← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 59

Sashe 55

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jamaal ma ciwon kan ne tareda zazzabin gaske ya rufesa sbd kirjinsa Daya toshe Dan haka cikin karfin hali ya fito kusan su babban da Dad Omar na bayansa suka fito gurin sedai babban tashin hankalin da suka tarar a wajen ne ya Saka jiri diban Dad Omar da Jamaal lokaci Daya sbd tabbatarda motar Haroon ce a gurin pake.

Ahmed ma dayake cikin shock saurin tare Omar yayi Yana kallan motar da tashin hankali yace

"Haroon Yana gurin Nan??

Babbah na Jin Hakan jiri ya zubar dashi jikin motar Omar Dake gurin Yana ambatar "Qalu innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Jamaal Daya ji kansa na sake daukan masifaffiyar zafi da sauri ya nufi motar yaganta a rufe

Ahmed da Shima cikin tashin hankalin ya zagaya Baya ya zagayo koina gidan baiga Haroon dinba ya dawo saiga key din motarsa a kasa gurin yashe.

Babbah na ganin Hakan yayi zaman Yan bori a gurin Yana cewa

"Shikenan haukarsa ta motsa zaije ya sanar WA mahaifinsa"

Zabura yayi da sauri ya nufi Omar Yana cewa

"Wallahi tinda baida cikakkiyar lafiya tsaf zai iya sanarwa ubansa,ku yi wani abu Akai ko wlh tallahi a cikin Daren Nan na tattara iyalina ku nememu ku rasa wlh ko zaka sake ganina sai qiyama idan mun hadu gaban Allah."

Dad Omar da Baya ma gane me Babbahn ke fada motarsa ya nufa Dan sauri Shima Jamaal tasa ya nufa Ahmed ne yasamu karfin halin Jan Babbah ya jefa mota ya rufe suka tayarda motacinsu kaman masu wasan tsere cikin mugun gudun Daya Saka Babbah sake shiga tashin hankali suka hau titi su sukai kudi shi yayi arewa kowannensu Yana Saka Kiran wayar Haroon din ba kakkautawa.

Jamaal kaman zai tashi sama haka ya figi motar Yana Saka Kiran Haroon din idanuwansa na rikidewa gaba Daya Dan kuwa kowannensu tsoronsa kada Haroon din ya nufi su Dad Dan haka tabbas yaji wani abu shiyasa ya bar gurin a halinda basuda tabbacinsa tinda ga key din motarsa yashe a gurin.
#MAMUH#
#JAMAAL JEEY SEELAH
#AMEENATOU JDEN SEELAH
#OMAR JDEN SEELAH
#MAM SEEELAH
#LAMS SEELAH
#THE SEELAHS
#WAR

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
#ZafafaBiyar
#BestLove

54
BB kuwa Kai tsaye gidansa ya nufa Dan Haroon din Kuma harya Isa Bai Hadu da wata matsala ta jamian tsaro ba Dan haka Yana Isa yayi parking motarsa a harabar gidansa ya Bude ya fito ya zagayo ya Bude motar ya dauko Haroon din Wanda ciwonsa yakai kololuwan tashi sai fizga yakeyi Yana jijjiga kansa Yana buga kan a jikin hannuwansa idanuwansa a rintse.

Kai tsaye Dayan dakinsa yakaisa ya zubar a kasa tareda juyawa ya fice daga dakin Yana Ciro wayarsa ya Saka Kiran babban yaransa.

Yana daukan wayar Kai tsaye BB yace

"Killer ka kawomin Ps biyu yanzun Nan"

"Yes oga" killer ya fada daga bangarensa Yana kashe wayar tareda ture macen datake kansa tana lashesa kaman sweet har Saida kanta ya bugu da Bango ko a jikinsa ya miqe tsaye Yana kama dadar kansa datake a watse ya Saka Roba ya daureta tsakiyar Kai Yana nufar toilet ya wanko jikinsa ya fito,
Underwear yafara sakawa kafin ya Saka Jean Akai ya Saka shirt ya dauki wayarsa da key din motarsa yafice bayan ya shiga dayar dakinsa da mugayen kwayoyin rayuwa suke ciki ya dauko wadda ogan ya buqata.

