← Book details Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 26

Sashe 14

Auren Ƙiyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fita ya tsaya ya clearing bill dinsu ya saya maganin suka kama hanya,still bbu wanda ke cewa kowa komai,sai dai Noor data fara rikici tana ɗaga hijab din Nanah,Yi tayi kaman bata san me take nufi ba Noor kam rikici take sosai tana sake jan hijab din Nanah, Salkhan na lura da ita ransa sosai ya ɓaci amma yayi kaman bai gani ba,baiko ankara ba yaji tana faɗin"Wai taya kike so ki sake sha ne bayan dazu wanke ni kikayi da amai,ni bazan baki ba sai mun isa gida,idan kika mun amai anan dame zan wanke? Tana faɗin haka ta sake gyara mata zama,kuka sosai Noor ta fashe dashi,baice mata komaiba jin zuciyar sa na tafa sa guri yane ma yayi parking inda bbu ƙafar mutane sosai,cikin ɓaci da ita kanta tasan ransa ya ɓaci yace,"Nanah kiba Noor abin da take so,wani kallo tabi shi dashi tana faɗin"taya zaka ce nabata abin da take so bayan kana kallo da tasha amai tayi,baiko juyo ba dan kukan Noor din har ransa yake ji,yace "ba mgnarki nake son ji ba oder nabaki ko baki ji me nace bane ki bata abin da take so,yana faɗin hka ya juyo yana kallon ta, ganin yadda har idon sa sukayi wani iri yasa bata ko iya sake mgna ba,tuni ta juya da Noor ta gyara mata kwanciya,ta ɗaga hijab ɗinta tasata ciki a yun wace ta karɓa tafara sucking,harta gama zata juya ta zuwa ɗayan kukan bata ƙoshi ba tafara yi,ta gefen ido ta kalla Salkhan da ya wani ɓata rai,"aa Noor juya ki zanyi sake juyata zuwa ɗayan tayi suna gun harta gama sha tama yi bacci,taci rota a hijab din tana share mata zufan face dinta,saide kaman daga sama taji Salkhan na faɗin,"Ajiye mun ƴata kifi tan mun a mota,jin mgnar tayi kaman daga sama kallon sa tayi tana faɗin "ban gane mekake nufi ba?"Thank God hausa nayi miki ba wani yare ba, Amma tunda baki gane ba barina mai² ta miki nace ki ajiye mun Noor ƴata ki fitan mun a mota,bazan jure kina wulaƙan ta mun ƴa a gabana ba gara muyi nida ke zan iya ɗauka,but bazan iya ɗaukan ko wani wulaƙanci akan Noor ba,mind you Noor ƴata ce kuma jina ce Nanah ina son Noor fiye da son da nake yima ni kaina,saboda Nanah kin sa na tsani duk wata ƴa mace a duniya gani nake duk halin ku ɗaya ne,Nanah ƙiris ya rage baki sa na shiga hallaka ba,kin sa nabar garin nan not knowing where am going,shiru yayi ya kasa ƙarasa mgnar kallon ta kawai yayi,yayi tsaki yace ajiye mun ƴata kifita mun a mota,cikin kuka ta miƙa masa Noor tafita a motan,shima jan motan yayi kaman zai tashi sama yabarta agun,hawaye takeyi ɗaya na bin ɗaya tafara tafiya ganin unguwan bbu mutane sai gidaje a kukkule kowa na cikin gidan sa tasan ba ganin napep zata yi ba hakan yasata miƙi titi tana tafe tana kuka ga tunanin bbu kuɗi a hannunta,ahka ta ɗanyi nisa da tafiya.

Kaman daga sama taji ana Mata sallama,"assalamu alaikum wa'alaiki Hajiya an wuni lfy,sake sauri ta shigayi dan bata da niyan tsaya wa sam,shima sake jan motan yayi yana faɗin"haba hajiya atleast ko sallaman dana miki kya ansa ni a matsayin ki na musluma, Sai tym ɗin tajuyo ta kalle sa bai zaifi shekara 40 ba a duniya yana da haske da dogon hanci bbu laifi duk da kallon tsoro ta masa tasan Masha Allah,"wa'alaikum sallam abinda tace knan taci gaba da tafiya, murmushi yayi mai ƙayata face dinsa yace"kaman kina sauri nikuma gashi na dame ki,bai dace ace mace mai kyau kamarki Masha Allah tana tafiya a ƙasa ba,bar ma wannan zancen kishi har ya kamani duk za'a kalle ki kafin ki isa gida,idan bbu damuwa zan iya dropping dinki?kallon sa tayi tana faɗin"nagode yanzu zan isa gida Insha Allah, murmushi yayi yace"Dan Allah kitema keni da number ki tunda bazaki shiga mota na ba ɗi ɗan yankan kaine ya ƙare mgnan yana kallonta,"niba na bada number ta gsky saide kayi hkri,baice mata komaiba ya juya motan yasha gaban ta yana faɗin,"Dan Allah kimin wannan alfarman karki sa zuciya ta buga,ganin zai ɓata Mata tym yasata faɗin "Idan nabaka zaka barni na tafi yace murmushi yayi yace"your wish is my command,nan ta fara kira masa num dinta harta kai ƙarshe tunda ta fara baiko rubuta komai ba,wayan ce kawai riƙe a hannunsa lips dinta kawai yake kallo sanda tagama tace"zan iya tafiya sai tym ɗin ya sauke idon sa akan ta yana faɗin,"sorry ga wayan kisa mun ban jiba,tsaki tayi aranta tana faɗin wannan yafiye naci takarba wayan tasa masa num din har zata tafi yace "Mai sunan sarauniyar? Nanah kawai tace tabi gefe ta wuce abinta,yanda taba shi num din da queen Nanah yayi saving sannan yayi dialling akashe,sake jan motar yayi yabita yana faɗin,"Queen Nanah num din baya tafiya Allah yasa ba halinku na mata kika munba, kaman zatayi kuka tace"wayan na gida anjima zan kunna tana kaiwa nan ta kara sauri, murmushi yayi yaja motan sa yayi gaba,Nanah kam na isa bakin hanya ta tari a dai² sahu ta roƙe sa akan sai sunje zata basa kuɗin yace bbu damuwa.

