi sosai nan hankalin Nanah ya tashi tasan bata kyauta ba,tunda abincinta ne agunta da kyar ta rarrasheta ta karɓa duk saitaji wani iri kuma,koda tagama wasa tashi ga yi mata rana nafarko knan data tage tana wasa da ita,sosai take kyalkyala dariya wayanta taciro ta mata video ta musu hotuna ta mayar,dan yanzu wayan ma sam baya gabanta,haka tayi ta mata wasa har bacci ya ɗauke su agun.......

Yau shekaran Noor ɗaya da wata uku bbu inda bata zuwa da ƙafarta Nanah taso yayeta Ammih tace sai ta shekara ɗaya da wata 8 sosai Nanah taji haushin abun saide bbu yanda zata yi,zaune take a ɗakinta Noor tayi bacci ajikinta bata san meyasa ba yau tunda ta tashi take tunanin Maina num dinsa tayi searching saide takasa dialling ta kashe ta ajiye,still jikinta bai bata ba tasa sake dakkowa tayi dialling har ya kusa tsinkewa akayi picking,saide muryan mace taji jitayi zuciyarta ta buga ƙarfin hali tayi tace "assalamu alaikum "wa'alaiki sallam wake mgna dan Allah?cikin ƙarfin hali "tace dan Allah inaso nayi mgna da Maina ne,Ayyah ya fita school ya manta da wayan ne saide ki kirasa ta ɗayan number sa, "ok tom nagode saide idan bazaki damu ba dan Allah dawa nake mgna? Murmushi tayi tace matarsa ce,Nanah bata gama sauraron ta ba ta kashe wayanta ta ajiye Noor tashi toilet ta soma rera kukanta,ashe karya yake yi dama ba auren nawa zaiyi ba ashe yaudara ta yayi ashe macucine bayida Amana nikam nashiga uku wannan wace irin rayuwa nake ciki tajima tana kukanta agun kafin ta wanke face dinta ta fita ta kwanta agun bacci yayi gaba da ita da tunani kala².

A month later saide shiru bbu ko ɗuriyar Mainah bbu lbrinsa zaune take a parlor tana ba feeding Noor datake ta mata rikici tasha ta sake taciga ba da kukanta har tayi zuciya tace tinda bazata sha ba bari ta mayar da kayanta saide kuma ta dameta da kuka sosai,hakan yasa ta dakko ta ta dubgure mata kai tana faɗin idan zaki sha kisha idan bazaki shaba wlh lst tym da zan baki knan haba kibarni da damuwar da ke damun na,tasata aiko ta karɓa ta fara sha,kaman daga sama taji muryan dako a mafarki tasan me ita muryar da harta koma ga Allah bazata manta da ita ba da ƙamshin turaren da ko bacci taji saita farka,kasa ansawa tayi har ya shigo inda suke batako iya ansa sallaman sa ba haka bata ko ɗaga ido ta kallesa ba ji tayi zuciyarta ta wani bala'in bugawa miƙewa tayi ta cire Noor a nono ta ajiye ta agun ta yi hanyan sama da gudu tana share hawayen dake ƙokarin zubo mata,da ido yabita da kallo yana mamaki kukan da Noor keyine ya dawo dashi hayyacin sa koda ya ɗaga ido ya kalleta ji yayi zuciyan sa ta daina harbawa cak ta tsaya yana kallon Noor dake kuka tana bin Nanah tana blabbing.....

*Daga alƙhalamin* ✍🏽📝

*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*08069224458*
[8/28, 1:13 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥

*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋

*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽

*Auren kiyayya*

🅿️2️⃣6️⃣🔁2️⃣7️⃣

*Bismillahir rahmanin* *Raheem*

"Kallon Noor yakeyi harta kai stairs ta fara hawa, kuma sai taja ta tsaya dan dama haka takayi idan a sama ne ko ƙasa zatayi ta yawonta,amma daga tafara hawa stairs sai taja ta tsaya har masu aikin gidan sun san halinta ne,saide a ƙarasa da ita.

"Cigabawa tayi da kukanta tsakanin da Allah,sai kuma tym ɗin ya dawo daga tunanin daya keyi,yabi bayanta yasa hannu ya ɗagata ganin bata san shiba yasata sake tsalla ihu,dai² da gangaro wan Ammih dan taji kukan yayi yawa kuma tana ta kiran Nanah shiru.

Baki buɗe Ammih kebin sa da kallo,Noor kam tunda taga Ammih take miƙa mata hannu,jikin Ammih a sanyaye ta karɓa Noor kafin tayi shiru,shikan sa kallon da Ammih ke masa sanda yaji wani iri,ba tare da tace masa komai ba ta juya ta haura sama,jikin sa a sanyaye yabi bayanta ɗakin Nanah tashi shiga,tana faɗin ina kika shiga?" kina ji yarinya sai kuka take kaman bbu kowa a gidan,Nanah kwance take a kan gado tana rusar kukanta mai ɗaci a zuciya,bata ko ɗago ba Ammih ta ƙarasa ta ɗaka mata duka tana faɗin,"idonki biyu nafaɗa miki ki dai na barinta tana wannan kuka mara anfani,miƙe wa Nanah tayi tana share hawayen idonta saide duk yadda taso ta boye ya gagara sbd jan da idonta suka yi,miƙa mata Noor Ammih tayi ta ƙarɓe ta saide koda ta ƙarbe ta,kallon mahaifinta kawai take mata tama kasa ko rarrashin ta kallonta kawai takeyi hawaye na zuba a idonta.

"Wai meye kike kukane?mutuwa akayi miki ne ko yaya? "Kibata Nono saiki kici gaba da kukun da ba zai anfane ki da komai ba,Ammih nakai wa nan ta juya zata fita Salkhan na tsaye ƙofar ɗakin saide ko nuna tasan yana gun bata yi ba zata wuce sa.
Chapter 12 · 0% Book details