Koda killer ya iso gidan BB ya tube yayo wanka dagashi sai underwear Wanda kusan Babu abinda na jikinsa da baka Gani.

Dakin suka nufa Yana miqawa killer hannu ya amsa fitinanniyar kwayar wadda take hade da ruwan alluran ta,

Tsananin karfi da balain dayake tattareda ita uku ake tanata asha Daya alluran Kuma tafi komai balai da masifa Dan hadda tsananin azabar gaske ne da ita Dan haka suna shiga dakin ya daga allurar Bai tsaya wata wata ba ya kama wuyan Haroon ya soka masa ita tareda dure masa ruwanta gabaki Daya Wanda yayi daidai da budewan idanuwansa cikin tsananin azabar da Bai taba samun kansa aciki ba take ya qame kaman Sanda kafin jikinsa ya saki gaba Daya Hawaye na gangaro gefen Idanuwansa da sukai duhu gaba Daya Baya ganin komai.

Sakin kansa BB yayi gaba Daya ya yanke jiki agurin ya zube kansa na bugawa da bakin table Dake gurin gashinsa na fashewa jini na fitowa ahankali ya lumshe idanuwansa Yana Jin jijiyan jikinsa kaman suna tsinkewan hakama jinin dayake jikinsa yana konewa cikin wata sanyayyar azaba Mai radadin gaske ga  ganinsa gaba Daya ya dauke Baya ganin komai Baya Jin komai.

Dad Lameenu ne da BB ya kira tin Yana hanya ya shigo dakin bayan BB ya Bude masa kofar Yana kallansa tareda basa tabbacin Haroon din bayaji Baya ganin Komai.

Tsayuwa Dad Lameenu din yayi akansa tareda kallan BB Wanda Shima killer ya kalla aka Ciro kwayar killer na kokarin rabawa uku BB yace ya basa a Hakan.

Cikin tsananin firgici da tashin hankali killer din duk rashin imaninsa ya Kalli BB din sbd ko ukun idan aka ranata akasha  ba qaramin Neman kashe mutum takeyiba bare duka Kuma har gida biyu.

Karban kwayoyin Yan kanana dasu BB yayi baiyi wata wata ba ya Bude bakin Haroon dayake kwance kaman gawan data rasa gatan suturtawa ya zuba masa su duka tareda karban ruwan da Alh Lameenu yake miqa masa ya zuba masa take suka wuce maqoshinsa.

Suna shiga kafin ma su fara aiki BB ya bari fuskansa da karfi tareda tayar dashi zaune duk da jikinsa asake yake Babu abinda yake Aiko a jikinsa.

Cikin tsananin mawuyacin halin da ko mara Imani Saiya zubar masa da Hawaye ya Bude bakinsa kansa na masa wani hayaqin masifa da balai yafara jijjiga Yana cewa

"Ameenatou itace 'yarka Dad Omar, Dad Omar ka auramun Ameenatou sbd mutuwa zanyi idan na rasata, Ameenatou bazan taba barin kowa yasan itace 'yar da ake nemaba ko da Hakan zaiyi sanadin Raina Dad Omar,
Babbah ku bani Ameenatou,
Jamaal ku bani Ameenatou,
Dad Omar ka taimakeni ka cika mun burin auren Ameenatou.......""

Sakinsa BB yayi tareda ja Baya da tsananin karfi jikinsa na daukan wani rawa da tashin hankalin da Bai taba tinanin shiga ba sbd Jin Abinda Haroon ke fada,

Shi kansa Lameenu Baya yayi da sauri Saida killer ya tarosa sbd firgici da shock din abinda yaji din.

Haroon kuwa sanqarewa yakeyi jini na fitowa bakinsa da hancinsa sosai sedai Bai Dena magana ba hakama jikinsa Bai Dena jijjiga ba.

Da sauri cikin masifaffen tashin hankali da tsoron abinda yake Gani da Wanda yaji Dad Lameenu ya Kalli BB Yana cewa suyi sauri su gogewa Haroon din jinin su mayar dashi inda zaa samesa kada ya mutu a hannunsu.

