← Book details Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sa'ako yana shiga yayi karo da Ammih ta rako baƙi nan suka gaisa ya ƙarasa da fara'ar sa, zaune take tana ƙoƙarin gyara hulan kanta ga duk garin sa ɗau kwallin har ribbon din yafita gashi duk ya baje,kawai saita sa kuka ganin hanu ɗaya ne da ita.

Koda aka buɗe ƙofar bata ma ɗago ba sai cewa tayi cikin kuka, "Ammih nakasa ɗaura ɗan kwallin,ta kowa yayi har inda take saide kamshin turaren sa shiyasa tasan ba Ammih bace koda ta ɗago kai taga shine wani haɗa rai tayi taci gaba da ɗaura da kokuwan ɗaura ɗan kwallin ta.

Baida muba ya ƙara so zai tattara mata cikin ɓacin rai ta turo baki tana faɗin, "bana so zan ɗaura abuna"

"To sauriniyar rikici wai ni meye nayine aketa fushi dani,wasu hawaye ne suka zuba a idanta tana faɗin, "kafin kowa sanin abunda kayi ni wlh na hkra da auren ka Allah yaba ka wacce tafini,duk jikinsa sanyi yayi yama rasa me zai ce mata sanda ya gama kama mata gashin ya ɗaura mata ɗan kwalin ya dawo kusa da ita ya zauna ya riƙo hanunta cikin nasa yace, "Nanah kiyi hkri ni zaki aura kuma ni kike so nake sonki Nanah idan kika ce zaki min bara zana da kin fasa aure na wlh zaki cutar dani kar kiyi mamakin ace miki zuciyata ta buga,wlh Nanah Allah ne yasan irin son da nake miki,cikin kuka harta na shiɗewa tace, "nifa ta taɓa sai kuma tayi shiru kallonta yakeyi sosai yana jiran jin mezata ce,kasa cigaba tayi da mganan sai kuka ganin bazata yi shiru bane gashi yana tsoron condition ɗin take ciki kawai ya haɗe lips dinsu,duk ƙoƙarin da takeyi na taja nata lips din kasa sosai yake kissing ɗinta hankalin sa kwance sanda yayi mai isarsa kafin ya saketa,girar sa ya ɗaga mata yana faɗin, "akwai ƙarin zance ne turo baki tayi tace, "yanzu da Ammih ta shigo fa"? "Murmushi yayi daya daɗa masa kyau yace Mata, shikenan kwana nawa dama yarage na mallake su duka.

"Nidai wlh bana so kuma zan faɗa ma Ammih tace aturo azo akarba kuɗin bazan iya kishi da matar ka ba tace mun karuwa,kuma nima kaddara ce ta faɗo mun wani kukan ta fashe dashi miƙe wa yayi yana faɗin, "Bari natafi tunda baki farin cikin ganina kome tace miki tace ita zata aureki koni duk abinda zata faɗa ina sane dasu kuma nace zan aureki,kina tunanin bansan komai bane Nanah murmushi yayi yace ki daina tunanin akan wannan zan fasa aurenki,shigo wan Ammih ne ya katsen zancen yayi musu sallama ya tafi ransa a ɓace da tunanin yanzu idan Nanah tace bazata aure shiba ya zaiyi.

Koda Ammih taga alamun Nanah tayi kuka nan ta ritsata saita faɗa mata meke faruwa,bata ɓoyewa Ammih komai ba duk ta mayar mata da yaddah akayi nan hankalin Ammih ya tashi,kuma koda Nanah tace ta hkra da Auren Jamal bataji zafi ba sbd bazata juri cin mutuncin yarta ba,da hka gara tazauna da yarta kawai dan tasan duk mijin da zata aura hakan saiya faru.

Nanah kwanciya tayi da tema kon Ammih bbu abida takeyi sai hawaye É—aya nabin É—aya.

Ammih kam bbu ɓata lokaci takira Anty Fatima ta mayar mata da duk abinda yafaru,kuma tace me suke gani koda Anty Fatima taji ba wani sabon abu bane gunsu sbd sun riga sun sani gun Salkhan,sosai Anty Fatima ta tausaya ma Ammih tace shikenan za'a kirasa yazo ya karɓa kuɗinsa ko zuwa gobe ne.

