← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 59

Sashe 48

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu amfani ko kadan ga gujewa zama gidansa dayake hade da masu tinda abinda yafi so da kauna duniyarsa fiyeda komai ta riga ta shiga hannunsu Dan haka ya yanke shawaran tinkaransu kaman yanda suka tinkaresa Dan yasan Nemansa ne sukeyi Kai tsaye shiyasa suka bayyanawa duniya fuskan Babbah Dan ya Gani duk da baida tabbacin sun gane asalin waye 'yarinyar da suke Shirin aurawa dansu din Hakan yake son tabbatarwa Dan baida ikon kowanne irin motsin da zai Saka babynsa a hadarin da zai illata masa ita sbd a yanda aka kawo sauran kwanaki ne kadai suka ragewa auren bayajin Babbah zai fahimci abinda yake son ya fahimta Amma dai Kuma bayajin har abada zai iya bayarwa ko barin 'yarsa da ita kadaice jininsa Kuma Jaden daya data rage ta shiga hannunsu Mamman.

A cikin Daren su dukkanin iyalan seelahs da suka dawo suka tararda koina na wutar mansion din Jden a kunne ta haskaka koina na zagayen gidan Wanda Hakan ya tabbatar musu da an kunna switch na wutan gidan gaba Daya dayake kashe hakama securities ne na musamman koina zagaye da gidan Wanda Koda suka fita hidiman bikin Babu ko Daya a mansion din.

Babban abinda ya sake raya mansion din shine matar Ahmed da yayansa biyu dasuke tareda su duka a cikin gidan Dayake kusan tsarin Mansion dinsa na can Greece Dan haka a cikin Daren ma'aikatan da duka aka Riga aka tanadar musu suka iso gidan cikin abinda Bai wuce awanni ba aka hau aikin gyaran gidan kafin su iso shiyasa Koda suka iso komai tsaf Babu abinda yake tashi sai kamshin freshners dana manyan humidifiers dana burners dayake tashi a duk inda ka Saka kafafunka da sanyin ACs da Suma suke aiki.

Ma'aikatan kusan guda biyar ne aka kawo dukkaninsu mata sai namiji Daya da shikuma harabar Mansion din itace tasa.

Mum Noor matar Omar da har lokacin ta riga ta rasa cikakkiyar lafiyanta akan abinda ya faru Bata Gani sosai hakama Bata iya tafiya sai akan wheelchair itama hakanan suka taho sbd yazo da niyar zama ya fuskanci wainda suke son fuskantarsa Amma zuwan na yarsa ne Daya danne dukkanin abinda yake ji akanta tsawon shekarun ya nesanta da ita sbd Bata kariya da rayuwar Kwanciyar hankali batareda tsoro ko fuskantar hatsarin dayake tattareda wata dukiyar ba,

Taimako da kyakkyawar rayuwar dayaso Basu itada su Babbah duk ya danne kansa ya janye daga garesu sbd koma huldan dazaiyi dasu a boye su Mam zasu iya bibiyan Hakan su mata illa.

Yayan Ahmed ba wani shekaru ne dasu ba sbd ya Dade sosai sosai baiyi aureba har Saida ya fara manyanta ma Dan haka suke Yara daidai kusan Ameenatou din Amma tama girmesu da shekaru biyu zuwa uku haka Dan babbar kenan sai namijin Wanda duka duka yanzu yakeda 10yrs zuwa 11 Dan haka masu aiki tini suka fara kokarin kaisu dakinsu Dan taimaka musu dasu wanka da sauransu.

Mai aikin da itace kaman babba a cikinsu sunanta Zahida itace ta Kai kayan kowannensu dakinsa ta fito ta nufi dakin yar budurwan wadda batasan sunanta ba Saida taji mom dinta ta ambaci sunanta da Fatmah kafin ta kama itama.