Suma Dake cikin tashin hankali sake shiga sabon tashin hankalin sukai sbd sanin waye Mam idan 'dansa ya mutu a hannunsu Dan haka ba Bata lokaci suka daukesa suka Kai mota
Kusan motarsu data Lameenu a tare suka fice su sukabi wata hanyar Shima yabi wata.

Tafiya sukeyi suna gudu sosai suna kallan Haroon din Wanda yake zubarda jini sosai har lokacin cikin mafi tsananin azabar rayuwarsa da Bai taba jiba.

Tafiya me tsayi sukai kafin suka Isa inda BB din ya daukosa suka ajiyesa agurin suka gudu batareda kowa ya gansu ba.

Suna barin gurin motar siddeeq da shima ya shiga layin masu tsananin Neman Haroon din sbd zautuwan da Jamaal ke Neman yi gurin Nemansa Yana Sako Kai a layin Dan sake dubawa sai gashi kuwa yayi mummunan Gani Dan halinda ya samu Haroon din saura kadan ya buga zuciyarsa,

Bazai iya barin Jamaal ya gansa a wannan mummunan halinba Dan haka hankali tashe ya daukesa tsaban shiga rikici Kai tsaye Mansion din ya nufa dashi sedai Yan Isa ganin abin yayi muni Dad ya nema Kai tsaye sbd shi kansa jijjiga jikinsa yakeyi tsaban tashin hankali.

Mam na fitowa kallo Daya yayiwa Haroon ya Yanke jiki ya Fadi sbd zuciyarsa data buga irin bugun da zai iya kamuwa da shanyewan Rabin jiki mum Atee ce tayi saurin rikesa itama jikinta na daukan rawar tsoro da firgita sbd ganin abinda yafi karfin nata rashin Imanin.

Daukansa Akai aka nufi ciki dashi Kai tsaye bangarensa Akai dashi zuwa lokacin jikinsa sake sanqarewa yakeyi Dan haka suna Isa Kai tsaye toilet siddeeq ya wuce dashi ya Saka a bathtub din dayake cike da ruwan sanyi.

Dad kasa tsayuwa yayi ya qarasa gurin Haroon din dayake sanqare acikin ruwan jini har lokacin Yana fitowa ta hancinsa.

Wani irin kukan da baisan yanada shi bane ya fashewa Dad din Yana ihun ambatar Haroon din daidai Nan Lameenu yashigo Shima kafafunsa na rawar tashin hankali da tsoron abinda zai iya biyo Baya.

Kamo Haroon din yayi Shima Yana ambatar sunansa sedai Haroon Babu abinda yake ji a lokacin.

Sosai jinin yake sake gudu Wanda ya Saka siddeeq kasa riqe kansa ya kira Jamaal Wanda yaketa bulayi a titin Lagos Yana Neman Haroon din Yanajin abinda siddeeq ya fada Kai tsaye ya juyo motarsa kaman zai tashi sama yayo mansion din.

Isowansa yayi daidai da wani tarin jinin gaske da Haroon ya feso daga bakinsa Mai yawa jikinsa na qarasa sakewa gaba Daya a jikin Dad Wanda yake rungume da Haroon din qamqam Yana Jin Abinda Bai taba ji ba na ganin zaka rasa Wanda kake tsananin so da dukkanin rayuwarka.

Ganin Dan uwansa ya Saka Jamaal karasawa kafafunsa na Neman sarewa hakama zuciyarsa koina yankewa yaji tana yi.

Dad Lameenu da sauri ya janye daga Haroon din ya bawa Jamaal guri.

Hannuwansa duka biyu yakai cikin ruwan ya kamo Dan uwansa Yana fitowa dashi sbd gaba Daya jikinsa ya lalace da jini
Bai tsaya komaiba ficewa yayi dashi daga dakin ya fita dashi Dad Wanda ya kasa motsawa daga inda yake tsaban mutuwan dayakejin duka jikinsa yayi Babu inda ke motsuwa mum Atee ce ta kamasa suka fito suma suka marawa Jamaal din Baya.
Chapter 55 · 0% Book details