Hakan ko akayi washe gari aka kirasa yazo,sanda mijin Anty Fatima yayi masa nasiha sosai dayake babban malami ne kuma yace karya sa aransa idan matar sa ce wlh saiya aura,jikinsa a sanyaye ya karɓa kudin yakama hanya,zuwa gida gun mahaifiyarsa agaba yasata kaman wani yaro ya kuka tsakanin sa da Allah,dakyar tasha kansa tare da masa alƙawarin gobe zataje mu saman suyi zama da Ammih,bai bar gidan ba sai dayayi isha'i ko abinci baici ba sosai Hajja mamah ta tausaya masa wa'azi tayi masa sosai kafin yakama hanya,saide da wani ciwon kai da komai bibbiyu yake gani yaɗau hanya,Kiran wayan Hajja mamah akayi da wata number nan ake sanar mata da Jamal yayi accident yanzu hka suna asibiti.

"Innalillahi wa'innah ilaihinji'un waime ke shirin faruwa ne wannan wace irin rayuwa ce agigice tafita tana kiran driver yazo su tafi asibiti,suna isa aka kaita É—akin dayake duk yajijji ciwo yana kwance baima san waye akansa ba.

Salkhan ne yashigo dan shi baima san abunda akeyi ba,yana office kuma ranar bai samu yazo ba yayi tafiya kuma Koda ya dawo dare yayi, "Ammih menene naga sojoji acike a asibiti? Zaro ido Ammih tayi tana faÉ—in, "kodai sun zo fitar damu a asibitin ne tunda shiya kawo ta? Salkhan sam bai fahimci me Ammih ke nufiba fita yayi yace mata yana zuwa,baifi 10mins da fitaba ya dawo jikinsa a sanyaye,kallon gadon Nanah yayi yaga baccinta takeyi nan yace ma Ammih aiga abunda ya faru,basu ankara ba sai dirarta suka ji daga gado tana faÉ—in, "nashiga uku yayah Salkhan kaddai akaina ne kaini na gansa dan Allah kafin kace me duk Nanah ta rikice musu agun.

*Daga alƙalamin* ✍🏽📝

*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*08069224458*
[9/3, 11:48 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥

*ELEGANT ONLINE WRITTERS* 📚

*A short story* 💋

*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Auren kiyayya*

🅿️4️⃣2️⃣🔁4️⃣3️⃣

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥
🔚🔚🔚🔚
❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

Alhamdulillah inayi ma Allah godiya daya bani ikon kammala novel ɗina mai suna, *AUREN ƘIYAYYA* , kuskuren da nayi Allah kayafe mun abunda na rubuta ba dai² Allah kamun afuwa.
Godiya ta muasanman zuwa ga fan's dina naji daɗin yadda kuka nunawa novel dina soyayya,ina godiya mai tarin yawa a gareku ma'assalam Nanah khadii namuku son so fisabillah😍🥰😘

Spacial thanks to:

Elegant online writer's Allah yabar mu tare yakuma bar zumunci,gaisuwa ta bangirma mussaman zuwa gareki aminiya ƙawar arziƙi kuma yar uwa LAURAT M BELLO (UMMU KHAIRAT) Keɗin ta daban ce aguna Allah yabar mu tare sonso fisabillah💋💋

Wai! Wai!! Wai!!! Tirƙashi shin kunada labarin sabon littafin da marubutan biyu suke shirin kawo muku,kuzauna da shirin ku dan jiran sabon novel ɗin da wayannan mauruba suka shirya dan nishaɗan tar daku, wayan nan maurubuta kuwa sune, NANAH KHADII MARUBUCIYAR AUREN ƘIYAYYA DA KUMA LAURAT M BELLO MARUBUCIYAR YAYI MUN KADAN,sun shirya tsab zaku kawo muku book ɗin su mai suna *RANTSENTSAN* *RABO* To fa koda sunan littafin kusan akwai cakwa Kiya dan hka ku saurare su nan bada jimawa ba insha Allah😂 saide fa abunda namanta ban sanar daku ba shine paid book ne fatan zaku nuna mana soyayya ta hanyar siyar wannan littafi,muna alfahari daku masoyan mu kuma muna muku barka da zuwa🥰😍💋😘

*Bismillahir rahmanin* *Raheem*

Nanah ji tayi duk bbu daɗi duk yadda Ammih ke convincing ɗinta akan tabari sai ciko wan sojojin nan yaragu taƙi,daga ƙarshe dai Ammih tace ma Salkhan ya rakata badan ransa yaso ba hka Ammih tasa mata hijab suka fice nan suka bar Ammih da mamaki.