Koda ta isa ta sallami mai napep sa stairs sukayi karo da Ammih,"har kun dawo ne ina Noor din?ji tayi zuciyarta ta buga da gske tana kallon Ammih da zararrun ido dan ita bata tasu take ba ta faɗan Ammih takeyi "wai dama da gske Yayah Salkhan din bai dawo da ita gida ba?"ban gane me kike faɗa ba a asibitin kika bar sune ko yaya?sunku yar dakai tayi alaman rashin gsky tana faɗin "Ammih wlh cewa yayi na sauka a motan sa nabar masa ƴar sa,nina zata gida zai kawo ta kuma ashe,bata ankara ba sai jin mari tayi har sau biyu "wlh Nanah bazaki kashe ni ba kifita mun a gida kije kinemo jikata ƙwalli ɗaya a duniya baki san yanzu nafi son ta dake bane,ki ɓace mun daga gani nace kifita kine mo mun Noor,A gigi ce Nanah ta gangara ganin yadda Ammih ta fitan mata agiya rasa ma ta ina zata fara tayi,gashi ko waya bbu a hannunta haka tafita bakin gate ta nemi guri ta zauna tana kuka tsakanin ta da Allah,"Nikam nashiga uku wannan wani irin rayuwa ce nake ciki ace kullun nike nan acikin damuwa,kukanta take sosai kaman ranta zai fita godiyan ta ɗaya akwai canjin ɗari biyar da mai Napep yabata miƙewa tayi,tana tunanin koda taje gidan sane kar taje baya nan kuma bata da kuɗin dawo wa,haka dai ta dinga tunani kala² agun idan tagama tayi kuka iya ƙarfin ta.

Wasa² har wajen magrib bbu Salkhan bbu Noor,ganin zaman bazai mata bane yasa ta shiga gidan,cikin san ɗa harta haura sama zata buɗe ɗakinta taji Ammih na faɗin ina"Noor din ji tayi komai nata ya tsaya cak da kyar ta juyo jiki na rawa tace,"Ammih dan Allah kiyi hkri wlh ban san inda zan same su ba yanzu zan kunna wayata na kirasa,"Ammih jin ranta ya sake ɓaci cikin ɓacin rai tace "wlh idan kin bari ya tafi da ƴar nan kema ki soma haɗa kayan ki zaki bar mun gidana,tana faɗin hka ta juya ta koma ɗakin ta Nanah ma ɗakinta ta shiga da sauri ta nufi inda take ajiye wayanta ta kunna, tafara dialling num din Salkhan saide switch off aka cemata wurgar da wayan tayi tana faɗin,"Nikam nashiga uku na yazan yine Salkhan da ƴar sa zasu kashe ni, sin tiri tafara yi a ɗakin tana kuka da tunani kala² kafin tashiga toilet ta ɗauro alola tayi azzahar da la'asar da magarib tana idar wa an fara kiran isha'i nan tayi kafin tafara duk wata addua data zo bakin ta yi takeyi,saide fa abu kaman wasa har wajen 9shiru ne.

*Daga alƙalamin* ✍🏽📝

*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*08069224458*
[8/28, 1:14 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥

*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋

*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽

*Auren kiyayya*

🅿️3️⃣0️⃣🔁3️⃣1️⃣

*Wannan page ɗin baƙi ɗayan sa sadau kar wane ga fans din book ɗina inajin daɗin comments dinku much love dearies💋😍🥰😘*

*Bismillahir rahmanin* *Raheem*

"Ɓangaren Salkhan kam yana jan motan sa gidan su Zaid,yanu fa ko daya isa bbu musu gate man din ya buɗe masa dan yasan shi yana parking yakira wayan Zaid,buga ɗaya yayi picking"guy how far ya akayine cewar Zaid,"klau ya kana gida ne?"eh gani parlorn mom muna hira,"to ok tom barina shigo.

Haka ya ɗauki Noor da ledan mganinta suka shiga ciki,mamaki ne yakama Zaid ganin Salkhan da ƴa riƙi² guri yane ma ya zauna,yana gaida mom din Zaid da fara'arta ta ansa, Zaid ne ya bishi da kallo yana faɗin,"Guy kai kuma daga ina harda baby haka? murmushi Salkhan yayi yana faɗin"Noor ce ƴa tace mana,baki sake yace "kana nufin yarka da Nanah? Wata harara ya bisa dashi yana faɗin"abeg karka dame ni da tambaya kaman ɗan jarida tom da dawaye,mom din Zaid ce ta daka tar dasu da faɗin"Masha Allah muga kishiyar tawa,miƙewa yayi ya miƙa mom din Zaid ita Noor kam baccin ta take tsakanin ta da Allah,kallo tabi ta dashi tana faɗin"ikon Allah kaga yadda yarinya tayi kama dakai sak lalle wannan kishiya tawa tafini kyau nima kanti zan shiga na sake fari,duk kansu dariya suka fashe dashi.
Chapter 14 · 0% Book details