Abincin alfarma marasa nauyi irin Wanda sukasan zasu iya ci ne dayake dukkanin masu aikin kwararri ne aka dauko wainda albashinsu ma na musamman ne suka jere a makeken dining din Wanda Babu abin buqatan ci da Sha da baa jere ba cikin tsari.

Alh Omar ne a sama gaba Daya da mum Noor
A qasa Kuma Dayan bangaren Ahmed da nasa Iyalin ne dakin Fatmah daban hakama dakin Arfat daban.

Dukkaninsu Babu Wanda zai iya cin wani abinci a Daren sbd gajiyan dasuke tattare da ita,basa wani Jin yunwa sbd sunci snacks dasu tea da sai sauransu a jirgi so basa wani Jin yunwa Hutu kawai suke buqata.

Arfat da Bai Saba da koina ba hasalima shi Bai taba zuwa Nigeria ba tinda aka haifesa Dan haka kwata kwata qin yadda masu aikin su kusantosa yayi wanka yayi abinda ya shirya cikin kayan bacci ya fito ya nufi dakin Fatmah ya kwanta tareda ita itama duk da Bata san Kwanciya dashi Amma sbd bakuntan gidan ya Sakata kyalesa bayan sunyi sallah tea me zafi ta buqata daga masu aikin kawai Tasha ta kwanta.

Duk yanda Mam suka shiga mamakin abinda yake faruwa Basu nemesa ba sbd dare yayi Suma Kuma a matiqar buqatan hutun suke sbd hidiman da aka Sha Dan haka suka bari zuwa da safe Dan tabbatarda idan Omar jden dinne ya sauka Nigeria.

******Washe garin ranar da mamaki kowa ya wayi gari da ganin dawowan Wanda baa taba tinanin Gani ko yaddar zai dawo din ba wato Alh Omar jeden seelah wadda tini labarin ya fara yaduwa.

Mam da Lameenu da kansu suka taho yi masa barka da sauka cikeda farin ciki Mai tsananin gaske da nuna yabawarsu batareda nuna komai a fuska ba,
Shima Bai nuna komaiba cikin farin ciki da nuna kewan juna ya bayyana farin cikin ganinsu.

Fira suka zauna sosai cikin kewa da murnan kasancewansu tare da juna a yau din bayan tsawon lokaci sun Hadu a matsayin brothers da aka Sansu.

Mum Noor Bata nuna komai ba sbd ba komai ma ta sani ba Dan haka sosai aka Hadu anata murna da farin ciki musamman dasu mum Atey suka shigo hakama su mummy Sarat ma duk sun shigo hadda su Aliyah anata murna harma da matar Ahmed Aunt Didi Wanda take wayayyar mace sosai Kuma ta waye ga ilimi Dan haka ta saki jikinta ta sake acikinsu.

A tare duka ahalin sukai breakfast qatuwar dining din gidan Dad Omar ana sake tattauna bayan rabuwa da Kuma murnan auren Haroon Daya sake hada auren.

Bayan breakfast shigewa su Dad suka sake yi Babu Wanda yake jinsu suna palonsa anata maganganu.

Su mum Atee ma sun jima sosai kusan a gidan aka wuni gaba Daya sai daga baya kowa ya koma masu fita Kuma irinsu Aliya tini ta qara gaba duk da Dad Omar tana yinsa sbd Yana kaunarsu sosai hakama wasu lokutan idan ta Kalli tazarar dukiya Dan rayuwan dayake da shi da 'yannansa su Dad dinta sai take Jin inama shine ya haifeta gashi a waye fiyeda Dad dinda da ilimin da kallansa kadai zakai kasan ya gama shigarsa Tako ina.

Sai dare Jamaar gidan suka samu Hutu da gidan yayi tsit sukaci abinci gaba dayansu a dining kafin kowa ya shige dakinsa yayi wanka ya kwanta Dan samun hutawa.

Washe gari Haroon ne da Bai samu zuwa ba jiyan ya taho yayiwa Dad din sannu da zuwa cikin farin ciki sosai.