Koda suka je sojan dake gadi ƙofar ɗakin hana su shiga yayi,cikin sa'a da Hajja mamah tajiyo sune tafito dan Nanah taƙi barin gun shikuma,sai muzurai yake musu tasu ta sojoji.

"Hayaniyar me nakeji ne hka"? Ganin su Nanah yasata fara'ar dole,nan tace mishi yabar su sushiga.

Cikin girmama wa tagaida Hajja mamah,bbu yabo bbu fallasa Salkhan ma ya gaishe ta yana mata yame jiki,yana gama gaida ta ya juya ya fice a É—akin.

Cikin sanyi jiki take jan ƙafarta ta ƙarasa gun dayake kwance,ya kukkuje a jikinsa kallo ɗaya zaka masa kasan baccin wahala yakeyi.
Koda ta ƙarasa kawai saita fashe da kuka tana faɗin,"ban taɓa kinka ba arayuwa ta kuma ban yanke hukunci dan nasaka a damuwa ba,wlh tsoro irin cin mutun cin da matar ta mun nakeyi tun awaje knan inaga idan nashigo gidan?" "Me kake ganin zai faru ni bazan zama sanadiyar shigan ka damuwa ba wlh nayar da zan Aure ka nashirya ɗaukan duk wani abu akanka,shiru tayi kuka yaci ƙarfin ta har ranta bata ji daɗin yadda tagan sa sam.

Shoulder ɗinta Hajja mamah ta dafa,ɗagowa tayi ta kalla Hajja mamah ta sake fashewa da kuka tana faɗin,"Dan Allah Mamah kiyi hkri wlh banyi hka dan nasa shi cikin wannan halin ba,katse ta Hajja mamah tayi tana faɗin,"ko kaɗan ban zarge ki yarinya sbd tun ranar daya zo mun da lbrin kin kika shiga zuciyata kuma koda nasaki a ido,naga mutunci da kunya a tare dake to ko hkan ya faru ko karya faru,Allah ya kaddara yau sai abun nan yafaru karki saka komai aranki kinji,cikin kuka ta girgi za kai kaman wata ƙaramar yarinya halaman to.

Ta É—an jima agun kafin tace ma Hajja Mamah zata tafi,zata dawo anjima har É—aki Hajja mamah ta rakata,nan suka gaisa da Ammih take mata jejeto tare da faÉ—in zata zo ta duba sa,Anty Nusaiba ba nan ta mata yame jiki tare da faÉ—in insha Allah tare zasu zo da Ammih,sosai Hajja mamah taji daÉ—in yadda Nanah ta nuna kulawa ga Jamal tana saka rai,da insha Allah tasan yanzu É—an ta zai samu nutsuwa da Mata tagari.

Sai da sukayi sallan isha'i tym ɗin driver ɗin Anty Nusaiba yazo suka fita dukan su dan zuwa duba Jamal,koda suka je sun same sa yana Sallah basu tsaya jiran sa ba suka gaida Hajja mamah ta musu rakiya,Nanah kam kujera taja ta zauna dama raka'ar ƙarshe yakeyi har ya idar yayi addua idonta na kansa,juyo wa yayi yana kallonta eye ball to eye ball itama shi take kallo ganin bayida niyan ɗauke idonsa neya sata,hura masa isakar bakinta tana faɗin,"hey tana murmushi kunya ne ya kamasa ƙeyan sa ya sosa yana faɗin,"Ina kince baki sona? Kuma a ƙarshe kinga halin dana shiga kin zata son wasa nake miki ne ko kin zata yauda rarki zanyi,Nanah wlh kinji na rantse bazan fasa faɗa miki ba nayi bin cike sosai akanki Nanah kuma a hka nake sonki,shiru yayi yana kallonta sunkuyar da kai tayi duk saita ji bbu daɗi.

Kallonta yakeyi bbu gaggautawa,kaman daga sama ba tare da ta ɗago kai ba yaji tana faɗin,"am so sorry i didn't mean to hurt you is just that am scared of ur wife,abun da tamun was so painful shiyasa nace na hkra.
Chapter 22 · 0% Book details