Zuba masa idanuwa Dad Omar din yayi Yana karantarsa cikin nutsuwa da kulawa a matsayinsa n Wanda zai auri yarsa ta cikinsa.

Haroon sosai yake kauna da girmama Dad Omar shima Amma Kuma kusanci da kaunan Dake tsakanin Jamaal da Dad Omar din Babu Wanda zai iya shiga ko samun irinta Dan haka Shima Omar yake kaunar Haroon har ransa sbd kaunar dayakewa Jamaal da Dr Aleena Amma Badan mahaifinsa ba.

Haroon ya Jima a gidan Shima kafin ya fito Kai tsaye ya nufi ganin amaryansa.

A Daren Ahmed da Omar suka fita sedai Bai nufi gidan Babbah Kai tsaye ba Wanda suka samu bayanin komai nasa da gidansa,
Zuwa gidansa Kai tsaye yanada hadari Dan haka masallacin da babban yake sallah ya nufa Dan yin sallan ishai acan.

Babbah tareda Abdul da Hafiz suka fito daga gida suka nufi masallaci kowanne da sauran ruwan alwala a fuskansa Hafiz na latsa wayarsa Babbah na masa maganar meyasa yake zuwa da waya masallaci Hakan baida amfani tinda ba dadewa zaiyiba a masallacin.

Shiga masallacin sukai Babbah ne a gaba kafin su a bayansa suna shiga suka shiga sahu
Ana kokarin tayarwa Ahmed da Dad Omar suka shigo masallacin Kai tsaye gefen Babbah Omar ya tsaya Yana gyara tsayuwansa Dan tayarda sallan Ahmed ma gefen Omar din ya tsaya Yana gyara nasa tsayuwar.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
48
https://chat.whatsapp.com/K3rO5UonX4GDVxtQbA5mZl

Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!!! Wannan group din dai na komai da komai ne. A taiqaice
*Farashin mu na daban ne compared to sauran Yan kasuwa
*Kaya masu kyau da quality. Abinda kika zaba shi za a Baki
* Swift delivery.watau waybill a sauqaqe da Yardar Allah
* Muna sake New Arrivals ka fin su cika Gari
* Muna iya duba maku kaya a good price ko da ba namu ba ne idan kuka Aiko da hoton kayan
Allah sa mu qaru da juna Ameen

***********
Babbah da baisan waye a gefensa ba sbd ya riga ya tayar da sallansa Dan haka hankali kwance da nutsuwa yake sallan hakama suma kowa ya natsu a cikin jam'in.

Dun Yana sallah ne Babu filin tinanin komai a zuciyarsa Amma dai Kuma ya tabbatarda ko waye a gefensa bako ne a masallacin Kokuma babban mutum ne sosai Dan qamshinsa me sanyi da nutsuwa ya tabbatarda Hakan kusan a duka sahun Babu Wanda qamshin me sanyi Baya shiga hancinsa.

Ana sallame sallar Babbah yana juyowa zai gyara zamansa idanuwansa suka sauka akan fuskan Wanda yake kusa dashi din take salatin daya debo daga bakinsa ya bace masa bat.

Juyawa gefensa Daya dasu abdul suke zaune yayi yaga hankalinsu Baya kansa adhkar kawai sukey,
Juyawa yayi bayasan yaga kowa abinda yake gabansa yakeyi da sauri ya sake dawo da kallansa gefen nasa ya sake kallan fuskan Omar ya kasa yadda da idanuwansa Gani sukeyi daidai Dan haka ya ambaci sunan Hafiz a hankali cikin nutsuwa yace

"Wannan bawan Allahn Dake gefena ka taba ganinsa a kuwa??"

Kallan Omar Dake zaune hankalinsa kwance Yana addua yayi yaga kwata kwata idanuwansa basa kansu hakama da alama lafiyayyan Mai abin duniya ne dan daga nutsuwansa da motsin jikinsa kadai zaka gane Hakan.
Chapter 48 · 0% Book details